Yadda aka mayar da jaririyar da aka yi wa tiyata a zuciya fagen daga a Gaza

Jariri Niveen kenan kwance akan matashi a tantinsu da ke Gaza, inda aka lullube ta da bargo mai launin ruwan bula da fari.
Bayanan hoto, Niveen mai watanni 6 na bukatar a yi mata tiyata a zuciya
    • Marubuci, Adnan El-Bursh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic Gaza reporter
    • Marubuci, Lina Shaikhouni
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 6

Enas Abu Daqqa ce zaune cikin tantinsu a sansanin 'yan gudun hijira da ke al-Shati da ke arewacin zirin Gaza, dauke da 'yarta Naveen, ga wata fanka da ke taimakawa wajen rage zafin da ake fama da shi a safiyar.

Hankalin Enas ba a kwance ya ke ba, ta damu kan halin da 'yarta Naveen ke ciki na rashin lafiya. Watannin ta 6, an kuma haife ta ana tsaka da yaki da kuma rami a zuciyarta.

Kamar yadda ta bayyana, ta na fadi tashin ganin 'yarta ta rayu a daidai lokacin da fannin lafiya ke kara tabarbarewa a Gaza. Naveen ta tsanyara kuka idanunta masu launin ruwan kasa sun firfito alamar da ke nuna tsananin rashin lafiya.

"Yakin nan mai tsanani ne a gare ta," kamar yadda Enas ta shaidawa BBC. "Ba ta girma, ba ta da nauyi, kuma kowanne lokaci za ta iya fara rashin lafiya."

Damar da ake da ita. domin ceton Niveen, shi ne a bata kulawar gaggawa a wajen Gaza. Kuma afarkon watan Maris kasar Jordan ta tabbatar da hakan.

Lokacin da aka cimma tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas, an samu damar fitar da yara 29 da ke bukatar kulawar gaggawa kuma Naveen na daga cikinsu, an kai su asibiti a kasar Jordan. Mahaifiyarta da 'yayarta na daga cikin wadanda sukai mata rakiya.

Su ne yara na farko da aka kai Jordan, bayan Sarki Abdullah ya sanar da shirin yi wa yara 2,000 da ke tsananin bukatar kulawar likita daga Gaza zuwa asibitocin Jordan. An yi aikin ne da hadin gwiwar hukumomin Isra'ila da sukai bincike kan iyayen yaran da su kan su yaran.

Likitoci a Jordan sun yi nasarar yi wa Naveen tiyata, kuma sannu a hankali ta na murmurewa.

Sai dai makonni biyu bayan hakan, yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta rushe, hakan na nufin an koma yaki fiye da lokutan baya. Enas ta shafe makonni ta na kallon abin da ke faruwa a Gaza, ta akwatin talbijin din dakin asibitin da suke a Jordan, ta shiga damuwa kan halin da mijinta da sauran 'ya'yanta ke ciki a gida.

Kwatsam a daren ranar 12 ga watan Mayu, hukumomin Jordan suka shaidawa Enas za a maida su Gaza a wanshekare, a cewarsu Naveen an kammala aikin da aka yi wa Naveen.

Lamarin ya kada Eanas.

"Mun baro Gaza lokacin an tsagaita wuta. Ta yaya za ku maida mu yanzu da ake tsaka da yaki?" ta fada cikin fusata.

Enas sanye da bakar riga da gyale ruwan kasa, rike da 'yarta Naveen da abin wasa a hannunta a cikin tantinsu da ke Gaza.
Bayanan hoto, Enas ta damu da halin da 'yarta Niveen ke ciki, na tabarbarewar lafiya a wurin da ya ke tamkar sansanin mutuwa
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Enas ta hadu da mijinta da 'ya'yanta a Gaza. Sun ce 'yarsu ba ta gama warkewa ba aka dawo da su, sun damu matuka kan abin da gobe za ta haifar.

"'Yata na cikin mawuyacin hali, wanda ka iya ajalinta," in ji Enas. "Ta na fama da ciwon zuciya, wasu lokutan ta na fama da sarkewar numfashi, sannan launinta kan koma na sararin samaniya, ba za ta iya ci gaba da rayuwa a cikin tanti ba."

A ranar 13 ga watan Mayu, Jordan ta sanar da mayar da yara 17 zirin Gaza, bayan kammala yi musu magani. Wanshekare aka sake kai yara 4 Jordan daga Gaza.

Hukumomin Jordan sun shaida wa BBC, dukkan yaran da aka mayar Gaza na cikin koshin lafiya, sun kuma yi watsi da ikirarin cewa an mayar da yaran da ba su gama warkewa zuwa Gaza ba.

Hukumomin sun ce, tun da fari masarautar Jordan ta yi bayani dalla-dalla kan aniyarta na mayar da yaran da zarar sun samu sauki, sun ce hakan na da muhimmanci kan dalilai na siyasa.

