Abin da ke haifar da cutar farfaɗiya da yadda ake magance ta

Asalin hoton, Getty Images
Cutar farfadiya, kamar yadda masana cututtukan da suka shafi kwakwalwa suka bayyana, cuta ce da take shafar kwakwalwar mutum ta yadda take wargaza wani saiti mai kama da wayoyin lantarki da ke cikin kwakwalwa.
Hakan kan sa wanda yake fama da cutar yin wasu dabi'u na daban ko fita daga hayyacinsa.
Shi ya sa da zarar cutar ta buge wanda ya kamu da ita, takan jefa shi cikin barazanar fadawa cikin hadurra idan babu wani a kusa.
Kuma bugewar kan faru ne babu zato babu tsammani.
Amma masanan sun ce ba a yanke hukuncin cewa mutum ya kamu da cutar ta farfadiya har sai an fahimci marar lafiyar ya fara jijjiga fiye da kima, wanda alama ce ta farko da kan bayyana a jikin mai fama da cutar.
Wannan makala ta yi duba kan wanna cuta da yadda ake kamuwa da ita da camfe-camfen da ake yi a kanta da kuma ko ana warkewa daga ita.
A hira da BBC, Dakta Woru Baba Goni na Asibitin Koyarwa na Jami'ar jihar Yobe a Arewa Maso Gabashin Najeriya, ya yi karin bayanin cewa farfadiyar cuta ce da wanda ya kamu da ita yake samu daga wani bangare na kwakwalwarsa.
A cewarsa: "Ita kwakwalwa tana da wasu jijiyoyi masu kama da wayoyin lantarki da kan aike da sakonni daban-daban, da a turance ake kiransu 'spikes', idan ya zamanto ba sa aiki sosai shi ne yakan kawo cutar farfadiya".
Dakta Isa Bukar, wani kwararren likita ne a fannin kula da lafiyar masu tabin hankali a yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya, kuma ya shaida wa BBC cewa farfadiya na daya daga manyan cutukan da suka shafi kwakwalwa da ake yawan gani a tsakanin ko wane irin rukunai ko jinsin mutane a fadin duniya.
"Duk abin da ya shafi kwakwalwa ya jawo mata wani rauni har ta samu wani tabo, to wannan tabon ka iya zama tushen samun cutar farfadiya," in ji Dakta Bukar.
Alamomin cutar farfadiya
Akwai bayanai da suka fito daga binciken masana daban-daban a fadin duniya game da alamomin cutar ta farfadiya da suka hada da:
- Jijjiga musamman daga hannaye da kafafuwa.
- Kafewar idanuwa zuwa kallon sama.
-Gushewar hankali ko rikicewa na dan kankanen lokaci.
-Alamomin razana da firgici.
- Jin jiri da hajijiya.
- Ganin haske kamar walkiya yayin farfadiya
- Tashin zuciya da yin amai, da fitsari da ba haya lokacin farfadiya.
Dakta Goni ya shaida wa BBC cewa: "Daga nan mutum yakan yanke jiki ya fadi ya rika cizon harshe, yana jijjiga, idanu su kakkafe, a wasu lokuta yakan yi fitsari da kashi a jiki ba tare da ya sani ba".
Mene ne yake kawo cutar farfadiya?

