Mene ne ainihin launin rana?

Asalin hoton, Getty Images
Tun daga shekarun yarintarmu, mun saba da ɗaukar fensir launin ɗorawa domin zana rana. Ko kuma mukan ɗan ƙara kore idan muna son nuna ɓullowar rana ko kuma faɗuwarta.
Sai dai kuma tauraron da ke tsakiyar unguwar rana ba ruwan ɗorawa ba ne, ba ruwan goro ba ne, ba kuma ja ba ne.
Ya haɗa dukkan waɗannan launin da kuma wasu.
Rana kan watso haske mai launi daban-daban a lokaci guda.
Idan kuka kalli hasken rana ta cikin abin hange, za ku fahimci cewa ta rabu zuwa launukan ja da ruwan goro da kore da shuɗi da ruwan shanshambale.
Waɗannan ne launukan da ake gani kamar dai na cikin bakan-gizo.
Hasali ma, baka-gizo shi ne launin da idanunmu ke iya ganin rana yayin da take wucewa ta cikin ɗigon ruwa daga sama.

Asalin hoton, Getty Images
Duk da cewa launin rana mai launuka daban-daban na da daɗin kallo, sai dai ba dukansa ne daidai ba.
Saboda da zarar an haɗa dukkan launukan da rana ke fitarwa waje guda, launi ɗaya za mu gani kacal.
Idan muna son sanin wane launi ne wannan, muna iya ƙura wa sararin samaniya ido.
Waɗannan hadarin da muke gani a sama da ke bayyana mana hasken rana, ba ruwan ɗorawa ba ne ko shuɗi ko kuma wani launi.
Farare ne, saboda shi ne ainahin launin da rana ke fitarwa.
Me ya sa muke ganin ta a matsayin ruwan ɗorawa?
Kowane launi da ke cikin ƙwallon rana yana da mabambancin tsawo da tazara.
A wani loakci ja ne, wanda ke da mafi girman tsawo.
Sannan sai launin ya sauya a yanayin tsawon nasa, yana mai saukowa daga ja zuwa ruwan goro, zuwa ruwan ɗorawa, zuwa shuɗi, zuwa ruwan shanshambale wanda shi ne launi mafi ƙarancin tsawo a cikin ƙwallon rana.
A sararin samaniya inda haske ke yawo gabagaɗi, babu abin da zai kawo wa zirin haske cikas, sai kuma rana ta bayyana a matsayin wani farin ƙwallo wanda shi ne 'ainahin launin' tauraronmu na rana.
A gefe guda kuma, idan harshen rana ya gifta ta saman duniyarmu ta Earth, sinadaran da ke sararin samaniya kan lalata zirin hasken da ba su da tsawo.
Launukan masu tsawo da ke cikin ƙwallon rana ne ke isowa idanunmu mu gan su cikin sauƙi.

Asalin hoton, Getty Images
"Sararin samaniya kan kare wani ɓangare na haske mafi ƙarfi a ƙwallon rana," a cewar Angel Molina, wanda ke gudanar da wani shafi mai suna Astronomer's Diary.
"Saboda haka, kamar ƙwan lantarki mai zafi, akan ga rana a wannan duniyar ba tare da wasu launuka ba waɗanda sararijn samaniya ya kange. Takan sauya launi mai kama da ruwan ɗorawa."
Amma me ya sa take bayyana a ruwan ɗorawa, ba ja ba, ko kore waɗanda zirin haskensu suka fi sauran tsawo?
Gonzalo Tancredi da ke koyarwa a Jami'ar Jamhuriyar Uruguay, ya faɗa wa BBC cewa hasken rana kan bayyana a tsakiyar ƙwallon wanda ruwan ɗorawa ne, bayan an kare zirin haske marasa tsayi na kore da ruwan shanshambale.
Koriyar rana?
Babu mamaki kun taɓa jin cewa rana koriya ce.
Gonzalo Tancredi ya ce idon mutum ba zai iya tantance turirin rana ba, amma akwai abubuwan da za su iya rarrabe hakan kuma za su iya gane kore a matsayin mafi ƙarfi.
"Amma da zarar mun ware zirin haske marasa tsawo, kamar shuɗi daga zanen da muka yi na ƙwallon rana, ƙololuwarta zai sauya zuwa ruwan ɗorawa," in ji Gonzalo Tancredi.
"Waɗannan bayanai kan taimaka wajen tantance dalilin da ya sa muke ganin rana ruwan ɗorawa a duniyar Earth."

Asalin hoton, NASA/SDO/Goddard Space Flight Center
Da kuma jan rana idan za ta faɗi?
Idan rana za ta fito ko ta faɗi, wani ɓangarenta yana kusa da sararin samaniya, abin da ya sa wani harshenta ke giftawa tare da wasu sinadarai na sararin samaniyar.
Hakan kan haddasa lalacewar launukan shuɗi, wanda ke sa tsawon launukan ja da ruwan goro su mamaye ɓullowar rana.
Hasali ma hakan yana da suna. Ana kiran sa karairayawar Rayleigh - wanda ya samo asali daga sunan Lord Rayleigh, wani masanin Physics wato ilimin sifa.
Yayin da rana ke tafiya a sararin samaniya, ɓangarenta da ke kusa da duniya na sauyawa a kowane lokaci, abin da ke ba ta launuka daban-daban a tsawon rana, ciki har da ɓurɓushin ja na faɗuwar rana.

Asalin hoton, Getty Images
Muna fatan wannan maƙalar ta ba ku sabon ilimi mai ƙayatarwa game da tauraronmu na rana, amma kar ku manta cewa kar ku sake ku kalli rana da idanunku kai-tsaye - ko da kuwa da tabarau ɗin hangen rana ne - saboda zai iya haifar muku da matsala ko kuma ya haifar da rashin gani.











