Yadda damuwa ke hargitsa rayuwar masu haihuwar fari

Wata mata riƙe da jariri

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Cutar matsananciyar damuwa da ke damun matan da suka haihu na iya janyo abubuwa masu tsanani kamar rashin iya bacci bakiɗaya da kuma kasa gane abin da ke zahiri da na mafarki
    • Marubuci, Angela Henshall
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 7

Gargaɗi: wannan labarin na ɗauke da abubuwa da za su iya tayar da hankalin mai karatu.

Ellie ta ce da farko ta ji farin ciki mara misaltuwa.

Ta haihu a gida, ba tare da maganin kashe zafi ba, ta kuma yi farinciki sosai da zama uwa.

Kuma duk da ba ta samu isashen bacci cikin kwanaki uku ba, ta na ganin cewa ba ta bukatar yin bacci.

''Yadda zan iya bayyana abin da naji shi ne kamar na tashi daga wani mugun mafarki, ba na iya bam-bance mene ne mafarki kuma menene zahiri,'' in ji ta. ''Kuma wannan yanayin da nake ji ya ƙi wucewa.''

''Daga bisani, na yi tunanin na kashe ɗana a kan gado. Na tuna sai da maigida na ya zo, sai na fara mamaki, 'wannan abin dagaske ne?''

Ellie na fama da matsananciyar damuwa da ke damun mata bayan haihuwa (PPP), wani yanayi da kan sanya damuwa da matsalar ƙwaƙwalwa ga iyayen da suka haihu a karon farko.

Wata uwa da ke cikin tunani da damuwa a gaban likita tare da jaririnta kan cinyarta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Cutar na da tsanani da ke buƙatar ƙwanciya asibiti da kulawan ƙwararru

Mece ce cutar matsananciyar damuwa da ke samun mata bayan haihuwa?

Ɗaya daga cikin alamun farko da ke nuna cutar na bayyana ne a lokacin da mahaifiyar ta kasa gane kanta, ko kuma ta kasa gane menene zahiri.

Iyaye da dama kan kasa yin bacci sosai bayan sun haihu. Amma mata masu cutar PPP ba sa iya bacci bakiɗaya.

Hukumar lafiya ta Birtaniya ta ce alamun cutar PPP sun haɗa da:

  • Sauyin yanayi cikin ƙanƙanin lokaci
  • Gane-gane
  • Tsarguwa
  • Jin muryoyi
  • Rashin natsuwa
  • Ruɗewa

Cutar PPP cuta ce mai bukatar kulawar gaggawa, kuma a lokuta da dama, ana bukatar kwanciya a asibiti domin samun kulawa ta musamman.

Sai da kwararru na ganin cewa yanada muhimmanci a yi la'akari da cewa duk tsananin da ciwon zai yi, mata da dama na samun sauƙi cikin ƴan watanni idan suka samu kulawar da ta dace.

Wata mata tana rarrashin wani jariri da ke kuka.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zuwa yanzu ƙwararru basu gano musabbabin cutar matsanaciyar damuwa da iyaye kan shiga bayan haihuwa ba

Me ke kawo Matsananciyar damuwa da ke samun mata bayan haihuwa?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Duk da shekarun da aka shafe ana bincike, har yanzu ba mu san takamai mai abin da ke janyo cutar ba.

Likitoci na ganin cewa akwai yiwuwar sauyi a sinadaran jiki lokacin haihuwa na da alaƙa da cutar. Sauyin kan kai ga tsananin ruɗewa da firgita.

Sai dai babu hanyoyin da za a dogara da su domin gane wanda zai iya kamuwa da cutar, kamar gwajin jini.

Aƙalla rabin sabbin iyaye mata da aka gane suna da cutar ba su taba fama da damuwar ƙwaƙwalwa ba, don haka suna fama da gane gane masu firgitarwa da jin muryoyi da basu saba da su ba.

Ga Ellie, alamun cutar ya soma da wuri.