Likitoci da sauran masana kan cututtukan da suka shafi kwakwalwa a duniya da dama sun yi ittifakin cewa abubuwan da suke haifar da cutar farfadiya na da sigogi daban-daban, kuma sun danganta ga yanayin yadda mutum ya samu kansa a fannin tafiyar da rayuwa.
Dakta Goni ya yi wa BBC karin bayani cewa cutar farfadiyar na iya faruwa tun daga lokacin haihuwa idan ta zo da gardama ya zamanto jaririn ya fito bai yi kukan farko ba, ko kuma wasu cututtuka kamar sankarau da shi ma kan shafi kwakwalwa.
Ya kuma kara bayyana cewa: "Yakan kuma faru idan yaro ya samu rauni, misali ko ya fado daga sama ko kan gado kansa ya bugu, yakan iya samun cutar farfadiya," sannan kuma ita kan ta cutar sankarau idan ba a samu an yi magani da wuri ba takan shafi kwakwalwa, wanda kan haifar da cutar ta farfadiya."
Wasu masanan sun bayyana cewa cutar zazzabin cizon sauro ma idan ta tsananta takan taba kwakwalwa.
"A wasu lokutan ma, mutum yakan kamu da cutar farfadiya sanadiyyar hadarin mota idan kai ya bugu, ya fita daga hayyacinsa har na tsawon kwanaki," in ji Dr Goni.
Haka shi ma Dakta Bukar ya yi karin haske cewa jarirai kan fuskanci barazanar kamuwa da cutar fardadiya a lokacin haihuwarsu a bisa dalilai da dama.
Ya kara da cewa: "A wajen haihuwa idan jarirai suka sha wahala, ko wata cuta ta shige su, da taruwar jini da ruwa a cikin kwakwalwa ko kuma a ji wa yaro ciwo a kai yayin da ake kokarin tiyatar fito da shi daga ciki, duk kan iya haddasa wannan cuta."
Dr Goni ya bayyana cewa akan samu hakan ne lokacin haihuwa ko kuma lokacin yaro na ciki.
"Akwai wata matsala da kan shafi ita kwakwalwar, misali akwai wasu cututtuka da a turance ake kira 'torch complex' da kan shafi kwakwalwar yaro kafin ko kuma lokacin haihuwarsa," in ji shi.
Har ila yau, masana sun tabbatar da cewa cutar barin jiki ita ce kan gaba wajen jawo cutar farfadiya ga mutane 'yan sama da shekara 35.
"Matsalolin cikin kwakwalwa kamar su kansar kwakwalwa da cutar shanyerwar barin jiki da aka sani a turance da 'stroke', kan iya haifar da cutar farfadiya,'' in ji Dakta Goni.
Yayin da wasu masanan ke cewa an samun cutar farfadiya ta hanyar gado, wasu kuma suna ganin batun ba haka yake ba.

Camfe-camfe

Asalin hoton, Getty Images
Akwai bayanai da suka shafi al'adar camfe-camfe da dama game da cutar farfadiya musamman a kasashe masu tasowa, inda galibi mutane ke danganta farfadiya da bugun aljanu ko kuma iskokai.
Hakan ya sa masu fama da ita ko danginsu kan fi dogara ne da maganin gargajiya a maimakon zuwa asibiti.
Sai dai masana a fannin cutukan da suka shafi kwakwalwa sun bayyana cewa cutar ta farfadiya ba ta da alaka da bugun iska, kuma rashin zuwa asibiti a kan kari na daga cikin abubuwan da ke haddasa ta'azzarar cutar.
Za ka ga da zarar cutar ta buge wanda ke da ita akan rika yin nesa da shi don gudun daukar cutar, a wasu lokuta ma a kan zuba toka ko kuma kona daidai wurin da mai farfadiyar ya tashi bayan ta sake shi duk dai don kada a dauki cutar.
Masana sun ce irin haka ne ya sa masu cutar farfadiyar ba sa samun taimakion da ya kamata bayan ta buge su.
A lokuta da dama za ka ga idan cutar farfadiyar ta buge wanda ya kamu da ita mutane kan kewaye shi, ko kuma a rika saka masa wani karfe a baki don kada ya ciji harshensa, ko a rika dura masa wasu jike-jike.
Amma kuma masana sun bayyana cewa akwai rashin fahimta sosai dangane da wannan matsala wanda hakan ya sa ake ta yin wadannan camfe-camfen.
Dakta Isa Bukar na daga cikin masanan da suka shaida wa BBC cewa wannan al'ada ta camfe-camfe da ake yi dangane da cutar farfadiya ba ta da amfani.
"Ba gaskiya ba ne a ce duk wanda ya tsallaka wurin da mai farfadiya ya tashi zai dauki cutar, hasali ma ba gaskiya ba ne a ce wai bugun aljanu ne, don haka ba zai sa don ka tsallaka inda ya tashi ka kamu da cutar ba, ba gaskiya bane," a cewarsa.
Haka shi ma Dakta Goni ya bayyana cewa ba daidai ba ne mutane su rika danganta cutar farfadiya da aljanu, yana mai cewa larura ce da ke samun kwakwalwa.
Ya kara da cewa: "Kamar yadda na fada a baya, wayoyi ne da suke hade da kwakwalwa masu kamar na lantarki da idan suka samu matsala a nan ne akan samu wannan lalura ta farfadiya."
Ko shakka babu yanayin yadda ciwon kan buge masu fama da cutar farfadiyar ne ya sa wasu ke danganta wa da bugun iska domin za ka ga a lokaci guda marar lafiyar ya yanke jiki ya fadi yana ta karkarwa yana zubar da yawu idanusa sun kakkafe.

