Hanyoyin ladabtar da ɗalibai maimakon duka

Asalin hoton, FB/Maikatanga Photography
Tun dai bayan kamun da rundunar ƴansandan jihar Jigawa ta yi wa wani malamin makarantar allo bisa zargin duka da ta kai ga kashe wani ɗalibinsa, ƴan Najeriya ke ta neman sanin duka ne kawai maganin ɗaliban marasa ji.
Shi dai malamin ya lakaɗa wa ɗalibin duka ne inda ta kai har ya rasa ransa, wani abu da ya sa malamin cire kai da marainan gawar da manufar ɓoye al'amarin ta hanyar nuna cewa matsafa ne suka aikata kisan.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu faya-fayan bidiyo da ke nuna yadda malamai suke ladabtar da ɗalibansu, a kafafen sada zumunta inda wasu suke zagewa iya ƙarfinsu wajen dukan ɗaliban da sunan ladabtar da su.
Me ya sa malaman suke bugun ɗalibai?

Asalin hoton, Aliyu I. Tilde/Facebook
Wannan ya sa BBC ta tuntuɓi Dokta Aliyu Tilde, wanda tsohon kwamishinan ilimi ne na jihar Bauchi, kuma fitaccen mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, musamman ilimi da tarbiya.
Tilde ya ce rashin sanin makamar aikin koyar da ɗaliban ne babbar matsalar da ake fama da ita.
"Duk wanda yake da ƙarancin ilimin koyarwa sai ya ɗauki irin tarbiyarmu ta Afirka irin ta gida wadda uwa ko uba suke bugun ƴaƴansu, sai ya ɗauka ta wannan hanyar ce zai ladabtar da ɗalibansa."
Sai ya ce koyarwa hawa-hawa ne, "akwai tsarin koyar da yara waɗanda ba su kai shiga firamare ba, akwai na ƴan firamare da na ƴan sakandare da na ƴan jami'a," in ji shi.
Malamin ya ce kowanne mataki akwai usulubinsa, sannan ciki akwai babi na musamman kan ladabtarwa na yadda zai koyar da malaman hanyoyin da za su ladabtar da ɗalibansu.
Dokta Tilde ya ce idan malami ya samu wannan horon shi ne zai sa ko da ɗalibai sun yi laifi ya gane wane irin mataki ya kamata ya ɗauka.
Ko duka na ladabtar da ɗalibai?
An sha samun labaran inda aka bugi ɗalibi ya samu rauni a makarantun boko da na allo, lamarin da Dokta Tilde ya alaƙanta da kuskure, domin a cewarsa, "bugu ba ya cikin hanyoyin ladabtar da ɗalibi."
Ya ce "kwata-kwata jigba ba ya cikin hanyoyin ladabtar da ɗalibai saboda maimakon ladabin, sai yaro ya kangare. Na san ɗalibai da yawa, ciki har da waɗanda muka taso tare da suka bar karatun allo, kuma har suka girma ba su iya haɗa baƙi ba saboda duka da malaman suke yi."
Ya ƙara da cewa akwai hanyoyin da ya kamata malamai su bi domin ladabin, wanda a cewarsa sun fi tasiri, sama da bugu.
Hanyoyin ladabtar da ɗalibai cikin sauƙi
A game da yadda ya kamata malamai su riƙa ladabtar da ɗalibansu, Dokta Tilde ya ce maimakon bugu, malaman su yi amfani da matakan da za su dawo da ɗaliban da hankalinsu ya fi muhimmanci.
"Ya danganci irin laifin. A makarantun boko matakan sukan bambanta da na makarantun allo, domin a na allo ne aka fi samun irin wannan matsala na bugun fitar hankali. Don haka hukunci ya danganta ne, domin lafin ma hawa-hawa ne."
- Jan hankali: Ya ce da farko shi ne ka masa magana, kuma shi ne ya fi kowane mataki muhimmanci. Ka fahimtar da shi ko su cewa abin da suka yi ba daidai ba ne. A cikin su 10, za ka iya samun takwas sun daina.
- Nanata jan hankali: Ya ce idan suka ci gaba, sai ka ake nanatawa, a nuna masa yadda abokansa suke yi, da fahimtar da shi illar da laifin zai haifar masa a gaba.
- Wariya: Ya ƙara da cewa idan ya ci gaba sai a kai ga ware shi a aji. A ce wannan kwanar marasa ji ce. Ko kuma a sa shi ya tsaya a tsaye, sauran ɗaliban suna, ko yara su fita hutun rabin lokaci shi a hana shi.
- Rubutu: Dokta Tilde ya kuma ce za a iya bai wa ɗalibin aikin rubutu mai yawa da zai kwana yana yi.











