Grealish zai je Everton, Hankalin Muani ya fi kwantawa da Juventus

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Ingila, Jack Grealish mai shekara 29, ya amince ya je Everton a matsayin ɗan aro daga Manchester City. (Teamtalk)
Chelsea na tattaunawa da RB Leipzig kan cimma yarjejeniyar musayar ɗan wasan tsakiya a Netherlands, Xavi Simons mai shekara 22, sai shi kuma ɗan wasan gaba na Faransa Christopher Nkunku mai shekara 27, ya koma ƙungiyar ta Jamus. (Guardian)
Nicolas Jackson zai so ya koma Newcastle United indai akwai bukatar matashin mai shekara 24 daga Senegal ya bar Chelsea a karshen kaka. (Telegraph - subscription required)
Newcastle na jira ta ga makomar ɗan wasan Sweden Alexander Isak mai shekara 25, kafin ta gabatar da tayi kan ɗan wasan Chelsea, Jackson. (PA news agency)
Newcastle ta gabatar da tayi kan ɗan wasan Brentford, Yoane Wissa na DR Congo mai shekara 28, wanda Liverpool ke sa wa ido saboda tana son saye shi idan ta rasa Isak. (Caught Offside)
Ɗan wasan gaba a Faransa, Randal Kolo Muani mai shekara 26, zai so ya je Juventus a maimakon Newcastle saboda zaman aro da ya yi a kakar da ta gabata a ƙungiyar ta Italiya daga Paris St-Germain. (Teamtalk)
Sunderland ta tuntubi ɗan wasan Ingila Lloyd Kelly mai shekara 26, wanda ya je Juventus bayan zaman aro a Newcastle. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
AC Milan na tattaunawa kan saye ɗan wasan Denmark mai shekara 22, Rasmus Hojlund, amma kamar sun fi son ya je zaman aro, yayinda Manchester United ke son yarjejeniya ta dindindin. (Sky Sports)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bayan saye ɗan wasan gaba a Slovenia Benjamin Sesko, Manchester United ta karkata kan rabuwa da ɗan wasanta a Ingila, Jadon Sancho mai shekara 25, da ɗan wasanta na Argentina, Alejandro Garnacho mai shekara 21, sai kuma na Brazil Antony mai shekara 25. (Standard)
Manchester United na nazari kan tsohon ɗan wasan gaba a Ingila mai shekara 28, Dominic Calvert-Lewin wanda ya baro Everton a karshen kakar da ta gabata. (Caught Offside)
Nottingham Forest ta gabatar da tayi kan ɗan wasan Monaco, Soungoutou Magassa. (L'Equipe - in French)
Kostas Tsimikas na gab da raba gari da Liverpool bayan shan zaman benci a fafatawar baya-bayanan na ƙungiyar, kuma tuni Nottingham Forest ke nuna kwaɗayinta kan ɗan wasan mai shekara 29. (Echo)
Besiktas da Fenerbahce na farautar ɗan wasan Marseille, Jonathan Rowe, yayinda ake alakanta Rennes da Atalanta da shiga farautar matashin mai shekara 22. (L'Equipe - in French)
Ɗan wasan gaba a Jamaica, Michail Antonio mai shekara 35, ya ce yana tattaunawa da ƙungiyoyin Ingila da ketare bayan barinsa West Ham a karshen kaka. (Talksport)
Enzo Fernandez ba zai bar Chelsea ba a wannan kakar, duk da cewa rahotanni a Sifaniya na alakanta ɗan wasan na tsakiya daga Argentina da Paris St-Germain. (Fabrizio Romano)
Ƙungiyar Al-Nassr ta Saudiyya ta cimma yarjejeniya da ɗan wasan Faransa, Kingsley Coman mai shekara 29 daga Bayern Munich. (Bild - in German)
Ɗan wasan tsakiya a Mali Abdoulaye Doucoure mai shekara 32, ya koma ƙungiyar Neom ta Saudiyya daga Everton. (L'Equipe - in French)