Me ya kamata a yi wa wanda farfadiya ta buge?
Idan ciwon farfadiya ya buge wanda kuke tare da shi abin da ya kamata ka yi shi ne ka cire duk abubuwan da za su iya cutar da shi - kamar kujera ko teburi ko wuta - daga gabansa, sannan kada a danne shi; a bar shi ya yi jijjga ya gama, a cewar masana.
Kada a kawo wani cokali ko man ja a danna a bakinsa.
Mutane sukan kewaye wanda farfadiya ta buge su hana shi shan isa. Hakan ba daidai ba ne, in ji masana.
Wanda farfadiya ta buge na bukatar sarari domin ya samu iska don a lokacin yana bukatarta sosai.
Masana irin su Dokta Goni sun ce tsallaka mai farfadiya ko kuma yawunsa ya taba mutum ba sa sa wa mutum ya kamu da cutar kamar yadda ake camfawa.
Duk rashin sani ne yake sa kawo wadannna abubuwa
Idan ana shan magani za a iya warkewa gabaki daya. Idan dai ana shan maganin lokaci mai tsawo.
Rukunan mutanen da suka fi kamuwa da cutar
Duk da cewa kwararru da dama sun bayyana cewa ana iya samun cutar farfadiya a tsakanin ko wane irin jinsi mace ko namiji, amma galibi ta fi shafar tsofafi da masu kananan shekaru.
Idan mutum ya manyanta aka samu wata cutar sankara a kwakwalwa.

Shin ana warkewa daga farfadiya?
Dokta Bukar ya ce idan aka gano anihin abin da ke kawo cutar farfadiya sanna aka warware shi to za a iya warkewa.
''Mukan kwantar da su a asibiti muna lura da yadda wadannan wayoyin masu kama da na lantarki ke aiki a kwakwalwarsu yayin da suke ci gaba da shan maguguna," in ji shi.
Amma ya ce: "Yawanci idan kamar rauni ne aka samu ko kuma lokacin haihuwa ne ba a cika warkewa ba, sai dai a rika yawan shan magani don rage yawan samun buguwa."
Sai dai kuma kamar yadda Dakta Goni ya bayyana, akwai magani da ake kira 'Anti-convulsants' a turance da hana yawan aukuwar farfadiyar, da akan bai wa masu dauke da ita .
"Muddin marar lafiya ya rika shan maganin yadda ya kamata, zai iya rage kaifin yawan aukuwar buguwar, amma idan ba haka ba zai iya kawo masa matsala," in ji Goni.

