Abin da yarjejeniyar Amurka da Japan ke nufi ga Asiya da duniya

Shugaban Amurka Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Suranjana Tewari
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Asia Business Correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 4

Shugaban Amurka Donald Trump ya kira yarjejeniyar da ya cimma da Japan a matsayin "ta cinikayya mafi girma a tarihi."

Ya kan iya zama ya yi wuri a yi irin wannan ikirari, amma tabbas ita ce yarjejeniya mafi girma tun da Trump ya sanar da karin haraji a watan Afrilu wanda ya haifar da rudani a kasuwar duniya.

Bayan watanni ana tattaunawa, Firaministan Shigeru Ishiba ya ce yana tsammanin yarjejeniyar za ta taimaki tattalin arzikin duniya.

Ikirari ne mai girma. BBC ta duba ko hakan ne, kuma ta yaya?

Japan ta zama tamkar kamfani

Japan na da tattalin arziki na hudu mafi girma a duniya, wato tana ba da gudunamawa mai karfi a kasuwancin duniya.

Tokyo na shigar da makamashi da abinci mai yawa daga kasashen waje kuma ta dogara da fitar da kayayyyaki kamar na'urori, kayan aiki da kuma motoci.

Amurka ce kasar da ta tafi kai wa kaya.

Wasu masana sun yi gargadin cewa harajin na Trump zai iya kwashe abu mai nauyi daga tattalin arzikin Japan, kuma ya haifar mata da koma baya.

Da haraji mara yawa kuma, masu kai kaya waje za su iya yin kasuwanci da Amurka cikin sauki idan aka hada da barazanar da Trump ya yi na kara harajin.

Kuma yarjejeniyar ta haifar da daidaito, wanda zai bai wa yan kasuwa damar yin tsari.

Sanarwar ta kuma karfafa kudin yen na Japan a kan dalar Amurka, kuma zai bai wa masu masana'antu karin karfin siyan kayan da suke bukata don sarrafawa a kamfanoninsu.

Yarjejeniyar ta Amurka na da kyau ga kamfanonin mota na Japan kamar Toyota, Honda da Nissan. A baya, kamfanonin Amurka na biyan harajin kaso 27.6% don shigo da motoci daga Japan.

Yanzu an rage harajin zuwa kaso 15%, kuma hakan zai tsadar motocin na Japan idan aka hada da na China.

Masu hada mota a Amurka sun nuna rashin jin dadi game da hakan.

Suna fargabar biyan harajin kaso 25% kan kayan aikin da suka shigowa da su daga kamfanoninsu da ke Canada da Mexico, idan aka hada kaso 15% daga Japan.

Ayyukan yi da kuma ƙarin yarjeniyoyi

A matsayin ramuwa ga ragin harajin, Japan ta yi tayin zuba hannun jarin dala biliyan 550 a Amurka don bai wa kamfanonin Japan "damar samar da cinikayya mai karfi a bangarori kamar na magunguna," a cewar Ishiba.

Japan babbar mai zuba hannun jari ce a Amurka, amma wannan kudin za su iya samar da ayyuka, tare da samar da abubuwa masun inganci.

Karkasin yarjejeniyar, Trump ya ce Japan za ta kara adadin kayan noma da take siya kamar shinkafar Amurka - ko da hakan zai bata wa manoman da ke cikin kasar.

Harajin na kaso 15% kuma ya zama abin la'akari ga kasashe kamar Koriya ta Kudu da Taiwan wadanda ke tattaunawar cinikayya da Amurka.

Buhunhunan shinkafa yar Amurka a wata kasuwa da ke Brooklyn, New York

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Japan zata siya shinkafa daga Amurka, a cewar Donald Trump

Ministan masana'antu na Koriya ta Kudu ya ce zai yi duba na tsanaki kan abubuwan da Japan ta amince da su da Amurka yayin da ya tafi Washington don tattaunawa mai muhimmanci.

Japan da Koriya ta Kudu na gogayya a masana'antu kamar na karfe da motoci.

Yarjejeniyar ta Amurka da Japan za kuma ta kara matsi kan sauran kasashe musamman na Asiya da ke fitar da kaya masu yawa su cimma yarjejeniya kafin 1 ga watan Agusta.

Sai dai wasu kasashen Asiya za su wahala.

Kasashe marasa karfin tattalin arziki sosai kamar Cambodia, Laos da Sri Lanka na sarrafa kaya su fitar da su kuma ba su da abubuwa da yawa da za su bai wa Washington na cinikayya ko hannun jari.

Ko Amurka ta samu abin da take nema?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Akwai rahotannin cewa Amurka ta nemi Japan ta kara abin da take kashewa kan bangarenta na tsaro.

Amma wakilin Tokyo na musamman ya ce yarjejeniyar ba ta kunshi kashe kudi kan tsaro ba.

Ryosei Akazawa ya kara da cewa haraji kan karafa da aluminium zai tsaya kan kaso 50%.

Hakan zai iya zama nasara ga Japan, tun da ta fi fitar da motoci zuwa Amurka sama da karafa.

Akwai kuma nauyi kan Amurka ta cimma wadannan yarjeniyoyi kafin lokacin da ta saka na watan Agusta.

Tare da wadannan tattaunawa da Amurka, ƙasashe za su iya fara neman abokan cinikayya a wasu wuraren.

A ranar Washington da Tokyo suka sanar da cimma tasu yarjejeniyar, Japan da Turai sun yi alkwarin "aiki tare domin yakar keta da kuma dabarun kasuwanci da ba su dace ba", a cewar Shugabar Tarayyar Tyrai Ursula von der Leyen.

Har yanzu Tarayyar Turai da Amurka ba su cimma yarjejeniyar cinikayya ba.

"Mun yar da da gogayyar cinikayya a duniya da za ta amfanar da kowa," a cewar Ms von dey Leyen.

On the same day as Washington and Toyko announced their agreement, Japan and Europe pledged to "work more closely together to counter economic coercion and to address unfair trade practices," according European Commission President Ursula von der Leyen.

The European Union is yet to agree a trade deal with the US.

"We believe in global competitiveness and it should benefit everyone," said Ms von der Leyen.