Wasu 'yan Australiya sun zaci tashin duniya ne ya zo bayan da launin samaniya ya sauya a garinsu

Asalin hoton, NIKEA CHAMPION
A lokacin da launin sararin samaniya ya sauya zuwa ruwan hoda a wani gari a Australiya ranar Larabar da ta gabata, wata mazauniyar garin Tammy Szumowski, ta yi zaton tashin duniya ne ya zo.
"Na yi ƙoƙari na nutsu ban ruɗe ba, na gaya wa ƴaƴana cewar: "Ba wani abin damuwa ba ne," kamar yadda ta shaida wa BBC.
"Amma a cikin raina cewa nake, kam bala'i, me ke shirun faruwa ne haka?"
Daga baya an gano cewa wani haske ne yake tasowa daga wata gonar wiwi da ke wajen garin na Mildura a arewacin Victoria.
Amma baya ga Misis Tammy, akwai wasu mazauna garin da su ma suka shiga halin ɗimuwa na ganin wannan lamari - har suna tunanin ko wasu baƙin halittu ne suka kutso duniya? Ko kuma wani ƙaton dutse ne yake wucewa ta sararin samaniyar?
"Mama da baba suna magana a waya yana ce mata: 'Gara na yi sauri na shanye shayina saboda duniya za ta tashi."
"Sai mama ta ce: 'To me shan shayi zai ƙara maka idan har tashin duniyar ne ya zo.'
"Shi ma wani ɗan garin, Nikea Champion, ya ce da fari ya zaci wata ne ya ƙara girma kuma haskensa ya yi bau a lokacin da ya ga launin samaniyar ya sauya."
Ta cewa BBC "Babu irin tunanin da ban yi ba na batun tashin duniya."
End of Karin wasu labaran da za ku so ku karanta
Gonar sirri
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An halatta amfani da wiwi don yin magunguna a Australiya a 2016, amma an haramta amfani da ita kara zube.
Sai dai akwai ƴan wurare da ake harkokinta amma a sirrance suke yi saboda dalilai na tsaro.
Gonar a rufe take, don haka ana amfani da hasken wuta launin ja da ya zama kamar hasken rana don taimaka wa shukar wajen girma.
Yawanci, wani labule da ake rufe wa don a daina ganin hasken kan bayyana da asuba. Amma ba sa aiki a ranar Laraba, kamar yadda wani mai magana da yawun wani kamfani na Cann Group ya bayyana.
Kuma da yake a wannan daren akwai hadari, sai wannan hasken wutar ya yi wata kamar rumfa a sama da ake iya hangowa daga nisan kusan awa ɗaya da inda gonar take.
"Na yi dariya sosai... zai iya zama wani abu mai kwantar da rai, amma ba komai ba ne illa gonar wiwi da ke samar da wannan hasken," in ji Ms Champion.
Ita ma Ms Szumowski ta ce daga baya sun sha dariyar abin."
Duk da ruɗewar da suka yi da farko, amma kyawun da hasken ya samar ya ƙayatar. "Ina ga ya kamata a dinga hakan akai-akai."











