Newcastle ta shirya daukar Isak daga Sociedad kan £60m

Asalin hoton, Getty Images
Newcastle ta shirya tsaf domin daukar dan wasan gaba na Real Sociedad Alexander Isak kan kudi fan miliyan 60.
Idan Cinikin ya fada dan wasan zai zama mafi tsada da Newcastle ta taba saya a tarihi.
Dan wasan gaban Sweeden din mai shekara 22 zai karfafa gaban kungiyar saboda yawan raunukan da Callum Wilson ke samu, wanda a yanzu haka ake jiran sakamakon binciken raunin da ya ji a cinyarsa.
Tsohon dan wasan Borussia Dortmund din Isak ya ci wa Sociedad kwallo 44 a cikin wasa 132 da ya buga mata, ya ci kuma kwallo 37 ga kasarsa.
Dan wasan mafi tsada da Newcastle ta taba dauka a tarihi shi ne Joelinton, wanda ta saya a 2019 kan kudi fan miliyan 40.
Kungiyar ta biya wasu kudade na kari da suka kai fan miliyan 35 ga dan wasan tsakiyar Brazil Bruno Guimaraes a watan Janairun da ya gabata, sai dai daukar Isak wani mataki ne da nuna sabbin masu kungiyar shirye suke a dama da su a kasuwar musayar 'yan wasa.







