An yanke wa mutum biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya a Kano

Hangman

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Wata babbar kotu da ke jihar Kano, ta yanke wa wasu mutum biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samun su da laifuka daban-daban.

Kotun ta same su da laifin cinna wuta da amfani da makami abun da yayi sanadin mutuwar mutum biyar.

Yayin da take yanke hukunci, mai shari'a Amina Adamu Aliyu, ta ce bayanai da kuma shaidun da masu gabatar da ƙara suka gabatarwa kotun ne, ta yi la'akari da su wajen zartarwa mutum na farko hukuncin kisa.

Mutum na farko mai shekara 22, kotun ta same shi da laifin cinna wa wasu iyalai su uku wuta a cikin gida a unguwar Gayawa cikin ƙaramar hukumar Gaya a jihar Kano.

Lauyan masu gabatar da ƙara, Barista Lamido Soron Ɗinki ya yi bayanin cewa lamarin ya afku ne a watan Satumban shekara ta 2019.

Ya ce: ''Wanda aka yanke wa hukuncin ya ƙetara ya shiga wani gida da jarkar mai, ya kuma kwarara man a jikin ɗakunanan da mazauna gidan ke kwance a ciki, sai kuma daga bisani ya cinna wa gidan wuta. Lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar iyalin da ke zaune a gidan da suka haɗa da maigidan Aminu da matarsa da kuma ƴarsa guda ɗaya''

Barista Soron Ɗinki ya ƙara da cewa bayan masu gabatar da ƙara sun gabatar da shaidu, wanda ake zargin shi ma ya bayar da bahasi a gaban kotu, inda daga bisani kotu ta yanke masa hukunci kisa bayan ta tabbatar da cewa shi ne ya aikata laifin kisan.

Sai mutum na biyu wanda kotun ta ce ta same shi da laifin caccakawa kishiyar mahaifiyarsa wani abu, da kuma shaƙe ƙanwarsa har ta rasa ranta a unguwar Rijiyar Zaki cikin ƙaramar hukumar Ungogo.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Barista Soron Ɗinki ya bayyana cewa an aikata wannan laifi ne a watan Janairun shekara ta 2023.

Ya ce ''Wanda aka yanke wa hukuncin ya dawo gida ya nemi abinci ya rasa, kuma daman ya daɗe yana zargin kishiyar uwar tasa da hana shi abinci, lamarin da ya harzuƙa shi ya ɗauki doguwar sukundireba ya caccaka mata a wuya.''

Ya ƙara da cewa baya ga kishiyar mahaifiyarsa da ya cakawa sukundireba, wanda ake zargin ya kuma afkawa wata yarinya da ke gidan inda ya yi amfani da ɗankwali ya shake mata wuya har sai da ta mutu.

To sai dai lauyan wanda ya kashe kishiyar mahaifiyarsa, Mubarak Abubakar, ya ce suna da ja akan wannan hukunci, kuma za su ɗaukaka ƙara.

Ya ce: ''Muna ganin shaidun da suka gabatar guda biyu, da mahaifinsa da ɗansanda wanda ya gudanar da bincike kan batun, kuma muna da damar tambaya kan wasu bayanan da suka bayar. Mun shaida wa kotu cewa waɗannan bayanai ba su isa su gamsar da kotu har ta same shi da laifi ba.''

Lauyan ya ƙara da cewa al'umma na iya miƙa buƙatar nazarin takardun da suka jiɓanci wannan shari'a domin su tabbatar da yadda komai ya gudana kamar yadda doka ta tanada.

BBC ta yi yunƙurin ji daga bakin lauyan wanda ake tuhuma da cinnawa miji da mata wuta, amma haƙar mu ba ta cimma ruwa ba.

Waɗanda aka yanke wa hukuncin kisan, suna da damar ɗaukaka ƙara cikin kwanaki 90 bisa tsarin doka.