Rasha ta amince a ziyarci tashar nukiliya ta Zaporizhzhia

Asalin hoton, Reuters
Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce za a bai wa jami’an Majalisar Dinkin Duniya damar ziyara tare da duba tashar nukiliya ta Zaporizhzhia da sojin Rashar suka kwace daga Ukraine.
Fadar gwamnatin Rashar ta sanar da haka bayan wata wayar tarho da Mista Putin ya yi da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron.
Wannan sanarwa ta Rasha da ke zaman wani abin albishir ta zo ne bayan da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya gaya wa BBC cewa ya damu gaya a kan halin da ake ciki a wannan tasha ta nukiliya.
A lokacin ya ce dole ne a kawo karshen ayyukan soji da ake yi a kusa da wannan tasha ta Zaporizhzhia, sannan ya bukaci Rasha ta bayar da dama ga jami’ai su je su duba yanayin yadda wurin yake.
Tun a farkon watan Maris Rasha ta karbe iko da tashar, amma kuma ma’aikatan Ukraine ne har yanzu suke aiki a wurin, bisa umarnin Rashar.
A sanarwar da Rashar ta fitar bayan tattaunawa ta waya tsakanin shugaba Vladimir na Rasha da Emmanuel Macron na Faransa, fadar gwamnatin Rashar, Kremlin ta ce, Mista Putin ya amince a bai wa masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya dukkanin taimakon da suke bukata su je su duba wurin.
Kremlin ta ce dukkanin shugabannin biyu sun lura da muhimmancin tura kwararrun ma’aikatan hukumar nukiliya ta duniya, IAEA zuwa tashar domin su ga yanayi da abin da ke gudana a can a yanzu.
Shugaban hukumar nukiliyar ta duniya ya yi maraba da kalaman na Shugaba Putin, inda ya ce shi da kansa zai jagoranci kai ziyara cibiyar.
Rafael Grossi ya ce a wannan yanayi mai tsananin hadari, abu ne mai matukar muhimmanci a ce ba wani sabon mataki da za a dauka wanda zai iya jefa tsaro da zaman lafiyar daya daga cikin manyan tashoshin nukiliya na duniya cikin hadari
Jami'an Ukraine sun ce Rasha ta mayar da tashar a matsayin sansanin soji, inda take tura kayan soji da makamai ta kuma jibge dakaru kusan 500 wadanda ke amfani da tashara matsayin wata garkuwa, su kai hari kan garuruwa da ke tsallaken Kogin Dnieper.
A 'yan makonnin da suka gabata an yi ruwan makaman atilare a kusa da tashar, inda gwamnatocin Rasha da Ukraine ke zargin juna da kai harin.
A ranar Alhamis a yayin wani taro tsakanin Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya da shugaba Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya soki Rasha kan kai hari da gangan kan tashar.
Duk da aniyar da Rasha ta nuna ta bayar da damar kai ziyara tashar, jamia'n Rasahar kememe sun ki yarda da bukatar kasashe da hukumomin duniya ta dakatarwa da kuma janye duk wasu ayyuka na soji a wurin.
Mukaddashin darektan yada labarai a ma'aikatar harkokin wajen Rasha
Ivan Nechayev, ya ce yin hakan zai ma sa tashar ta kasance ba ta da kariya.
Sannan ya musanta zargin kasarsa na jibge kayan soji a wuri.











