Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Cutar al'aurar mata da ta daɗe tana rikitar da likitoci
- Marubuci, Maria Zaccaro
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 4
"Na yi tunanin dukkan mata na fuskantar ƙaiƙayi," in ji Clare Baumhauer.
Wata mata mai shekaru 52 daga Kent, Burtaniya ta ce tana ƴar kimanin shekara biyar lokacin da ta fara jin ƙaiƙayi a bakin gabanta.
"Yana yi min ƙaiƙayi a kowane lokaci, yana zafi, ina samun kumburi da tsattsagewa mai fitar da jini, sannan kuma idan na je tsuguno wurin na matuƙar zafi," kamar yadda ta ƙara bayani cewa zama ko tafiya na yi mata wuya.
Ta shafe shekaru da dama tana ganin likitoci waɗanda suka shaida mata cewa tana da ƙwayar cutar da ta kumbura mata mafitsara amma kuma dukkannin magungunan da aka ba ta babu wanda ya yi aiki a ciki.
Masu aikin ungozoma a asibiti lokacin da ta haifi ƴaƴanta guda biyu sun duba ta sannan ta je an yi mata gwajin kasar mahaifa har karo takwas amma duk da haka ba a ga wata matsala ba.
Sai a 2016 ne lokacin tana ƴar shekara 43 ta je wurin likita domin a ɗinke mata wata ƴar yankewa da fatarta ta yi inda a yankin wani ɓangare na fatar domin yin gwaji, abin da ya sa aka gano cewa tana ɗauke da larurar ɗaɗewar bakin gaba da ake kira da "vulval lichen sclerosus." a turance.
Wata larurar fata da masana suka ce ba a cika magana a kanta ba sannan kuma ana kuskuren gano ta a faɗin duniya.
Cutar dai kan janyo wani yankin na fatar gaban mace ya ɗaɗe tare da zogi da kuma tsagewa da wasu sauye-sauye dai da ka iya sanya gaban mace ya ƙanƙance wanda ka iya janyo mata rashin samun nutuswa a lokacin fitsari ko bahaya ko kuma yayin saduwa.
Wannan larura ka iya shafar mata ƙanana ko manya duk da dai ya fi shafar mata masu shekaru 50 wanda ka iya jefa su a hatsarn kamuwa da kansar bakin al'aura, duk da dai likitoci na cewa hatsarin kamuwa da kansar ba shi da yawa.
Clare ta fahimci cewa laɓɓan gabanta na tsukewa sannan ɗan tsakan da ke gaban nata na haɗwa da fatar da ke kewaye da shikuma abin da hakan ke nufi shi ne ta samu cutar kansa a bakin al'aurarta.
"Abin na da takaici saboda irin yadda aka kasa gano cutar tun da wuri.," in ji Clare.
'Na kunyata'
Sai bayan cutar ta ƙaiƙayin gaba da kuma gano cutar kansar ta shaida wa maigidanta dangane da abin da ta daɗe tana fuskanta a rayuwarta.
"Ban faɗa ba, saboda abin da kunya cewa gabana na ɗaɗewa sannan yana ƙaiƙayi kenan sai na samu dalilan ƙin saduwa saboda zafi. Ban san me ce ce matsalata ba saboda haka ban san me zan ce ba," in ji Claire.
"Ya san cewa na je ganin likita kuma aka ba ni maganin ɗaɗewa saboda haka ya yi tsammanin na samu ɗaɗewar mai girma ne."
Claire wadda take tafiyar da wata ƙungiyar da ke tallafa wa mata a duniya, ta ce mata masu ɗauke da wannan larura da ba za su san alamomin cutar ba.
"Abu ne mai wuya, akwai al'adar rashin son tattauna batun", in ji ta. "Ba ma magana a fili dangane da jima'i ko gaban mace. Babu cikakken wayar da kai dangane da hakan."
Debbie Roepe, darekta a ƙungiyar da ke nazarin cutar bakin al'aurar mata, ta ce cutar ba a santa ba sosai a duniya.
Tana tunanin cewa an samu cigaba dangane da wayar da kai a ƴan shekarun nan to sai ta ce ana buƙatar ƙara yin hoɓɓasa.
'Rashin bacci'
Kamar Clare, ita ma Meenakshi Choksi ƴan shekara 85 ƴar ƙasar India a jihar Gujarat ta ji rashin daɗi lokacin da ta fara fuskantar ƙaiƙayi a kewayen gabanta a 2000. Daga nan ne kuma ta fara samun tsatstsagewa tare da fitar da jini.
"Na ji kunya wajen tattauna batun. Ba na iya bacci," in ji ta.
An kwashe shekaru 24 tare da zuwa wurin likitoci 13 kafin a gano cutar. Daga ƙarshe, sai a bara ne wani likitan fata ya faɗa mata cewa tana da cutar daɗewar gaba, inda ya ba ta maganin da ya rage mata raɗaɗi cikin ƴan kwanaki.
"Na warke. Zan yi sabuwar rayuwa," in ji ta.
Likitoci sun ce cutar ba ta warkewa. Sai dai amfani da wani mai domin rage raɗaɗi.
Ba a san dalilin samuwar wannan cuta ba, inda masana suka yi imanin cewa cutar ka iya samuwa sakamakon yaƙar da garkuwar jiki ke yi ga fata maimakon ga ƙwayoyin cuta.
Ba wata ƙwayar cuta ce ka haddasa cutar ba ko kuma ƙazanta sannan ba a ɗaukar ta d ake nufin wnai ba zai iya ɗaukar ta ba ta hanyar saduwa ko kuma kusantar juna.
Yadda aka gano cutar
Sai dai kuma ba duka matan ne ke ganin alamun cutar a jikinsu ba.
Lucia wadda ba sunanta ba kenan ta ce ta ji ƙaiƙayi a kewayen gabanta kuma an gano tana da cutar ɗaɗewar gaba "ba tare da shiri ba."
Matar maishekara 50 ƴar birnin Rio de Janeiro a Brazil ta ce tana zuwa gwaji a kowace shekara wurin likitan matan da ta kwashe shekaru 25 tana gani ba tare da gano matsalar ba.
An gano cutar ne lokacin da ta je ganin wata ƙawarta wadda likitar fata ce domin a duba ta kan wata matsalar ta daban a matsematsinta, inda aka sanar da ita cewa kewayen gabanta yana da matsala.
"Ƙananan leɓɓan da ke gaban nata sun haɗe da manyan leɓɓan. Kewayen gaban kamar ya haɗe da ɗan tsaka," ta yi ƙarin haske.
Wani bincike ya gano cewa kaso 38 cikin ma'aikatan lafiya 122 da suka amsa tambayoyi yayin binciken sun ce ba a taɓa koya musu cutar ɗaɗewar gaba ba a lokutan karatunsu.