Ko harin Isra'ila a Qatar zai gurgunta alaƙarta da Amurka?

    • Marubuci, Luis Barrucho
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Global Journalism
  • Lokacin karatu: Minti 5

Masana sun shaida wa BBC cewa harin da Isra'ila ta kai kan manyan jagororin Hamas a Doha, babban birnin Qatar zai iya lalata ƙoƙarin tsagaita wuta a Gaza tare da yin illa ga alaƙar Amurka a Gabas ta Tsakiya.

Isra'ila ta bayyana harin da ta kai a tsakiyar birnin Doha a matsayin "hari ne takamaimai kan shugabannin Hamas".

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa wannan hari martani ne kan harin bindiga da aka kai a Urushalima a ranar da ta gabata wanda ya kashe mutum shida, da kuma rawar da Hamas ta taka a hare-haren da aka kai kan Isra'ila a ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Sai dai masana sun ce abin da ba za a iya daƙilewa ba shi ne sakamakon wannan harin a nan gaba.

Damar samun tsagaita wuta ta dusashe

Hugh Lovatt, ƙwararren masanin harkokin Gabas ta Tsakiya a majalisar Turai (ECFR), ya ce harin da Isra'ila ta kai kan shugabannin Hamas ya yi wa tattaunawar tsagaita wuta da Amurka ke goyon baya babbar illa wajen kawo ƙarshen yaƙin Gaza.

A halin yanzu, Qatar tare da Masar da Amurka ne ke shiga tsakanin Hamas da Isra'ila domin cimma yarjejeniyar sakin fursunoni da kuma tsagaita wuta a Gaza.

Lovatt ya ce, "Kashe mutanen da kake tattaunawa da su kan tsagaita wuta na nuna cewa babu wata alamar za a cimma yarjejeniya."

A cewar rahotanni, mutum shida daga cikin wakilan Hamas sun mutu a harin da Isra'ilar ta kai a Doha, ciki har da ɗan shugaban Hamas a Gaza, Khalil al-Hayya, da mai kula da ofishinsa, yayin da manyan shugabannin ƙungiyar suka tsira.

Lovatt ya ce, "A takaice, Isra'ila ta tarwatsa tawagar Hamas a lokacin da suke tattaunawa kan sabon shirin Amurka na kawo ƙarshen yaƙin Isra'ila da Gaza."

Wannan shi ne karo na farko da Isra'ila ta kai hari kan shugabannin Hamas a ƙasar Qatar, duk da cewa sun daɗe suna da matsuguni a can.

Amma Lovatt ya ce ba sabon abu ba ne, inda ya tuna cewa Isra'ila ta kashe shugaban siyasar Hamas, Ismail Haniyeh, a bara lokacin da shi ne babban mai shiga tattaunawar tsagaita wuta.

Ya ƙara da cewa, wannan matakin ya nuna babu wata alama cewa Isra'ila na sha'awar tsagaita wuta.

Isra'ila ta taɓa kai irin wannan hari kan shugabannin Hamas a Lebanon da Siriya a baya.

Harin ba Gaza kaɗai zai shafa ba

Masana sun ce tasirin harin da aka kai ranar Talata ba Gaza kaɗai zai shafa ba.

Sun bayyana cewa harin ya kafa sabon tarihi.

Hugh Lovatt ya ce: "Ba wannan ne karo na farko da Isra'ila ta kai hari a wani babban birnin ƙasar Larabawa ba, amma shi ne karo na farko da ta kai hari a ƙasar da ke da babbar alaƙa da Amurka.

Qatar ba Iran ba ne, ba kuma Lebanon ba ne. Akwai wani babban sansanin sojin saman Amurka a ƙasar, kuma tana da manyan hannun jari a ƙasashen Yamma."

