Sabon tsarin hada-hadar kudi na CBN zai kawo mana cikas a sana'armu — ‘Yan kasuwa

Asalin hoton, OTHER
‘Yan kasuwa a Najeriya na ci gaba da kokawa gane da sabon matakin babban Bankin Najeriya CBN na iyakance kudin da mutum zai iya fitarwa zuwa naira dubu 100 a Mako.
‘Yan kasuwar sun ce matakin mai yiwuwa ne zai kawo musu cikas sosai don kuwa, abokan hulɗarsu da yawa ba ma su da asusun ajiyar banki.
‘Yan kasuwa kamar wadanda ke kasuwar hatsi ta Dawanau da ke birnin Kano, akasarinsu na hada hada ne kudi hannu.
Daya daga cikin ‘yan kasuwar da BBC ta zanta da su ya ce suna kasuwancin sune da mutane daban-daban kama daga mutanen birni dana karkara, inda wasunsu ko asusun ajiyar banki basu da su dashi komai da tsabar kudi suke yinsu.
Ya ce, ‘’ Kamar misalin mutanen mu na karkara basu san a tura musu kudi ta waya ba, to kuwa ta yaya wannan kasuwanci zai yiwu?”.
Dan kasuwar ya ce da dama daga cikin wadanda suke hulda dasu a kasuwa manoma ne kuma daga karkara suka zo, don idan ya suka kawo hatsinsu kasuwa kamar buhu 10 zuwa sama, abin da suke so shine kawai a siye a basu kudinsu a hannu su koma gida, to irin wadannan yaya za’ayi da su?
Suma matan da ke kai kayansu kasuwar ta Dawanau wadanda yawancinsu ke sana’ar sarrafa gyada wajen samar da mai da kuli-kuli, sun shaida wa BBC irin matsalar da suke gani zasu shiga idan wannan mataki na CBN ya fara aiki.
Daya daga cikin matan ta ce, ita ko wayar salula ma bata ita ballantana asusun ajiya na banki.
Ta ce,” To idan an ce idan aka sayi kayanmu bayan mun kai kasuwa za a tura mana kudi ta banki to ya zamu yi ke nan, don bamu da asusun ajiya na banki, a hannunmu ake bamu kudi idan mun kawo kasuwa an siya.”
Babban Bankin Najeriya, CBN, ya ce daga ranar 9 ga watan Janairun sabuwar shekara ta 2023, yawan kudin da mutum zai iya fitarwa a banki a rana Daya shi ne naira dubu 20, a mako kuma naira dubu 100.
Kazalika CBN, din ya ce duk wanda ya je cire kudin da suka haura naira dubu 50 da cekin bankin da wani ya rubuta masa, to ba za a bashi kudin ba, yayin da dokar cire kudin da suka kai naira miliyan 10 ta amfani da bankuna daban-daban, tana nan yadda take.










