Matsalar abinci: Ko Ukraine za ta iya ciyar da duniya duk da yaƙin da ake yi?

Asalin hoton, Nadiya Stetsiuk
- Marubuci, Daga Stephanie Hegarty
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Population correspondent
Manoman Ukraine sun girbe amfanin gonar da ya kai tan miliyan 20 amma ba za su iya fitar da shi kasuwar duniya ba, kuma ga shi lokacin sabuwar shuka ya kawo kai. Me za a yi domin kai wa mutane da ke matsananciyar bukata abincin, yayin da farashin abinci ya yi tashin gwaron zabo a duniya?
A farkon watan Fabrairu, Nadiya Stetsiuk take cike da farin ciki da fatan samun ingantacciyar shekara. An samu kyakkyawan yanayi tun shekarar 2021, ta kuma samu yabanya mai kyau domin masara da alkama da ta shuka a karamar gonarta da ke tsakiyar yankin Cherkasy da ke Ukraine sun yi kyau.
Farashin kayayyaki a kasuwannin duniya sun tashi, kuma hakan take kusan kowacce rana, don haka sai ta adana amfanin gonar da nufin saidawa nan gaba. Kwatsam sai Rasha ta kai wa kasar mamaya.
Yakin bai daidaita yankin da ta fito ba, kamar sauran kashi 80 cikin 100 na gonakin kasar. Har yanzu sojin Ukraine ne iko da yankin, sai dai radadin yakin ya afka wa gonarta.
"Tun fara mamayar, ba mu sayar da ko kwayar hatsi ba. Farashin a nan rabi ne kan wanda muka saba saidawa kafin fara yakin nan," in ji Mrs Stetsiuk. "Za a fuskanci karancin abinci a Turai da duniya baki daya, a nan lamarin ba haka yake ba, saboda babu hanyar da za mu fitar da abincin wasu kasashe."
Ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba ya bayyana hakan da "bita da kulli" wata tayin Rasha na dage haramcin rufe tashar ruwan Ukraine, shi kuma a janye wa kasarsa takunkuman da aka kakaba ma ta.
Ukraine ta kasance sahun gaba a kasashe masu fitar da abinci a duniya, tana bada gudummawar kashi 42 cikin 100 na 'ya'yan sanfulawa (sunflower) da ake amfani da shi don samar da man girki, sai kashi 16 na masara da kashi 9 na alkama.
Wasu kasashen sun dogara kacokam da Ukraine. Kashi 80 cikin 100 na alkamar da kasar Labanun ke amfani da shi daga Ukraine yake fitowa, da kuma kashi 76 na man girki da aka sarrafa da sanfulawa (sunflower).
Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya da ke ciyar da mutanen da tsananin yunwa ke neman hallakawa a kasashe kamar Habasha da Afghanistan da kuma Yemen, yana sayen kashi 40 cikin 100 na alkamar da ake ciyar da wadannan kasashe.
Gabanin yakin, an samu raguwar safarar abinci a duniya. Matsanancin fari da aka yi fama da shi ya janyo koma-baya ta fannin noman alkama da man girki a kasar Canada a shekarar da ta gabata, yayin da waken soya da masa suka yi karanci a kudancin Amurka.
Annobar korona ta yi mummunar illa. A kasashen Malaysia da Indonesia raguwar ma'aikata na nufin raguwa a fannin manja, wanda ya janyo tashin gwauron zabbin farashin man girki a kasuwannin duniya.
A farkon shekarar nan, farashin yawancin kayan abinci a duniya ya yi matukar tashi. Yawancin mutane na fatan amfanin gona daga Ukraine zai sassauta karancin abincin da ake fama da shi.
Sai dai kash!!! mamayar Rasha ta toshe wannan dama. Ministan noma a Ukraine ya ce a yanzu haka akwai tan miliyan 20 na abinci nau'in hatsi a kasar da babu damar fitar da su waje.
Gabannin yakin, kashi 90 na kayan abincin da Ukraine ke fitarwa tana amfani ne da tashar ruwan Baharul Aswad, da ke iya daukar manyan tankokin hatsi, da yin tafiya mai nisa zuwa China da Indiya, kuma ana samun riba mai tarin yawa.
Amma a halin yanzu duka an rufe su. Rasha ta kwace iko da yawancin tashoshin ruwan Ukraine, yayin da ta toshe saura da hana manyan jiragen ruwan dakon kaya 20 motsi, ciki har na yaki hudu.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban shirin samar da abinci na MDD David Beasley ya yi kira ga kasashen duniya su shirya jerin gwano domin bude tashoshin da Rasha ta toshe.
"Idan babu fahimta a Rasha, ta fannin soji babu wani abu da zai fuskanci turjiya," in ji Jonathan Bentham, mai sharhi kan sha'anin safara ta ruwa kuma jami'in Cibiyar nazari kan harkokin kasashen waje. Jerin gwanon tawagar na bukatar rakiya ta sama, da samun karfi ta sama da ta ruwa, sannan za a cimma hakan ta amfani da siyasa.
"Idan ana son kwantar da hankula, ya kamata a bukaci kasashen da ke Baharul Aswad kamar Romania da Bulgeria su yi hakan. Sai dai watakila ba su da karfin yin haka. Don haka aka bukatar shigo da kasashe mambobin Nato."
Hakan zai kawo shigar Turkiyya, wadda ke iko da wani bangare na tekun a wani yanayi mai sarkakiya. Tuni ta bayyana ba za ta taba bari a yi amfani da shi wajen safarar jiragen yaki ba.
Rasha ta yi musu tayin ba da wata kafa ta shigar da jiragen kayan abinci, ita kuma a saka mata da cire takunkuman da ke kanta, hakan na zuwa ne bayan tattaunawar da Tarayyar Turai ta jagoranta a ranar Laraba wadda ta sake lafta wa Rasha sabbin takunkumai, babu kuma wata alama ta sassauci ko sauya matsaya.
Ko da kuwa an kawo karshen yakin, za a dauki watanni ko shekaru kafin tekun Baharul Aswad ta koma daidai, kamar yadda Mr Bentham ya bayyana, sakamakon yadda Ukraine ta kare tashar ruwan ta da mayan nakiyoyi da wasu dabaru da suka yi ta yadda jiragen da ba su aminta da su ba za su nutse.