''A yanzu ina ta tunani ko ya fara ne tun lokacin da na soma naƙuda da daddare a gida,'' in ji ta. '' Na kasa fahimtar dalilin, amma ban tashi mijina ba sai karfe shida na safiya.''

Cutar tana shafar mace 1-2 cikin mata 1000 bayan haihuwa. Ba ta da yawa kamar damuwa bayan haihuwa, wadda ke shafar aƙalla mace ɗaya cikin goma na iyaye sabbin haihuwa.

Ƙwararru na ganin cewa akwai matan da ke fama da cutar a yanzu fiye da yadda akayi hasashe a baya.

A shekarun baya, ita kanta cutar damuwa bayan haihuwa a kan ki mayar da hankali kanta.

Sai dai likitoci na gargaɗin cewa ƙin bayar da muhimmanci ga lafiyar ƙwaƙwalwar iyaye na ƙara wa mata wahalar zuwa asibiti domin samun kulawar da ta dace.

Wani sabon bincike da ƙungiyar Charity Action on Postnatal Psychosis (APP) da ke Birtaniya ta yi na ganin cewa har yanzu wasu matan ba a iya gane cutar ce ke damunsu, wasu lokutan daga likitoci ko kuma Ungozoma, waɗanda kan basu maganin bacci kawai.

Ƙungiyoyi kamar su APP, da ƙungiyar Centre of Perinatal Excellence da ke Australia, da Perinatal Anxiety and Depression Aotearoa da ke New Zealand na aiki tare wajen wayar da kai kan cutar matsanaciyar damuwa da ke damun mata bayan haihuwa a tsakanin alumma da ma'aikatan lafiya.

A yanzu haka Ellie na aiki tare da wata ƙungiya da ke taimakawa mata da ke fama da cutar.

Tana ganin abubuwa da dama ne suka janyo cutar, kamar rashin bacci, da kuma matsin lamba domin zama uwa ta gari.

Amma kuma a yanzu ta gane cewa nata cutar ta yi tsanani saboda ta yi fama da matsalar fushi da hucewa cikin suri samfuri na 1.

A cewar binciken Jami'ar Cardiff da ke Birtaniya wanda aka wallafa a mujallar The Lancet, aƙalla kashi 25 na matan da ke fama da wannan cutar kan yi fama da ita a wai lokaci da kan buƙaci zuwa asibiti bayan haihuwa ta farko.

A Birtaniya da Australia da New Zealand, akan shawarci mata da ke wannan rukunin su cigaba da shan magungunarsu.

A shekarun baya, likitoci na bayar da shawarar daina sha, wanda kuma har yanzu a wasu ƙasashen ana bayar da wannan shawara.

Matan da ke cikin wannan yanayi na buƙatar ganin liktocin ƙwaƙwalwa da ke kula da mata tun ranar da suka ɗauki ciki zuwa shekara 1 ko biyu bayan sun haihu, a cewar ƙungiyar APP da ma wasu ƙungiyoyin.

Wata Uwa a zaune a kasa da ɗanta a wani ɗakin kula da mata da ƴaƴa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gimbiyar Wales, Catherine a lokacin da ta kai ziyara wajen wata uwa da ɗanta a sashen kula da su da ke asibitin Bethlem Royal Hospital da ke Landan

Mene ne zai iya taimakawa?

Akwai fargabar cewa idan ba'a nemi magani ba, iyayen da ke fama da Cutar za su iya ƙoƙarin cutar da kansu, a cewar bincike da dama.

Bincike da aka yi a Birtaniya da Australia da New Zealand na ganin cewa kulawar da tafi da za a iya bai wa masu cutar ita ce ajiye Iyaye mata da ƴaƴansu a sashen kula da lafiyar ƙwaƙwalwa da aka ware wa iyaye da yara, ƙarƙashin sa ido.

Wannan mataki na kai wa ga nasara sosai, sai dai samun ire-iren wuraren na da wahala saboda akwai ƙarancinsu da kuma ƙaranacin gadajen kwantar da su.

