Me Seyi Tinubu ke nema a ziyarce-ziyarcensa zuwa jihohin arewa?

Seyi Tinubu

Asalin hoton, Bashir Ahmed/Facebook

Lokacin karatu: Minti 4

A karon farko wani ɗa ga shugaban ƙasa mai ci a Najeriya yake wani rangadi da ya kira na ƙulla zumunci da matasa irinsa da sauran al'ummar arewacin ƙasar.

Oluwaseyi Afolabi Tinubu ko kuma Seyi kamar yadda aka fi sanin sa da shi, ya kai ziyara a jihohin arewacin ƙasar da suka haɗa da Kano da Katsina da Kaduna da Neja da kuma Sokoto, inda ya yi buɗa baki da matasa sannan ya gana da dattawa da malamai da ƴan siyasa.

Masu lura da al'amuran yau da kullum dai na yi wa ziyarar kallon wani abu mai kama da siyasa da ba zai rasa nasaba da kakar zaɓe mai zuwa a 2027 ba.

Abubuwan da Seyi ya yi lokacin ziyarar

.

Asalin hoton, facebook seyi

Bayanan hoto, .
  • Seyi ya buɗe baki da matasa a Kano, inda aka gayyato ɗaruruwan matasa daga jihar domin cin abincin buɗe baki kuma a nan ne ya haɗa ɓangarori masu hamayya da juna a jihar a wuri guda - an ga ƴaƴan shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje da ɗan gidan gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da ba a ga maciji da juna.
  • Ya ƙaddamar da ƙungiyarsa ta tallafa wa marasa galihu mai suna RHYE.
  • Ɗan gidan shugaban ƙasar ya kai ziyara ga gwamnan Kano da Alhaji Aminu Ɗantata da kuma limamin masallacin Al-Furqan, Dr Bashir Aliyu Umar
  • A jihar Kaduna, Seyi ya kai ziyara wurin tsohon shugaban Najeriya, Muammadu Buhari, da gwamnan jihar Uba Sani da Sarkin Zazzau, Alhaji Nuhu Bamalli da Sheikh Ahmad Abubakar Gumi da kuma buɗe baki da dandazon matasa.
  • Da yake jihar Neja kuwa, Seyi Tinubu ya gana da tsoffin shugabannin sojin Najeriya Janar Ibrahim Babangida da Janar Abdussalam Abubakar da kuma
  • A jihar Sokoto, Seyi ya kai ziyara ga fadar Mai Martaba Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III baya ga ganawa da shugabannin siyasa da kuma matasa.

Mece ce manufar ziyarar ta Seyi?

Seyi Tinubu

Asalin hoton, Seyi/Facebook

Bayanan hoto, .

Farfesa Tukur Abdulƙadir malami a jami'ar jihar Kaduna kuma mai fashin baƙi kan al'amuran siyasa ya ce ziyarar ta Seyi Tinubu abu ne da ba a saba gani ba.

"Za a ce kusan wani sabon al'amari ne domin ba safai akan ga ɗan gidan shugaban ƙasa na yin irin waɗannan ziyarce-ziyarce ba. Ko a baya ma mun ga yadda ya je jihar Borno lokacin ambaliyar da jihar ta fuskanta.

Ƙila yana ganin irin yadda matakan da gwamnatin da mahaifinsa ke jagoranta ke fito da su waɗanda kuma ke gallaza wa al'umma. Saboda haka wataƙila ziyarar wani mataki ne na jan hankali da haƙurtar da jama'a da kuma neman goyon bayan al'umma ga gwamnatin."

Shi ma Dakta Mukhtar Bello Maisudan masanin kimiyyar siyasa kuma malami a jami'ar Bayero da ke Kano, ya ce lallai ziyarar ta siyasa ce.

"Sako shi Seyi Tinubu a tsarin kamfe na jam'iyyar APC a hanƙoronta na 2027 na nufin wani sabon salo na amfani da matasa. Idan ka duni gwamnatin da ma akwai matasa a cikinta kuma shi Seyi ne ke kula da matasan". In ji Dakta Bello Maisudan.

Dangane kuma da yadda aka ga Seyi da ƴaƴan Dr Abdullahi Umar Ganduje da na Aba Kabir Yusuf tare suna raha Dakta Maisudan ya ce hakan ma yana ƙunshe da wani ɓoyayyen al'amarin da jama'a ba su sani ba.

"Kasancewar ƴaƴan ƴan hamayyar tare da ƙunshe da manufa ta ɓoye da jama'a ba su sani ba. Tafiyar na da manufofi da dama da suka haɗa da janyo ra'ayin masu hamayya a jiha kamar Kano zuwa jam'iyyar APC. Duk da dai gwamnatin Kano ba ta ce komai dangane da ziyarar amma da ma akwai raɗe-raɗin cewa ana zawarcin gwamnatin ta NNPP." In ji Dakta Mukhtar Bello Maisudan.

Ko ziyarar za ta yi tasiri?

Seyi Tinubu

Asalin hoton, Seyi/Facebook

Bayanan hoto, .

Farfesa Tukur Abdulƙadir ya ƙara da cewa tabbas ziyarce-ziyarcen na Seyi ba za a raba su da batun siyasa ba a Najeriya.

"Tabbas yana da alaƙa da siyasa sai dai kuma zan iya cewa ba za a iya ganin tasirinsa ba har sai lokacin da aka kaɗa kugen siyasa musamman bisa lura da yanayin da ake ciki yanzu na mtasin tattalin arziƙi. Saboda haka abin da kawai zai iya yin tasiri a zaɓen 2027 shi ne hanypyin da aka bi wajen kyautata wa ƴan Najeriya."

Shi kuwa Dakta Mukhtar Bello Maisudan na jami'ar Bayero ya ce ziyarar ka iya yin tasiri ta fuska biyu.

"Na farko ziyarar ta Seyi za ta iya yin tasiri ta fuskar jan matasa a jiki a nemi ƙuri'arsu a zaɓen 2027 sannan abu na biyu za a iya zawarcin masu hamayya zuwa jam'iyya mai mulki.

Amma dai ba za ka ce ga haƙiƙanin abin da zai faru a nan gaba ba. Sai dai mu jira mu gani amma kuma lallai al'amarin na da alaƙa da siyasa." In ji Dakta Mukhtar Bello Maisudan.