United na son dauko De Jong, Nottingham ta taya Lingard

Manchester United na son daukar Frenkie de Jong wanda ba ya son barin Barcelona – amma idan har ya amince, dan wasan tsakiyar na Netherland, mai shekara 25, zai fi son komawa Bayern Munich ko Chelsea maimakon United. (Sport - in Spanish)

Jules Kounde ya shirya domin a duba koshin lafiyarsa a Chelsea nan da kwanaki biyu masu zuwa, bayan Blues sun amince da biyan fam miliyan 55 ga Sevilla domin daukar dan wasan, mai shekara 23, wanda shi ne mai tsaron gida na Faransa. (Sun)

Blues din kuma suna harin dauko dan wasan RB Leipzig da Croatia, mai shekara 20, Josko Gvardiol, inda suke son maye gurbinsa da dan wasan baya na Sifaniya, Cesar Azpilicueta, mai shekara 32, wanda ake sa ran zai koma Barcelona da taka leda. (Sun)

Nottingham Forest na duba yiwuwar daukar dan wasan Watford mai shekara 24, da dan wasan gaba na Najeriya, Emmanuel Dennis, wanda darajarsa ta kai fam miliyan 25. (Mail)

Har yanzu Manchester United na son daukar dan wasan Ajax, kuma na tsakiyar Brazil Antony, mai shekara 22, duk da cewa ya yi watsi da farashin fam miliyan 51 da kungiyar ta yi masa tayi.(Talksport)

Leicester ta yi watsi da tayin fam miliyan15 domin daukar dan wasan Monaco Boubakary Soumare, a daidai lokacin da suke kokarin samun fam miliyan 23 da suka kashewa dan wasan tsakiyar na Faransa, mai shekara 23, a kakar wasa da ta wuce. (Mail)

Dole Foxes ta sayar da ‘yan wasa, kafin sake sayo wasu, don haka za su iya amsa tayin dan wasan tsakiya na Ingila, James Maddison, mai shekara 25, da dan wasan gaba na Najeriya Kelechi Iheanacho, mai shekara 25, da dan wasan baya na Belgium Timothy Castagne, mai shekara 26. (Telegraph - subscription required)

Nottingham Forest ta tayin dan wasa Jesse Lingard kan kwantiragin fam 200,000 a kowanne mako, fam 800,000 a kowanne wata ke nan, a daidai lokacin da suke kokarin rattaba hannu kan kwantiragin daukar dan wasan West Ham kuma mai kai hari na Ingila mai shekara 29. (Mail)

West Ham da Crystal Palace sun yi magana da Burnley kan dan wasan tsakiya na Ingila Dwight McNeil mai shekara 22. (Sky Sports)

Newcastle ta shiga zawarcin dan wasan Leeds United da Ingila, winger Jack Harrison mai shekara 25, kan fam miliyan 18. (Football Insider)

West Ham, da Everton, da Napoli da kuma Sevilla na duba yiwuwar daukar dan wasan Belgium Adnan Januzaj, mai shekara 27, a kyauta, bayan ya bar Real Sociedad a kakar wasan da ta wuce. (AS - in Spanish)