Yadda Sweden da Finland suka sauya daga 'yan ba-ruwanmu zuwa mambobin Nato

Asalin hoton, Swedish Armed Forces
Sweden da Finland za su shiga Nato - wani sauyi da ake ganin daga kasashen da suka jima suna zama 'yan ba ruwanmu da janye jiki daga duk wani ƙawance na soji.
A lokacin wani taron Nato a Madrid, sun shawo kan abin da ake ganin zai kasance cikas na ƙarshe a garesu - adawar da Turkiyya ke nunawa.
Rasha ta nuna kakausar adawar ganin ƙasashen biyu sun zama mamba a Nato kuma ta yi amfani da batun faɗaɗar ƙungiyar ƙawance a matsayin hujjar yaƙin da ta ke yi da Ukraine.
Ƙasashen biyu sun shafe tsawon shekaru ba sa shiga harkokin kowa, amma tun bayan da Rasha ta kutsa Ukraine goyon-bayan Nato na ƙaruwa sannu a hankali.
Me ya kawo shiga Nato a yanzu?
Matakin Vladimir Putin ya raunata zaman lafiya da aka jima ana gani a arewacin Turai, da jefa Sweden da Finland cikin rashin tabbas.
Tsohon Firaministan Finland, Alexander Stubb ya ce shiga ƙawance abu ne da an riga an gama ga kasar sa, tun lokacin da dakarun Rasha suka kutsa Ukraine a ranar 24 ga watan Fabarairu.

