Neymar ya kusan tarar da Pele a yawan ci wa Brazil kwallaye

Dan kwallon tawagar Brazil Neymar na kara sa kwazo a tamaula, domin kasarsa ta taka rawar gani a gasar kofin duniya da za a yi a Qatar a shekarar nan.

Brazil na fatan lashe kofin duniya na shiga jumulla ranar 18 ga watan Disamba a Qatar, wato ranar fafatawar karshe daga nan a rufe labulen wasanni sai wata shekara hudu.

Ranar 6 ga watan Yuni Brazil ta yi nasara a kan Japan da ci 1-0 a wasan sada zumunta da suka kara a sabon filin wasa a Tokyo.

Neymar ne ya ci kwallon a bugun daga kai sai mai tsaron raga, saura minti 14 a tashi a karawar da ya shiga daga baya.

Kwallo na 74 kenan da ya ci wa Brazil, guda 19 a bugun fenariti, ya kuma haura Ronaldo na Brazil mai 62, yana kokarin kamo tarihin Pele, wanda ya ci wa Brazil 77.

Neymar ya yi wa Brazil wasa 119, yana kokarin tarar da Dani Alves mai 125, sai Roberto Carlos mai 125 da kuma kafu da ya buga wa Brazil fafatawa 142.

Brazil za ta buga gasar kofin duniya a Qatar, bayan da kawo yanzu wasa daya aka doke ta shi ne wanda Argentina ta lashe Copa America a 2020 a Maracana.

Brazil ta samu gurbin buga gasar kofin duniya kai tsaye, bayan da ta ja ragamar wasannin rukunin kudancin Amurka.