Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mene ne ra'ayin ƙasashen Larabawa kan ƙungiyar Hamas a Gaza?
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce yana shirin ''ƙwace cikakken ikon Zirin Gaza tare da kakkaɓe ƙungiyar Hamas.''
Sai dai, a wata hira da gidan talabijin na Fox News na Amurka, ya nuna cewa Isra'ila ba ta da niyyar "ci gaba da zama a yankin a matsayin mai tafiyar da mulki."
Jawabin na Netanyahu ya ƙara matsin lamba kan Hamas, wadda tuni take fuskantar matsi daga ƙasashen yankin da sauran ƙasashen duniya kan ta ajiye makamanta
Sai dai cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ƴan kwanakin nan, Hamas ta yi watsi da buƙatar, tana mai cewa ba za ta ɗauki wannan mataki ba, har sai an amince da kafa ƙasar Falasɗinawa tare da kawo ƙarshen mamayar yankin Falasdinawa da Isra'ila ke yi.
A baya-bayan nan dai ƙasashen yankin da na duniya na ci gaba da kiraye-kiraye ga kungiyar ta ajiye duka makamanta, domin bayar da damar fara tattaunawa kan yarjejeniyar da za ta kai ga amincewa da ƙasashe biyu.
A babban taron duniya da aka gudanar cikin watan Yulin da ya gabata a shalkwatar Majalisar Dinikin Duniya da ke birnin New York na Amurka - wanda Saudiyya da Faransa suka jagoranta - ƙasashe 17 ƙari kan Tarayyar Turai da kungiyar ƙasashen Larabawa sun bayar da shawarar hadin gwiwa da za ta kawo zaman lafiya tare da amincewa da kafa ƙasashe biyu.
Kumdin shawarwarin da aka cimma a taron na New York, mai shafuka 42, ya yi kira ga Hamas ta janye daga ikon Zirin Gaza tare da miƙa makamansu ga hukumar tsaron Falasɗinawa ta PA.
Daga cikin ƙasashen da suka sanya hannu a taron har da Masar da Qatar, wadanda koyauashe ke cikin masu shiga tsakani a Gaza.
To sai dai, Isra'ila da Amurka ba su sanya hannu kan shawarar ba, hasalima ba su halarci taron ba.
'Hamas za ta ci gaba da faɗa'
A lokacin wata hira da gidan talbijin na Al Jazeera Mubasher, daga birnin Doha, shugaban Hamas, Ghazi Hamad ya ce ƙungiyar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba, ko da kuwa ''harsasanta za su ƙare,'' saboda ita ce ''makamin yaƙin Falasɗinawa.''
Ya jaddada cewa a shirye Hamas take don ci gaba da fafutika har sai an kafa ƙasar Falasɗinawa.
Farfesa Hussam Al-Dajani masanin kimiyyar siyasa a Jami'ar Al-Ummah da ke birnin Gaza na ganin cewa kafafen yaɗa labarai na mayar da hankali kan sashe na 11 cikin shawarwarin da aka cimma a New York.
Sashen ya yi tanadin cewa ''iko da tabbatar da bin doka da tsaron duka yankunan Falasɗinawa zai zama haƙƙi ne kawai da ya rataya a wuyan Hukumar Falasɗinawa.''
Haka kuma sashen ya yi kira ga ''Hamas daga ikon Zirin Gaza tare da miƙa wa Hukumar Falasɗinawa makamanta.''
Al-Dajani ya ce akwai sassa 41 a cikin shawarwarin da aka cimma, inda wasu daga cikinsu ke kira da amincewa a kafa ƙasar Falasɗinawa da za ta ci gaba da zama lafiya da Isra'ila.
Ya tabbatar wa BBC cewa ''Idan har aka aiwatar da sauran shawarwarin, sashe na 11 zai kasance na ƙarshe da za a amince.''
Farkon gwamnatin Falasɗinawa
Amurka da Birtaniya da wasu ƙasashen Yamma sun ayyana Hamas a matsayin ƙungiyar ta'addanci.
To sai dai Hamas ta faɗa, ba sau daya ba, ba sau biyu ba, cewa za ta miƙa makamanta ga hukumar Falasdinawa ne kawai idan an amince da kafa ƙasar Faalasɗinawa.
Sai dai har yanzu ƙungiyar na da tsarin gwamnati a Zirin.
Sabon sashen tsaronta da aka fi sani da ''Arrow'' na aiki bisa manufar ƙungiyar na wanzar da zaman lafiya da hana sace kayan agajin da suka shiga Zirin.
To amma bayan wata 22 da ƙungiyar ta kai harin ranar bakwai ga watan Octoban 2023, tare da matakin martani da Isra'ila ta ɗauka, Hamas da tsagin sojinta sun gajiya.
Dangane da haka, farfesa Yossi Mekelberg, babban mai ba da shawara a Chatham House, wata cibiyar bincike da ke Landan, ya ce Hamas ba ta yi la'akari da munin sakamakon harin na ranar 7 ga Oktoba ba.
A wani ɓangaren kuma, wasu majiyoyin cikin gida a Gaza sun bayar da rahoton cewa har yanzu Hamas na da makamai, amma alburusanta sun fara ƙarewa.
Majiyoyin sun ƙara da cewa mayaƙan na wannan yunƙuri na sake amfani da ragowar makaman da suka yi amfani wajen kai wa Isra'ila hare-hare, waɗanda yawancinsu bama-bamai ne da ba su fashe ba, domin samun ababen fashewa da zai ba su damar yin bama-bamai na gida don kai wa sojojin Isra'ila hari.
