Waɗanne irin ƙalubale ne a gaban Sarki Charles III?

Asalin hoton, Getty Images
A takarda, ba a cika samun miƙa mulki ya tafi lami lafiya kamar na Masarautar Birtaniya. Ƙasa da sa'a 48 bayan mutuwar Sarauniya Elizabeth II, aka ayyana Sarki Charles III a matsayin sabon sarkin Birtaniya. Sai dai abubuwa ba su da sauƙi kamar yadda ake gani: Charles ya hau kan karaga a daidai lokacin da Birtaniya da masarautarta ke fuskantar ƙalubale.
Masana tarihin da BBC ta tattauna da suna ganin sabon sarkin zai fuskanci ƙalubalen da ba a taɓa ganin irin sa ba wanda zai haska mulkinsa da waɗanda za su biyo baya.
Daga tunkarar tasirin matsalar makamashi a ƙasar zuwa fuskantar sauya ra'ayin mutane game da masarautar bayan shekara 70 da mahaifiyarsa ta yi tana mulki.
Ga wasu daga cikin manyan batutuwan da ka iya buƙatar kulawar sabon sarkin.
Masarauta mai sanin ya kamata
Miliyoyin iyalai a Birtaniya na fuskantar ƙarancin iskar gas a wannan lokaci na hunturu saboda hauhawar farashin makamashi sanadin yaƙin da ake yi a Ukraine.
Hasashen da aka yi na cewa kusan mutum miliyan 45 ne za su shiga garari wajen biyan buƙatunsu - kusan kashi biyu bisa uku na al'ummar ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
Da alama irin wannan yanayin ka iya sa a sanya ido kan kuɗaɗen masarautar saɓanin da. Koma kafin yaƙin, akwai raɗe-raɗin cewa tsohon Yariman Wales yana son rage yawan bukukuwan masarautar, wato naɗin sarautarsa.
Jaridar Daily Telegraph ta yi hasashen cewa a ranar 13 ga watan Satumba taron ba zai kasance irin na marigayiya sarauniya ba da aka yi a 1953 - wanda shi ne biki irinsa na farko da aka nuna ta talabijin.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Da take ambato wasu majiyoyi daga gidan sarautar, jaridar ta ce bikin naɗin Charles III, wanda ba a tsammanin za a yi shi kafin watan Yunin baɗi, zai kasance taƙaitacce, babu kashe kuɗi sannan zai haɗa al'adu daban-daban domin nuna banbancin al'ummar Birtaniya.
A baya Charles ya yi magana kan sha'awarsa ta yi wa masarautar garambawul abin da ka iya zama taƙaita masarautar ga wani rukuni na masarautar, inda sarki da mai ɗakinsa Camilla da Yarima William da matarsa Catherine za su kasance a tsakiyarta.
"Tana iya yiwuwa muga an taƙaita abubuwa, musamman bikin naɗin," kamar yadda masaniyar tarihin masarautar Kelly Swab ta shaida wa BBC.
"Dole ne a ga iyalin masarautar domin sanin abin da ke wakana a ƙasar a irin wannan mawuyacin lokaci," in ji ta.
Ƙudaden gidan sarautar wani lamari ne mai rikitarwa wanda a mafi yawan lokuta ake muhawara a kai: kuɗaɗen na zuwa ne daga harajin da mutane ke biya duk shekara da ake kira Sovereign Grant.
Tsakanin 2021 zuwa 2022, an sa tallafin kan $99.8m - ke nan kowane mutum a Birtaniya na biyan $1.49 amma bai haɗa da kuɗaɗen tsaro ba na iyalan masarautar.
Raguwar martaba

Asalin hoton, Getty Images
Goyon baya ga masarautar ya ragu matuƙa cikin sama da shekara 30, a cewar nazarin ra'ayin jama'ar Birtaniya wanda a kai a kai yake duba ra'ayin asu ƴan Birtaniya game da wasu yan gidan sarautar.
Nazarin baya-bayan nan da aka wallafa a 2021 ya nuna kashi 55 na ƴan Birtaniya ne kaɗai suke ganin masarautar na da matuƙar muhimmanci. A shekarun baya, goyon bayan na tsakanin kashi 60 da kashi 70 cikin 100.
A Mayun bana, Charles ya kasance na uku a jerin mutanen da aka fi so a ƴan gidan masarautar bayan Sarauniya da babban ɗansa, Yarima William.
Yayin da ƙuri'ar jin ra'ayin da aka yi bayan mutuwar Elizabeth II sun nuna ƙaruwar goyon baya ga sabon sarki, akwai alamun akwai aiki ja a gaban Charles III game da martabar masarautar.
"Ɗaya daga cikin ƙalubale ga sarki Charles III shi ne ƙara wa masarautar armashi domin janyo ra'ayin matasa," in ji masanin tarihin masarautar Richard Fitzwilliams.
Ra'ayin Fitzwilliams ya yi dai-dai da na ra'ayin Jama'ar Birtaniya da ya nuna a 2021, kashi 14 cikin 100 ne kaɗai masu shekara 18 zuwa 34 suka nuna yana da matuƙar muhimmanci ga Birtaniya ta samu masarauta yayin da waɗanda shekarunsu suka haura 55 suka kasance kashi 44 cikin 100.
A cewar ra'ayin jama'a na YouGov, da aka yi a watan Mayu, kashi 27 cikin 100 na al'umma na goyon bayan a rushe masarautar - hakan ƙari ne kan kashi 15 cikin 100 da aka saba samu a wannan ƙarnin. Sannan an fi samun rashin gamsuwa daga ɓangaren matasa.
Kelly Swab ta ce "abubuwa da dama sun sauya tun 1952" (shekarar da Elizabeth II ta zama sarauniya). Ta yi magana ne kan zanga-zangar nuna ƙin jinin masarauta da aka gudanar a ƴan kwanakin baya-bayan nan.
"Irin abin da Sarki Charles ya kamata ya yi la'akari da su ke nan."
Rashin bayyana ra'ayi

