Mece ce lalurar galahanga?

Children with Down's syndrome gather in Graha Pandawa, Yogyakarta, Indonesia, to take part in the 2023 Down syndrome day celebration in March 2023

Asalin hoton, Getty Images

Ana bikin ranar masu galahanga ranar 21 na watan Maris ɗin kowace shekara domin wayar da kan jama'a game da lalurar.

Tun shekarar 2012 Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da ranar kuma ake bikinta.

Taken bikin na wannan shekara shi ne 'kawo karshen tsangwama ko wariya' da ake yi wa masu lalurar.

Akwai kuma zimmar da ake yi domn gano matsaloli da masu galahanga ke fuskanta, ta yaya za su kasance ko kuma me za su iya yi.

Mece ce galahanga?

Galahanga dai shi ne haifar yaro da wasu ƙarin kwayoyin halitta. Yanayin kwayoyin halittar yawanci na shafar koyon wani abu da zai yi da kuma yanayin jikinsa.

Lalurar ba cuta ba ce, illa rashin lafiya ko yanayin da wani zai iya kamuwa da shi. Ba a dai san me yake haddasa lalurar ba - saboda kawai haifar mutum ake yi da ita.

Yawanci mutanen da aka haifa da lalurar suna samun ƙarin kwayoyin halitta, saboda canjin maniyyi ko kwai kafin a haife su.

Ana samun waɗanda ake haifa da lalurar ko'ina a yankuna da ke faɗin duniya kuma galibi tana yin tasiri a kan salon koyo, halayen jiki da kuma lafiya, in ji Majalisar Ɗinkin Duniya.

Ana haifar jariri ɗaya cikin 800 da galahanga, a cewar masu shirya bikin Ranar Galahanga ta Duniya .

Lalurar tana da nau'o'i guda uku amma (trisomy 21) wanda shi ne nau'i na yau da kullum - inda ake samun waɗanda ake haifa da wasu kwayoyin halitta.

An saka wa lalurar sunan wani likita ne Dr John Langdon Down wanda shi ne mutum na farko da ya fara rarraba nau'o'inta.

Yaya alamomin galahanga suke?

15 year-old Ahad who has Down's syndrome poses for a photo at a private school for children with special needs ahead of the Down Syndrome Day in Barishal, Bangladesh, in March 2023

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Akwai wasu alamomi da ake iya gane masu lalurar galahanga

Alamomin lalurar sun kunshi:

  • Lallausar fuska, musamman kan hanci
  • Idanu waɗanda suka karkata sama
  • Gajeren wuya
  • Layi ɗaya a kan tafin hannu
  • Rashin tsayi kamar yara da manya

Shin ana iya magance lalurar?

 A number of children with Down's syndrome attend a 2023 Down Syndrome Day event at Graha Pandawa, Yogyakarta, in Indonesia in March 2023

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rayuwar masu lalurar ta Galahanga kan inganta ta hanyar kula da lafiyarsu

A halin yanzu dai babu maganin lalurar.

Ana iya ba da taimako bisa la'akari da buƙatun kowane mutum kama daga tunani, ƙarfi, da kuma gazawa.

Samun isassun hanyoyin kula da lafiya, shirye-shiryen bayar da taimako da kuma ilimi, da kuma binciken da ya dace, na da muhimmanci ga ci gaban mutum, in ji MDD.

MDD ta ce za a iya inganta rayuwar mutanen da ke fama da galahanga ta hanyar biya musu buƙatu na lafiya.

Wannan ya kunshi gwaje-gwaje na yau da kullum tare da sa ido na ƙwararrun kiwon lafiya don duba yanayin tunani da jiki da kuma samar da lokaci mai mahimmanci da bai wa masu lalurar warakar kashi da waraka ta magana da waraka ta aiki da kuma bayar da shawarwari ko kuma ilimi na musamman, in ji Majalisar Dinkin Duniya.

Wannan yana sauƙaƙe yanayin mu'amalarsu a cikin al'umma da kuma biyan buƙatun kansu.

Down's syndrome employee at a Starbucks coffee shop in Barcelona, Spain (2019 picture)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutane da dama masu ɗauke da lalurar galahanga ne ke zuwa makaranta da kuma wurin aiki

Mutane masu lalurar suna iya samun rayuwa mai inganci, zuwa makaranta da aiki, kuma wasu daga cikinsu na yin aure tare da yin rayuwa yadda suke so.

Wasu daga cikinsu na samun ayyuka masu tsoka, kamar Mar Galcerán a Sifaniya, wadda aka zaɓa zuwa majalisar dokokin yankin Valencia da ke gabashin ƙasar.

Ana tunanin cewa ita ce mutum ta farko ɗauke da lalurar da ta lashe zaɓe zuwa majalisar dokoki ta tarayya.

Mar Galcerán, after collecting her certificate as a parliamentarian of Les Corts de Valencia, in September 2023 in Valencia, Spain

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mar Galcerán

Akwai kuma Ellie Goldstein wadda ta kafa tarihin zama tauraruwa ta farko ɗauke da lalurar wadda ta fito a gaban jaridar Vogue - duk da cewa likitoci sun ce ba za ta iya tafiya ko magana ba saboda ciwon.

Kuma Heidi Crowter 'yar Birtaniya ce mai fafutukar kare hakkin masu nakasa ɗauke da galahanga wadda ke kalubalantar dokar da ke ba da damar zubar da tayin da ke da yanayi har zuwa haihuwa.

Ta kai kara zuwa Kotun Turai ta kare hakkin ɗan'adam. Ta ce dokokin da ake da su na nuna wariya ne.