Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd da Chelsea na son Pavard, PSG ta yi wa Roma tayin Wijnaldum
Brighton ta yi watsi da tayin da Manchester City ta yi kan Marc Cucurella, dan wasan baya kan fam miliyan 30. Brighton na son a ba ta fam miliyan 50 ne kan dan wasan mai shekara 23. (Athletic - subscription required)
Sai dai Benfica ta yi wa City tayin Alejandro Grimaldo, dan wasan baya mai shekara 26 a matsayin wanda zai maye gurbin Cucurella. (i Sport)
Barcelona kuwa za ta yi kokari na karshe domin sayo Jules Kounde, dan wasan baya mai shekara 23 kuma dan Faransa. Sai dai Chelsea ta riga ta mika tayin fam miliyan 55 kan dan wasan. (Sport - in Spanish)
Barca za ta nemi sayo Aymeric Laporte dan wasan baya mai shekara 28 na Manchester City idan ba ta sami damar sayo Kounde ba. (Fichajes - in Spanish)
Manchester United da Chelsea na gasa da juna kan Benjamin Pavard, dan wasan baya na Bayern Munich da Faransa mai shekara 26. (L'Equipe, via Sun)
Leeds United ta ki amincewa da tayin da Newcastle ta yi na fam miliyan 18 kan dan wasan tsakiya Jack Harrison mai shekara 25. (Football Insider)
Nottingham Forest na duba yiwuwar sayen Emmanuel Dennis, dan wasan gaba mai shekara 24 na Watford da kuma Najeriya kan fam miliyan 25. (Mail)
Borussia Dortmund na jinjina daukan Luis Suarez, dan wasan gaba mai shekara 35 bayan da kwantiraginsa ta kawo karshe da Atletico Madrid a karshen wannan kakar wasan. (Sky Sports - in German)
Chelsea na fuskantar matsaloli na rashin masu taya gola Kepa Arrizabalaga mai shekara 27 da dan wasan gaba Timo Werner mai shekar 26 saboda tsadar su. (Telegraph - subscription required)
Paris St-Germain ta yi wa Roma tayin daukan Georginio Wijnaldum, dan wasan tsakiya mai shekara 31. (Corriere dello Sport - in Italian)