Mata 'yan kasuwa da suka maye gurbin shagunansu da shafukan intanet

Sharon Tarit

Asalin hoton, Sharon Tarit

    • Marubuci, Daga Sam Fenwick
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Business Daily presenter

BBC ta tattauna da matan Afirka uku - wata tsohuwar mai shagon sayar da kaya, da malamar makaranta, da kuma direbar tasi - da suka kara bunkasa samun kudin shigarsu tun bayan da suka rungumi sana'a ta hanyar shafukan sada zumunta na zamani.

Annobar korona ta tilasta wa mutane da dama sauya tunanin yadda za su rika samun kudin tafiyar da rayuwa.

Kungiyar masu bincike mai zaman kanta Caribou Digital, ta gano cewa mata a kasashen Kenya, da Najeriya da kuma Ghana na amfana da hanyoyin sadarwa na zamani - da ke ba su damar samun kudin shiga na tafiyar da rayuwarsu, a yayin da suke cigaba da daukar kula da 'ya'yansu.

Short presentational grey line

Sharon Tarit

Mis Tarit (a hoto na sama) ba ta yi tsammanin ninka irin kudin da ta saba samu a cikin watanni tara ba.

Annobar korona ta tilasta mata rufe shagonta na sayar da kayan jarirai a rukunan shaguna na Eldoret a yammacin kasar Kenya, kuma bayar da hayar dakunan kwana na Airbnb ya kasance mataki mafi sauki na shawo kan matsala.

Amma yanzu Mis Tarit, mai shekaru 29, na cikin matan Afirka da dama da ke samun sabbin sana'oi ta hanyar amfani da dandalin sada zumunta irin su Facebook, da WhatsApp, da Instagram, har ma da manhajojin tukin motocin tasi kamar Uber da Bolt.

Ta fara kasuwancinta da gida daya watanni tara da suka gabata, amma yanzu tana da guda bakwai - tana bayar da haya bayan rattaba hannun yarjejeniyar haya mai tsawon lokaci ta manahajar Airbnb.

"Ina samun kudi sosai fiye da irin kasuwancin da na yi a baya kafin barkewar annobar," Mis Tarit ta shaida wa BBC.

Mutane da ke amfani da kasuwancinta akasari baki 'yan yawon bude-ido ne da ke neman a shirya musu wuraren kwana a otal-otal da kuma 'yan kasuwa da suka fi gwammacewa su zauna a dakunan kwana na Airbnb a maimakon otal.

"Lokacin annobar korona abokaina da dana sun rasa aikinsu, inda suka fara amfani da dandalin sada zaumunta na shafukan intanet wajen samun kudin shiga. Yanzu suna sayar da kayan abinci ta shafin intanet kana suna aiki a matsayin direbobin da ke kai sakonnin kayan da aka saya," Mis Tarit ta ce.

Josephine Adzogble

Josephine Adzogble

Asalin hoton, Josephine Adzogble

Mis Adzogble, mai shekaru 32, kan fara gudanar da harkokinta wajen saka tallace-tallacen kayayyaki a dandalin sada zumunta na WhatsApp da kuma Facebook daga cikin gidanta a babban birnin Accra na kasar Ghana.

Tana amfani da damar da ta samu na babban sauyin da aka samu a fannin tattalin arzikin Afirka - karuwar kasuwannin shafin intanet.

Tana sayar da wayoyin salula, da na'urorin sanyaya dakuna, da akwatunan talabijij ta hanyar tallatawa da saka hotunansu a wani dandali na musamman da ta kirkira a WhatsApp da Facebook, har ma da wanda ta bude musamman saboda 'yan cocinta.

Mis Adzogble ta bar aikin koyarwar harshen Faransanci inda ta mayar da hankali wajen harkokin kasuwancin shafin intanet.

"An fi samun kudi fiye da aikin koyarwa. Nakan sayar da abu guda daya in kuma samu fiye da abin da nake samu a wata na aikin koyarwa. Ni uwa ce. Ina bukatar na bai wa 'yayana ingantaccen ilimin da ya kamata kuma suna karfafa min guiwar wajen 'yancin samun kudin shiga," ta ce.

Ga Mis Adzogble, gina tubalin mai kawri na dangantaka ta kostomomi shi ne ginshikin samun kudi ta shafin intanet.

"Ta yadda suke sayen kaya a hannunka, kana su yaba maka," in ji ta.

Ayobami Lawal

Ayobami Lawal

Asalin hoton, Ayobami Lawal

Mis Lawal, mai shekaru 34, na aiki wa kamfanonin tasi-tasi na Uber da Bolt a birnin Legas na Najeriya.

Amma kuma, bai zama wani abu mai sauki ba - in ji Ayobami mai 'ya'ya hudu, wacce ta kuma ce maza kan ki amincewa mata su tuka su.

"Lokacin da n afara tuka tasi-tasi a Legas duka mazan kan soke tafiyar ta su a lokacin da na isa wurin da zan dauke su," Mis Lawal ta bayyana.

"Legas birnin ne mai hayaniya da cunkoso, kuma dole sai ka kasance mai juriya kafin ka yi tuki a cikin garin. Maza ba sa tunanin zan iya jurewa. Dole sai ina rika janyo hankalinsu kafin su amince su shiga motar,'' ta kara bayyanawa.

Binciken da kungiyar ya Caribou Digital ya kuma gano cewa mata da dama da ke amfani da dandalin sada zumunta na zamani don samun kudin shiga na nuna damuwa game da tsaron lafiyarsu.

"Mata da dama da muka yi magana da su sun bayyana cewa ana cin zarafinsu ta hanyar lalata idan suka dauki mutane," jagorar binciken Grace Natabaalo ta shaida wa BBC.

"A yayin da gwamnatoci ke karfafa guiwar matasa mata da su kama irin wannan sana'a, suna bukatar sanin daga bangaren - cewa akwau hadurra kama ya kamata 'yansanda da hukumomin gwamnati su kula da su sosai," ta bayyana.

Amma Mis Lawal ta bayyana cewa abubuwan alherin sun rinjayi sharrin da ke ciki.

"Yana da matukar muhimmanci ka nemi sana'ar tafiyar da rayuwaka amma kuma ina son bayar da gudumawa ga tattalin arzikin kasa ta hanyar biyan haraji. Ina son in bunkasa kai na da kuma tattalin arzikin Najeriya," ta ce.