Asalin hoton, Hulton Archive
Ga 'yan Finland da dama, abubuwan da ke faruwa a Ukraine ya haifar da fargabar ganin yiwuwar hakan nan gaba a ƙasarsu.
Tarayyar Soviets ta mamaye Finland a shekarun 1939. Sama da shekaru uku sojojin Finland sun nuna jajircewa, duk da fin karfinsu a yawan dakaru.
Sun hana a mamayesu, amma a ƙarshe sun rasa kashi 10 cikin 100 na yankinsu.
Ganin abin da ke faruwa a Ukraine na tunasar da su tarihi, a cewar Iro Sarkka, masanin harkokin siyasa a Jami'ar Helsinki.
Finland na hango iyakarta mai tazarar kilomita 1,340 daga Rasha, a cewarta, su na kuma tunani: "Hakan na iya faruwa da mu?".
Sweden ita ma na ganin tana cikin barazana a shekarun baya-bayanan, yayinda ake samun rahotanni kan karya dokokin sararin samaniyarta da jiragen Rasha ke yi.
A 2014, Sweden ta firgita da rahotanni da ke cewa jirgin yakin Rasha ya yada zango kan tekunta a Stockholm.
Shekaru biyu bayan wannan dakarun Sweden sun koma tsibirin Gotland da ke gabar tekun Baltic, bayan watsar da shi na tsawon shekaru 20.
Me zai sauya?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sweden da Finland sun kasance abokan huldar Nato a hukumance a 1994 kuma tun daga wannan lokaci suka kasance masu bai wa ƙawance gudunmawa sosai.
Sun kasance cikin ayyukan Nato da dama tun bayan kawo ƙarshen yaƙin cacar-baka.
Ƙasashen biyu a karon farko za su samu tabbacin tsaro daga ƙasashen da suka mallaki nukilliya karkashin kundi na 5 na sharudan Nato, wanda ya amince da cewa hari kan mamba guda tamkar hari ne kan dukkanin mambobinsu.
Masanin tarihi, Henrik Meinander, ya ce Finland a shirye take na zama wannan mamba, biyo bayan hanƙoranta na rungumar Nato tun bayan faɗuwar Tarayyar Soviet.
A 1992, Helsinki ta saye jiragen yaƙi 64 daga wajen Amurka. Bayan shekara uku, ya shiga cikin Tarayyar Turai, tare da Sweden, kuma gwamnatin Finland tun lokacin tana nazartar zabinta kan batun Nato.
Rundunar, mai yawan mutane miliyan 5.5, na da karfin sojoji 280,000 da 900,000 da aka tanada baki ɗaya.
Sweden ta rungumi hanya na daban a shekarun 1990, da rage karfin sojinta da sauya fifiko daga kare yankunanta zuwa wanzar da zaman lafiya a sassan duniya.
Amma duk wannan ya sauya a 2014, lokacin da Rasha ta ƙwace yankin Crimea daga Ukraine.
Finland ta kai matsayin da aka amince da ita na kashi 2 cikin 100 a ma'aunin tattalin arziki na GDP, kuma Sweden ita ma na kan hanyar cimma hakan.
Mece ce abin barazana?
Shugaba Vladimir Putin na Rasha na da yardar cewa faɗaɗar Nato barazana ce kai-tsaye a gareshi da tsaron kasarsa, don hakan Sweden da Finland shigarsu ƙawancen na iya kasance kokarin tunzuri.
Ministan harkokin wajen Rasha ya ce an gargaɗi dukkanin ƙasashen biyu kan abin da ka iya biyo baya.
Tsohon Shugaba Dmitry Medvedev, da ke da kusanci da Shugaban Rasha, ya gargadi cewa wannan yanayi na iya tunzura Moscow ta jibge makaman nukiliya a Kaliningrad, da Rasha ke iko da shi tsakanin Poland da Lithuania.
Yayinda wannan barazana ba abin watsi ba ne, Alexander Stubb ya yi tunanin cewa wata barazanar da ke iya biyo baya, ita ce batun kai harin intanet daga Rasha, yada labaran boge da karya dokokin sararin samaniya.
Nato na iya tabbatar da kariya ga Sweden da Finland?
Akwai tsiraru a Sweden da ke ganin ba lallai ba.
Deborah Solomon, daga Ƙungiyar tabbatar da zaman lafiya da Sweden, na cewa batun nukiliya a Nato na kara daga hankula da jefa barazanar rige-rigen makamai da Rasha.
Wannan na sake sukurkuta batun kokarin samar da zaman lafiya, a cewarta, da mayar da Sweden kasar da tsaro ya yi karanci.
Wani abin fargaba shi ne shiga ƙawance, Sweden za ta rasa damarta na jagoranci kan batun kwance ɗamarar nukiliya a duniya.
Mutane da dama na tuna rawar da Nato ta taka tsakanin shekarun 1960 zuwa 1980, lokacin da Sweden ta yi amfani da matsayinta na 'yar ba-ruwanmu wajen shiga tsakanin.
Shiga Nato tamkar watsi ne da wannan burin, a cewar Ms Solomon.
Matsayin Finland ya fita daban. Ya zo da sharuɗan zaman lafiya da Tarayyar Soviet ta kakaba a "yarjejeniyar ƙawance" 1948.
Ana kallon haka a matsayin kokarin tsira da ci gaban 'yancin kai a kasar.
Idan kasancewa 'yar ba-ruwanmu na Sweden ya zama abin bayyana asali da martaba, ga Finland batu ne na yalwa, a cewar Henrik Meinander.
Wani dalili da zai iya sanya Sweden ta amince da batun tafka muhawara kan zama mamba a Nato dalili ne na tana amfani da Finland da yankin Baltics a matsayin 'yar ba-ruwanmu". a cewarsa.
Finland ta yi watsi da matsayinta bayan rushewar Tarayyar Soviet.
Wani irin kalubale ka gabansu?
Tsawon makwanni, Turkiyya ta datse bukatar Sweden da Finland. Amma duk wani kokarin faɗaɗa Nato sai ya samu amincewar mambobinta 30.
Gwamnatin Turkiyya ta yi zargin cewa ƙasashen na goyon-bayan ƙungiyoyin da ta kira na ta'addanci, ciki harda 'yan awaren Kurɗawa da ƙungiyar Gulen, da Turkiyya ta ɗaurawa alhakin kokarin kifar da gwamnatinta a 2016.
Kurɗawa sun kasance kashi 15 zuwa 20 na al'ummar Turkiyya, kuma an shafe tsawon shekaru su na fuskantar shari'o'i daga mahukuntan Turkiyya.

Asalin hoton, FREDRIK SANDBERG
Domin samun goyon-baya, Turkiyya ta ce ta na son Sweden da Finland sun dai na ba da taimakon siyasa da kuɗaɗe da "makamai" ga ƙungiyoyin.
Tana kuma son su dawo da sayar ma ta da makamai da miƙa mata mutanen da ake zargi na da alaƙa da ta'addanci.
Bayan shafe sa'o'i na tattaunawa a taron Nato da aka gudanar a Madrid a karshen Yuni, ministocin ƙetare daga Sweden, Finland da Turkiyya sun sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro na haɗin-gwiwa domin shawo kan batun tsaron da Turkiyya ke nuna damuwa a kai.
Shugaban Nato Jens Stoltenberg ya ce Sweden ta amince ta mutunta bukatar Turkiyya na miƙa mata mutanen da ake zargi na da alaƙa da ta'addanci.
Ƙasashen biyu sun kuma ce za su dage takunkumin cinikin makamai ga Turkiyya, a cewarsa.
A nata ɓangaren kuma, Turkiyya za ta janye adawarta kan ƙasashen na shiga cikin kawancen Nato.











