Taimakon da ya kamata a yi wa yaron da ya ƙware

...

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Aisha Babangida
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

Ƙwarewa na ɗaya daga cikin manyan dalilan da ke jawo mummunan rauni ko mutuwa a ƙananan yara, musamman waɗanda ba su kai shekara biyar ba.

Ƙwarewa na iya faruwa cikin ƙanƙanin lokaci ko da a lokacin cin abinci, lokacin da yaron yake shan mama, lokacin wasa, ko ma lokacin barci.

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, dubban yara a faɗin duniya na rasa rayukansu duk shekara ta dalilin ƙwarewa ko shaƙewa saboda hanyoyin numfashi ne ke toshewa.

Dalililin haka ne BBC ta tuntuɓi Dr. Aisha Bako, wata likitar yara a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja, wadda ta bayyana muhimman matakan taimako da kowanne iyaye ko mai kula da yara ya kamata ya sani idan yaro ya shaƙe.

"Shaƙewa zai iya zama a ɓoye ko kuma a bayyane, amma a kowanne hali, la'akari da lokaci na da matuƙar muhimmanci," in ji Dr. Aisha.

Likitar ta ce "Yara ballantana ƴan ƙasa da shekara biyu sun kasance suna son saka abubuwa na ko wane iri a baki idan suka samu, shiyasa yake da matuƙar muhimmanci ga iyaye su san matakan agajin gaggawa na farko da za a bai wa yaron da ya shaƙe."

Muhimman matakan gaggawa idan yaro ya ƙware

...

Asalin hoton, Getty Images

Dr. Aisha Bako ta lissafo wasu muhimman taimakon gaggawa da ya kamata iyaye da sauran mutane su sani domin taimakawa yaron da ya shaƙe, ko da a gida, ko kasuwa ko ofishi ko wurin jama'a haka.

  • Mutum ya kasance cikin natsuwa kuma yayi ƙoƙarin gane yanayin da yaro ke ciki:

Likitar ta ce "Abu na farko shi ne a gane ko yaron da gaske ya shaƙe. Idan har yana ƙoƙarin tari kuma yana kuka ko magana, hakan yana nuni da cewa hanyar numfashinsa ba ta toshe gaba ɗaya ba,"

"A irin wannan lokaci, kawai a ƙarfafa shi ya cigaba da tarin tare da shafa masa baya. Kada a buga bayan." in ji likitar.

  • "Ga yaron da bai kai shekara ɗaya ba kuma ya ƙware – a ɗaura shi a kan bayan hannun, fuskarsa na kallon ƙasa sai, a tabbatar an riƙe kansa da kyau, sai a buga masa baya sau 5 da tafin hannu."
  • "Idan abun da ya ƙwarar da yaron bai fito ba, a juyar da shi baya – fuskarsa na sama sannan a danna tsakiyar ƙirjinsa sau 5 da yatsun hannu biyu." in ji likitar.

Likitar ta ce a ci gaba da maimaita bugun baya da dannan ƙirji har sai yaro ya sami sakewa kuma abin da ya shaƙe shi fito ko kuma taimako ya iso

...

Asalin hoton, Getty Images

  • Idan yaron ya wuce shekara ɗaya – a yi amfani da dabarar da ake kira da 'Heimlich' wato za a rugumo wanda ya shaƙe ta baya a tsaye, sai a nannaɗe hannuwa a ƙugunsa, samar cibiyarsa sai ana matsawa da ƙarfi daga wurin zuwa saman ƙirji" in ji ta.

Liktar ta ƙara da cewa za a ci gaba da yin hakan har sai an fitar da abin da yaron ya ƙware da shi ko har taimako ya iso.

...
  • Idan yaron ya fita hayyacinsa ko ya daina numfashi, a yi ƙoƙari a kira taimakon gaggawa nan take, idan kuma an san yadda ake CPR wato bai wa mutum iska ta baki da kuma danna ƙirjinsa, sai a yin hakan.", likitar ta ƙara da cewa
  • Kada ka zura yatsa a bakin yaro idan ba a ga abin da za ka cire ba.

"Daya daga cikin kurakuran da iyaye ke yi shi ne zura yatsa cikin bakin yaron, hakan na iya zurfafa abun da ya kwarar da yaron can cikin makogwaro" in ji ta.

...

Alamomin da ke nuna yaro ya ƙware

Liktar ta lissafo alamomin da ke nuna cewa yaro ya ƙware kamar haka;

  • Za a ga yaro yana riƙe wuyansa ko kirjinsa da hannu
  • Za a ga yaro yana ƙoƙarin yin tari amma sauti ba ya fita
  • Za a ga yaron yana buɗe baki amma ba ya fitar da wani sauti.
  • Za a ga fuskar yaro ko leɓe suna sauya launi zuwa ja ko shuɗi wanda ke nuna alamar samun rashin isasshen numfashi.
  • Za a ga numfashin yaro yana karanci ko ya daina gaba ɗaya
  • Za a ga yawun baki ko majina na fitowa fiye da kima

Abubuwan da ya kamata iyaye su sani

Dr. Aisha ta kuma lissofa wasu abubuwa da iyaye ya kamata su sani a matsayin shawararta. Ta ce;

  • Tsananta kula a lokacin da yara ke cin abinci ko wasa in ji Dr. Bako.
  • A yayyanka abinci ƙanana kafin a ba su.
  • A tabbatar yara suna zaune sosai yayin cin abinci – kada su ci suna wasa.
Yara

Asalin hoton, OTHERS

  • A guji ba su kayan wasa da za su iya sakawa cikin baki ko iya tsotsa ko haɗiyewa ba.
  • A tsabtace ɗaki da guri daga ƙananan abubuwa da yara za su iya saka wa a bki.
  • A koya wa yara su tauna abinci sosai kafin su haɗiye.
  • Iyaye su koyi yadda aka yin CPR a jarirai da yara: "Yana da matuƙar amfani ga iyaye da masu kula da yara su koyi yadda ake yin CPR wato bai wa mutum iska domin ya dawo da numfashi ta hanyar danna ƙirji da busa iska ta baki, yin hakan na iya ceton rai."

A Najeriya a cewar Dr. Aisha, asibitoci na karɓar matsalolin da ke da buƙatar kulawar gaggawa na yara da suka shaƙe akai-akai, inda abubuwa kamar shinkafa, gyaɗa, ko wasu abubuwa da yara ke ɗauka su saka a baki ke haddasa hakan.