Asalin hoton, Getty Images
Sarki Charles III shi ne jagora a Birtaniya. Amma a ƙarƙashin kundin tsarin mulkin masarautar Birtaniya, iyalan masarautar na tsame kansu daga siyasa.
A baya Charles yana magana kan batutuwa daban-daban da suka shafe shi. A 2015, an gano ya rubuta wasu wasiƙu 10 zuwa ministoci inda yake bayyana damuwarsa kan batutuwan da suka shafi kuɗi da sojoji da maganin gargajiya.
Shin zai sauya? Wani ƙwararren masanin kundin tsarin mulki Farfesa Vernon Bogdanor na ganin zai sauya.
"Ya sani tun a baya cewa tsarinsa zai sauya. Jama'a ba za su so sarki mai kamfe ba," in ji Farfesa Bogdanor.
A ranar 12 ga watan Satumba, yayin da yake jawabi ga ƴan majalisa, sabon sarkin tuni ya bada alamun sauya abubuwansa. Sannan da sanin cewa akwai abubuwa da dama da ba zai ci gaba da yinsu ba."
Commonwealth da zamanin mulkin mallaka

Asalin hoton, Getty Images
Bayan mutuwar mahaifiyarsa, Sarki Charles III ya zama shugaban ƙungiyar commonwealth, mai ƙasashe mambobi 56, galibinsu waɗanda Birtaniya ta mulka. Shi ne kuma shugaban ƙasashe 14 har da Birtaniya - da suka haɗa da Australiya da Canada da Jamaica da New Zealand.
A ƴan shekarun nan ne wasu ƙasashen Commonwealth suka fara muhawara kan dangantakarsu da masarautar Birtaniya. A wani ɓangare na wannan mataki ne Barbados ta yanke shawarar zama Jamhuriya a ƙarshen 2021, matakin da ya cire marigayiya Sarauniya a matsayin shugabar ƙasar tare da kawo ƙarshen tasirin da Birtaniya take da shi kan tsibirin.
Zagayen Yarima William zuwa yankin Carribean a farkon 2022 ya janyo zanga-zangar adawa da mulkin mallaka inda suka buƙaci Turawa su nemi afuwarsu.
Firaministan Jamaica, Andrew Holness a bainar jama'a ya faɗa wa masarauntar cewa ƙasar za ta yi ta samun ci gaba. Sean Coughlan, wani wakilin BBC a masarautar na ganin sake fasalin alaƙarta da ƙasashen commonwealth zai kasance gagarumin ƙalubale ga Sarki Charles.
Ƙwararren Sarki

Asalin hoton, Getty Images
Charles III shi ne sarki mafi tsufa da aka ayyana a matsayin sarki a Birtaniya. Ɗaya daga cikin tambayoyin kan yadda yake tafiyar da mulkinsa, shi ne ya nauyin ayyukan masarautar da ake sa ran zai tafiyar da su da kansa za su kasance?
Akwai jita-jita da dama cewa ɗansa kuma magajinsa, Yarima William, zai riƙa tafiyar da wasu ayyukan masarautar musamman tafiye-tafiye zuwa kasashe.
Sarauniya Elizabeth II ita ma da kanta ta ajiye batun tafiye-tafiye zuwa wasu ƙasashen tun tana shekaru 80.
"Charles Sarki ne da ya tsufa. Ba zai iya komai shi kaɗai ba," in ji Kelly Swab.
Cike ƙatoton giɓi

Asalin hoton, Getty Images
Elizabeth II ta kasance basarakiya da ta yi suna ganin yadda mutane suka riƙa tururuwar nuna jimami a sassan kasar bayan mutuwarta.
Wannan kaɗai ma ƙalubale ne ga sabon sarki - a cewa masaniyar tarihi Evaline Brueton. Ta ba da misali da yadda Edward VII ya gaji sarauta a 1901 sakamakon mutuwar Queen Victoria, wata basarakiyar da al'umma ke ƙauna.
"Akwai kamanceceniya tsakanin yanayin da muke a ayznu da kuma na ƙarshen mulkin Victoria," in ji Brueton.
"Edward da Charles dukkansu sun karɓi ragama ne a lokacin da ake samun sauyi a tsakanin al'ummar Birtaniya. Sannan dukkansu ba su kai farin jinin mahaifansu ba."
Edward VII ya yi mulki ne tsawon shekara tara (1901 - 1910) amma ana tunawa da shi a matsayin sarkin da ya tsunduma cikin ƙoƙarin diflomasiyya wanda ya aza harsashi ga shahararriyar yarjejeniyar Entente Cordiale da aka ƙulla tsakanin Birtaniya da Faransa a shekarar 1904.