Asalin hoton, Getty Images
A yanzu dai za a iya fitar da kayan abincin daga Ukraine ne kadai ta hanyar amfani da hanyar mota ko a bi ta kogin Danube.
A makon da ya wuce, Tarayyar Turai ta sanar da shirin zuba jarin biliyoyin yuro a fannin ayyukan baben more rayuwa. Sai dai makofciyar Mrs Stetsiuk, Kees Huizinga - wanda ya mallaki gona eka 15,000 ya ce hakan bai wadatar ba.
Ya na ta kokarin fitar da kayan abincin tun farkon fara yakin, cike-ciken takardu da EU ta bukata ya janyo tsaiko da gajiyawa, ga kuma dogayen layukan da ke iyakar kasar da ya kai kilomita 25, wato mil 16.
Lamarin akwai gajiya da karaya, cikin makonni uku da suka wuce, da kyar da sidin goshi Mr Huizingaya iya fitar da tan 15 na hatsi.
In da zai yi amfani da tashar ruwan Odesa cikin awoyi kalilan zai fitar da su maimakon makonni.

Asalin hoton, Getty Images
Duk da cewa an fi batun karancin alkama a duniya, yawancin hatsin da Ukraine ke da shi dai masara ce. Wannan kuma ya samo asali saboda dalilai biyu, kamar yadda mai sharhi kan abinci dangin hatsi Elena Neroba a Ukraine ta bayyana.
Ta yi amanna da cewa, manoman Ukraine sun kagu su sayar da alkamarsu, saboda sakamakon tuna zamanin bakin fari da tsananin yunwa na Holodomor a shekarar 1938, lamarin da ya hallaka miliyoyin 'yan kasar. Sannan 'yan Ukraine ba su fiye cin masara ba.

Asalin hoton, Getty Images
Har yanzu Mrs Stetsiuk tana da kusan kashi 40 cikin dari na abin da ta noma a shekarar da ta wuce, wanda take tarawa kadan-kadan a rumbunta, kafin kaka mai zuwa. Ta ce matukar aka ci gaba da tafiya a haka, tabbas za a shiga mawuyacin hali sakamakon karancin abinci a shekara mai zuwa.
"Muna son ci gaba da noma. Muna son taimakawa, mu samar da abinci ga mutane."
Amma ta ce cikin kankanin lokaci, Rasha ta janyo musu koma-baya, ta mayar da su shekaru 20 a baya lokacin da aka yi fama da rashin wadata.