Me ya kamata a yiwa wanda fardadiya ta buge?
Masu dauke da cutar farfadiya na matukar bukatar taimako a koda yaushe, saboda irin halin da sukan samu kan su a lokacin da ta buge su.
Haka ya sa kwararru ke fadakar da mutane, musamman makusantan masu dauke da cutar cewa kada su rika kasancewa cikin duhu kan matakan da suka kamata su dauka na kai daukin gaggawa ga wadanda ke dauke da cutar.
Dr Goni ya bayyana cewa: "Ana son a tabbatar da an kawar da duk wani abu da aka san zai ji wa maras lafiya barazana kamar wuta, ko kujera, teburi ko wani karfe a lokacin da cutar ta buge shi".
Ya ce: "Kada a taru a kan maras lafiya don yana bukatar iska sosai, a kyale shi ya numfasa kafin nan a garzaya da shi asibiti".
Haka kuma in ji shi ma masani Dakta Bukar akwai masu al'adar dura wa mai farfadiya man ja ko wani jiko a baki wai don ya farfado, amma hakan ba daidai ba ne.
Ya kara da cewa: "Bai kamata a ba shi wani abu ko a dura masa magani a baki ba, hakan zai iya shake shi ya hana shi numfashi, ko a saka masa cokali ko wani abu a baki ba don zai iya kawo masa damuwa a lokacin".
Lokaci zafi ko kuma zafin rana ka iya kar yawan abkuwar bugun farfadiya ga mai dauke da cutar, idan aka samu matsala zai iya buge shi, haka ma idan sanyi ya yi yawa.

Abinda wasu masu cutar farfadiya ke cewa
Wani dattijo mai fama da cutar farfadiya ya shaida wa BBC cewa a da shi da danginsa suna cewa aljanu ne suka kama shi don haka ba su taba tunanin zuwa asibiti ba.
"Da muna rokon Allah ne da kuma maganin gargajiya, mun dauka aljanu ne, a da da zarar farfadiya ya buge ni sai in nemi wajen da wuta take in shiga, amma daga baya aka ba mu shawarar ganin likita," in ji dattijon.
Ita ma mahaifiyar wani matashi mai cutar farfadiya ta ce lokacin da abin ya shafe shi mun dauka iskokai ne shi ya sa suka rika yin na gargajiya.
Ta kara da cewa: "Lokacin nan mutane sai suka rika cewa iskokai ne, har ya samu shekaru da dama, shi ne daga baya aka ba ni shawarar in kai shi asibiti don a duba lafiyarsa, saboda tun yana karami ya taba faduwa ta kai."
Ta kuma bayyana yanayin yadda farfadiyar ke buge dan nata: ''Farkon da ya fara, cutar ta kan buge shi har sau goma a rana.
Wani magidanci da ya kamu da cutar da farfadiya shi ma ya bayyana yadda ya fara da cewa ya dauka ciwon ba na asibiti bane.
''Ya kai wajen shekara daya da wani abu lokacin da na fara cutar farfadiya, kuma mun fara na gargajiya ne amma abin sai ya rika karuwa shi yasa aka kai ne asibiti, yanzu ina samun sauki,'' ya ce.
Lokacin da ya kamata a gagaguta kai mai farfadiya wajen likita
Ya kamata wadanda ke tare da mai cutar farfadiya su rika lura sosai da yanayin da yake ciki, domin sanin lokacin da ya dace a dauki matakin gaggawa na ganin likita.
Alamomin dai in ji kwararru sun hada da:
- Jijjiga ko bugewar farfadiyar da ta wuce minti biyar.
- Daukewar numfashi da kuma fita daga hayyaci bayan farfadiyar ta saki marar lafiya.
- Bugun farfadiyar da ta wuce sau daya a rana ko lokaci guda.
- Marar lafiyan da ya ji rauni ko ya bugu sosai bayan farfadiyar ta sake shi.
- Sai kuma zazzabi me zafi da kan dade bai sauka ba.
- Mace mai juna biyun da farfadiya ta buge ta da ta.












