Ya kamata a ba NJC ikon naɗa shugaban INEC

 Mambobin Majalisar sharia ta ƙasa ƙarƙashin jagorancin babbar mai sharia Kudirat Kekere-Ekun

Asalin hoton, NJC

Bayanan hoto, NJC
Lokacin karatu: Minti 2

A Najeriya yayin da zaɓen 2027 ke matsowa kusa wasu sun fara yin kiran karɓe ikon naɗa shugaban hukumar zaɓen ƙasar watau INEC daga hannun shugaban ƙasa kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.

Masu irin wannan ra'ayi na ganin cewa hakan na kawo cikas ga ingancin zaɓen ƙasar, a don haka ya kamata a yi gyara, yayin da ake ci gaba da tuntuɓa don gyara kundin tsarin mulkin ƙasar.

Wannan na zuwa ne yayin da tuni siyasar ƙasar ta fara ɗaukar zafi gabanin zaɓen 2027 da ke tafe.

Alhaji Yabagi Sani, shugaban jam'iyyar AD na cikin masu irin wannan kira kuma ya shaidawa BBC cewa yana cikin abubuwa da ke ci wa jam'iyyun ƙasar tuwo a ƙwarya:

''Da wuya ayi adalci idan wanda ke Mulki ne ya naɗa wanda zai jagoranci hukumar ta INEC''.

" Shi ya sa mu ka yi kira ga ƴan Majalisar dokoki wadanɗa ke yi wa kundin tsarin Mulki garambawul akan cewa wannan yana cikin ƙalubalen da zaɓe mai sahihanci ke fuskanta''. in ji shi.

Ya ƙara da cewa wannan ne da zai sa a gudanar da zaɓe mai inganci wanda jama'a za su karɓa.

''Abinda mu ke cewa shi ne kada ya zama cewa shi shugaban ƙasar ne zai naɗa tare da miƙa suna ga majalisar dokokin ƙasar''

Alhaji Sani ya nemi a bai wa Majalisar sharia ta ƙasa watau NJC wannan dama.

''Duk wanda ya cancanta a ba shi muƙamin, Majalisar sharia ta ƙasa za ta iya miƙa sunansa ga Majalisar dokoki domin su amince da naɗinsa''

Shugaban jam'iyyar ta AD ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ne ya ba shugaban ƙasa wannan dama amma kuma an daɗe ana kiraye -kirayen a yi wa sashin gyra saboda a samu adalci wajan gudanar da zaɓen.