A jawabin da aka yi a Fadar White House bayan harin, mai magana da yawun shugaban ƙasa Karoline Leavitt ta ce Isra'ila ta sanar da gwamnatin Trump game da harin, amma ba a bayyana ko an gargaɗe su ba kafin harin, ko a lokacin da ake kai shi, ko kuma bayan an kai harin.

Ta kuma ruwaito Shugaba Donald Trump yana cewa harin Isra'ila a Doha "ba zai kawo ci gaba ga manufofin Isra'ila ko na Amurka ba," sai dai ya kara da cewa kawar da Hamas "abu ne mai muhimmanci."

Sai dai Dr. Sanam Vakil, daraktar shirin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka a Chatham House da ke Landan, ta ce wannan hari ya raunana tsaron Qatar tare da bayyana raunin ƙawancen ƙasashen yankin Gulf.

Ta ce, "Idan har gwamnatin Amurka ta goyi bayan wannan hari kan shugabannin Hamas a Doha, hakan zai shafi dangantakar Qatar da wasu ƙasashe. Ba za su katse zumunci da Amurka ba, amma tabbas za su ji cewa sun zama masu rauni a wannan sabon yanayi."

Ta ƙara da cewa wannan lamari ya wargaza amanar da ake zaton akwai a lokacin da ake yin ƙawance tsakanin ƙasashe.

"Akan yi tunanin cewa idan ana ƙawance, ƙasashe ba za su kai wa junansu hari ba kuma ba za su amince wasu su kai wa ƙawayensu hari ba," in ji ta.

Dr. H. A. Hellyer na cibiyar nazarin tsaro ta Birtaniya (RUSI), ya amince da hakan, inda ya ce tasirin wannan hari na nufin cewa Qatar da sauran ƙasashen yankin za su fara tambayar kansu: "Me kariyar tsaro na Amurka a ƙasashensu ke nufi a zahiri, idan har Isra'ila na iya yin abin da take so cikin gadara?"

Dr. Vakil ya kuma nuna ƙarancin ganin girman Qatar a cikin ƙawancenta da Amurka, duk da cewa akwai sansanin sojin saman Amurka na al-Udeid a cikin ƙasar kuma tana shiga tsakani a rikicin Isra'ila da Hamas.

A cewarsa, "Qatar tana matuƙar dogaro da Amurka wajen tsaronta, wannan ya sa Qatar ta zama kamar fursuna kuma ya nuna iyakacin tasirinta."

Tun shekaru da dama, an yi imanin cewa Isra'ila ba za ta kai hari kan jami'an Hamas a Qatar ba domin martaba fagen tattaunawa da ƙasar ke samarwa.

Amma Dr. Vakil ya ce yanzu Isra'ila ta watsar da wannan zato, tana mai fifita abin da take ganin dama ce ta soja.

Abubuwan da hakan zai haifara a yankin

Dr. Vakil da Mr. Lovatt duka sun yi gargaɗin cewa sakamakon harin na iya yin tasiri mai zurfi a yankin.

Lovatt ya ce; "Jami'an Larabawa sun fara nuna damuwa sosai game da abin da ke faruwa kuma Isra'ila ba kawai tana ƙara nuna ƙarfinta ba ne, har ma tana aiki ta yadda ke ƙara kawo rashin daidaito ba tare da wani takura daga Amurka ko Turai ba."

Dukkan su, sun ce wannan damuwa na iya sa ƙasashen yankin su ƙara karfafa ƙarfin sojojinsu.

Lovatt ya ce; "Wannan ba yana nufin za su kai hari kan Isra'ila ba, amma suna son su samu ikon kare kansu."

A ƙarshe, masanan biyu sun jaddada cewa sakamakon mummunan harin da ya faru ranar Talata zai yi tasiri mai yawa.

Lovatt ya ƙare da cewa: "Daya daga cikin manyan waɗanda za su sha wahala daga abin da ke faruwa ba kawai Isra'ila ko Falasɗinawa ba ne, har da yankin gaba ɗaya da kuma Turai kanta."