Sakamakon zaɓen Afirka ta Kudu

Asalin hoton, AFP
Sakamakon zaben Afirka ta Kudu bai wa jam’iyyar ANC mai mulkin kasar dadi ba.
Jam’iyyar wadda Nelson Mandela ya taba jagoranta ta lashe kujeru 159 ne kacal a cikin 400.
Hakan ya yi kasa sosai idan aka kwatanta da kujeru 230 da jam’iyyar ke rike da su a tsohuwar majalisar dokokin kasar.
Wannan sakamakon zabe shi ne mafi muni ga jam’iyyar ANC tun shekaru 30 bayan kawar da mulkin wariyar launin fata - duk kuwa da cewa har yanzu jam’iyyar ita ce ta fi kowace yawan kujeru a majalisar.
Zaɓen ya kafa tarihi, inda jam'iyyu 70 da kuma ƴan takara masu zaman kansu 11 suka fafata domin neman kujerar majalisar dokoki da kuma ta lardi.
Masu sharhi sun nuna cewa mutane da dama sun dawo rakiyar jam'iyyar ANC.
Sakamakon da aka sanar a ranar Lahadi na nuna yadda farin jinin jam’iyyar ke dusashewa, kuma hakan na nufin wajibi ne a yanzu jam’iyyar ta shiga kawance domin kafa gwamnati mai zuwa.

Asalin hoton, Getty Images








