Lafiya Zinariya: Yadda za ki haɗa kunun jariri mai gina jiki don kauce wa tamowa

Bayanan sautiLatsa sama don sauraron shirin
Lafiya Zinariya: Yadda za ki haɗa kunun jariri mai gina jiki don kauce wa tamowa

Masana masu bayar da shawara a ɓangaren abinci, sun bayyana cewa shirya abinci ga jariri ta hanyar da ya dace na taimakawa wurin kare shi daga kamuwa da cutar tamowa.

Wasu daga cikin matakan da za su sanya jarirai da ƙananan yara cikin koshin lafiya sun haɗa da:

  • Shayar da nonon uwa zalla na wata shida na farko a rayuwar jariri.
  • Kiyaye tsafta a ɓangaren uwa da yaro da wurin shiryawa da bashi abincin.
  • Farawa da bashi ruwa mai tsafta bayan wata shida na shan nonon uwa zalla.
  • Fara bashi abinci mai ruwa-ruwa daban-daban domin gane wanda zai karɓe shi. Misali koko ko kunu.
  • Fara lasa masa abinci a baki domin ya san ɗanɗanon gishiri da suga.
  • Dama abinci mai tauri domin ya yi wa jariri taushi wurin ci.
  • Kada a yaye jariri farat ɗaya, a bi shi sannu-sannu.

Domin jin cikakken bayani kan yadda za ki haɗa abincin jariri mai gina jiki, ciki har da kunun jarirai, latsa makunni na sama don ji daga bakin masaniya kan harkar abinci, Hajara Idris.