'' A gare ni, na ji kamar an kashe wani ɓangare na ƙwaƙwalwata kuma alamu sun nuna min haka,'' in ji Ellie.

Akwai wasu abubuwa da ta mance, sai dai ta tuna lokacin da ta tsaya kan matattakala a gida tana jin mijinta yana kiran ma'aikatan lafiya na unguwarsu.

'' Na ji tsoro sosai'' a cewar ta. '' a lokacin ina buƙatar taimako, kuma saboda sun ji ni ina ihu, shugabar Ungozoma na yankin ta yi iya ƙoƙarinta na shigar dani cikin fannin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa na iyaye da yara. Abu mafi muhimmanci shi ne ana samun sauƙi, shi ne abin da aka mayar da hankali kai.''

Ariane Beeston, mai magana da yawun ƙungiya mai zaman kanta ta Perinatal Centre of Excellence, a baya ta yi fama da Cutar. Ta jaddada muhimmancin samun isassun gadaje domin kula da masu cutar.

A baya Beeston na aiki ne a cibiyar kare ƙanana yara. A cewar ta cutar ta zo mata ne ba zato ba tsammani.

A cikin littafinta mai suna' Because i am not Myself'' ta bayyana yadda take gane ganen dabbobi masu aman wuta kusa da ɗanta da kuma jirage maras matuƙa da ke shawagi a sama.

Bayan an kwantar da ita a asibitin kula da ƙwaƙwalwa na iyaye mata da yara, ta sami kulawar da take buƙata domin samun isashen bacci, ta shaƙu da sabon jaririnta, ta kuma shiga ajujuwan koyar da yadda ake zama iyaye kuma ta sami sauƙi.

Ɗaya daga cikin lokuta mafi wahala ga matan da ke barin irin wannan wuri shi ne yanke hukunci tare da masu kula da su wani lokacin ne ya dace su koma gida.

Zaɓin shayarwa ko kuma ƙin shayarwa shi ma yana da muhimanci ga matan da ke fama da cutar.

Samun irin wannan kulawar na ƙaranci a wasu ƙasashen. Ana samun bam-bance bam-bance na al'adu a faɗin duniya game da mata da suka haihu a karon farko.

Wasu al'adun kan tilastawa iyaye mata da suka haihu a karon farko kaɗaicewa na kwanaki 40.

A wasu wurare a Indiya kuwa, ana alaƙanta cutar matsanaciyar damuwa da kan damun mata bayan haihuwa da addini, abin da ake kira devva hididide, wato fatalwa ta shige su.

A wasu al'adun kuma ana kallon rashin lafiyar ƙwaƙwalwa bayan haihuwa a matsayin wata kasawa daga matan ko kuma gazawa wajen zama uwa.

A Hong Kong, masu bincike sun gano iyaye mata na fuskantar matsi domin cike matsayin da uwa ke da ita a al'adance. kuma duk wata gazawa wajen yin hakan ana kallonsa a matsayin babban abin kunya.

Wata mata mai ciki da ta ɗora hannunta kan cikin.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu bincike na ganin cewa sauyi a ƙwayoyin halittun da ke da alaƙa da haihuwa na iya janyo cutar a wasu mata

Me ke faruwa idan mace na son ƙara haihuwa?

A cewar binciken Jami'oin Manchester da na Cardiff da ke Birtaniya, abin takaici shi ne mace ɗaya cikin biyu da suka yi fama da cutar za su ƙara fama da shi a haihuwa na gaba.

Ga iyaye da ke da ƴaƴa da dama, bincike ya nuna cewa yin shiri sosai gabanin haihuwan na iya tabbatar da cewa akwai masu bayar da kula da goyon baya isassu, ko abokai ko ƴan uwa da za su taimaka, da bai wa bacci muhimmanci, da kuma ƙoƙarin sanya kanka a gaba domin zama Uwa ta gari,'' A cewar Ellie.