Isra'ila na hana ƴanjarida shiga Gaza, don haka ba za mu iya tabbatar da wannan ba.
A halin da ake ciki kuma, Falasɗinawa a Gaza na nuna ɓacin ransu ga Hamas, yayin da Amnesty International ta yi Allah wadai da matakin ƙungiyar na "danniya da tsoratarwa" kan masu zanga-zangar kyamar Hamas a watan Mayun da ya gabata.
Ra'ayin ƙasashen Larabawa
Ƙungiyar ƙasashen Larabawa mai mambobi 22 , ciki har da ƙasashen da ake yi wa kallon ƙawayen Hamas, kamar Qatar sun sanya hannu kan yarjejeniyar New York, da ke kiran ƙungiyar ta ajiye makamai.
Farfesa Mekelberg ya yi imanin cewa Isra'ila da Amurka na ɗaukar matakin da suka saba kan Hamas.
Sai dai ya ce muryar ƙasashen Larabawa ta sauya. Ya lura cewa ƙaruwar matsin lamba daga ƙasashen Larabawa da na yankin na iya sa ƙungiyar Hamas ta zama saniyar ware.
A yankin Gabas ta Tsakiya, yanzu Hamas na da ƙawaye ƙalilan ne kawai da suka rage.
Bayan yaƙin kwana 12 tsakanin Isra'ila da Iran a watan Yulin da ya gabata, ikon Tehran na ci gaba da tallafa wa Hamas ya ragu matuƙa.
Ita ma ƙungiyar Hizbullah - ɗaya daga cikin fitattun masu ƙarfi a yankin da ke da alaka da Iran - ta samu rauni matuƙa sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai da kuma kashe shugabanninta a lokacin ƙazamin faɗa tsakanin ɓangarorin biyu sama da shekara guda.
Tuni ita ma ƙungiyar Hezbollah ke fuskantar matsin lamba daga gwamnatin Lebanon don miƙa makamanta.
Isra'ilawan da ake garkuwa da su
Hamas na ci gaba da riƙe Isra'ilawan da take garkuwa da su tun bayan harin 7 ga watan Oktoban 2023 da nufin yin sulhu da su.
Mayaƙan sun yi garkuwa da mutum 251 a lokacin harin da ba ta taɓa kai irinsa ba da ya yi sanadin mutuwar kusan mutum 1,200, a cewar hukumomin Isra'ila.
Fiye da Falasɗinawa 60,000 aka kashe a hare-haren da sojojin Isra'ila suka ƙaddamar a Zirin Gaza tun bayan harin na 7 ga watan Oktoba, a cewar alƙaluman hukumar lafyar Gaza.
Ƙiyasin Amurka ya nuna cewa har yanzu akwai Isra'ilawa 20 da ke raye cikin waɗanda ake garkuwa da su, yayin da wasu suka mutu, aka kuma mayar da wasu Isra'ila.
A farkon watan Agusta, Hamas ta fitar da wani bidiyo da wani ɗan Isra'ila da take garkuwa da shi, mai suna Eviatar David, cikin matuƙar ramewa da ƙanjamewa.
Kashe jagororin Hamas
Tun bayan harin 7 ga watan Oktoba, isra'ila ta kashe manyan jagororin Hamas, ciki har da shugaban siyasarta, Ismail Haniyeh, wanda aka kashe a wani hari da ƙungiyar ta ayyana da ''samame'' a gidansa da ke Tehran, babban birnin Iran a watan Yulin 2024.
Haka ma Isra'ila ta kashe Yahya Sinwar, wanda ake kyautata zaton shi ya kitsa harin ranar 7 ga watan Oktoba.
A ganin Farfesa Mekelberg, jagorin Hamas a Gaza na da ra'ayi na daban da shugbannin ƙungiyar da ke wajen Zirin Gaza.
Baya ga fifita rayuwa, shugabannin Hamas a Gaza na ƙoƙarin ''kiyaye matsayinsu na siyasa, wanda har yanzu ke samun goyon baya, domin cimma yarjejeniya''.
Amma domin ƙungiyar ta ci gaba da riƙe matsayinta, dole ne sauran shugabanninta su ɗauki matakai masu tsauri.
Bayan Netanyahu ya bayyana aniyarsa ta "karɓe cikakken ikon Gaza," zaɓin Hamas na ci gaba da raguwa a kowace rana.
Makomar Hamas
Abu mawuyaci a iya hasashen makomar Hamas.
Ƙungiyar ta ce za ta ajiye makamanta idan har aka kafa ƙasar Falasɗinawa, matakin da ake ganin ba mai yiwuwa ba ne idan har gwamnatin Isra'ila ta sauya matsayinta na yanzu.
Amma masu sharhi na ganin cewa ajiye makaman Hamas, in ma ta ajiye ɗin, ba ya nufin ƙungiyar ta mutu.
Yossi Mekelberg ya yi hasashen cewa, Hamas za ta iya samun damar sake gina kanta a nan gaba, ta kuma ci gaba da kasancewa babbar mai taka rawa a fagen siyasar Falasdinawa, a ciki da wajen yankunan Falasɗinawa.
To sai dai duk wannan ya danganta ne da matsayin Isra'ila kan ƙasar Falasɗinawa, da kuma farin jinin Hamas, duba da halin da al'ummar Gaza ke ciki a halin yanzu bayan harin da aka kai a ranar 7 ga watan Oktoba da kuma yaƙin sojin Isra'ila.