"Manufar Jordan ita ce tabbatar da Falasdinawa na kasarsu, ba wai su bada gudummawar maida su 'yan gudun hijira a wasu kasasshe ba," kamar yadda sanarwar hukumomin Jordan din da ta aika wa BBC ta bayyaba. Sun ce mayar da yaran 17, za ta bayar da damar daukar karin yaran da ke bukatar taimakon a Gaza.

Sai dai wani jami'in ma'aikatar lafiya da Hamas ke tafiyarwa a Gaza ya shaida wa BBC cewa yaran da aka dawo da su Gaza na bukatar kulawa, amma an dawo da su tsakiyar yaki kuma hakan barazana ce ga lafiya da rayuwarsu.

'Dawowar dole'

Wannan ita ce damuwar Nihaya Bassel mai shekaru 30. Danta Muhammad dan shekara daya, na fama da cutar sarkewar numfashi wato asthma da matsalar abinci. Ta yi amanna danta bai samu kulawar da ta dace ba.

"Mun sake dawowa zaman tsoro da zullumi da yunwa, kewaye da mutuwa,"in ji Nihaya idanunta cike da hawaye. "Ina zan sama wa dana madarar da ya ke bukata? duk da ya shekara daya amma baya iya cin abinci sai dai wannan madarar, saboda da zarar ya ci abinci zai fara rashin lafiya."

Isra'ila ta yi wa zirin Gaza kawanya na sama da makonni 10, babu kayan agaji ko dai abinci, ko ruwan sha da magani da man fetur da dukkan abubuwan bukatun yau da kullum da ya shiga zirin. Lamarin da ya janyo tagayyara da matsananciyar yunwa ga Falasdinawa.

Ta kare matakin da cewa matsa lamba ne ga mayakan Hamas su sako Isra'ilawan da sukai garkuwa da su.

Kungiyoyin agaji sun yi gargadin halin da Falasdinawa ke ciki ya munana ana kuma gab da fadawa matsananciyar yunwa. A ranar Litinin din makon da ya wuce ne Isra'ilar ta sanar da barin shigar da kayan abincin da ake bukata zirin na Gaza, shi ma dan kadan da fakewar Hamas ka iya amfani da damar wajen kwashewa. Shi ma hakan ya samu ne sakamakon matsin lambar Amurka.

Nihaya dauke da danta Muhammad a tantin da suke zaune a Gaza
Bayanan hoto, Nihayata ce danta Muhammad ba zai iya jurewa yanayin da ake ciki a Gaza ba

A halin yanzu, Nihayana zaune ne a wani tanti da ke sansanin 'yan gudun hijira na al-Shati da danta Muhammad da iyalan dan‘uwan mijinta. Mjinta da 'ya'yansu uku sun tsere arewacin Gaza, sun guje wa tashin bama-bamai da makamai masu linzami da Isra'ila ke kai wa a lokacin da Nihaya ke kasar Jordan.

"A nan na bar 'ya'yana tare da mijina, sun shiga mummunan yanayi a lokacin da ba na nan," in ji Nihayalokaci guda kuma ta fashe da kuka.

"Kullum su na cikin zuciyata da tunanin halin da suke ciki a lokacin da na ke Jordan. Duk na yi haka ne domin danmu ya samu kulawar likita, don me za a tilasta mana dawowa alhalin ba a gama yi masa magani ba?"

A lokacin da ta ke magana, mu na iya jin karar makamai masu linzamin Isra'ila da jirage marassa matuka. Muhammad ya rugo da gudu wurinta, mun ga hayaki na tashi a wajen ta kofar tantin da iyalan ke amfani da shi domin girki.

Da kyar ta iya ci gaba da magana, ta na bayyana mana yadda sukai ta guje-guje wurare daban-daban a Gaza.

"Da karfe 4 na asuba muka fito, ba mu isa Gaza ba sai kusan karfe 11 na dare,'' Nihaya ta ce su na zuwa iyakar Jordan da Gaza a nan suka fuskanci wulakanci daga sojin Isra'ila.

"Kawai suka fara tsine mana, sun yi barazanar za su lakada mana duka. Sun kwace kudadenmu da wayoyin hannu, kai har da jakunkunanmu, komai da ke tare da mu sun kwace,'' in ji Nihaya, haka suka bar su tsura babu komai.

Ita ma Enas ta shaida mana abin da ya faru da ita, an kwace komai ciki har da magungunan 'yarta Naveen.

Rundunar sojin Isra'ila ta shaida wa BBC cewa an karbe kudaden da suka haura wanda ya kamata su wuce da su, kuma doka ce kan 'yan Gaza da suke dawowa daga Jordan saboda zargin za a iya amfani da su wajen ayyukan ta'addanci a Gaza. Ta ce sun adana kudaden ana kuma gudanar da bincike kan su. Ba kuma su bada dalilin da ya sa suka kwace sauran kayayyakin matafiyan ba.

Nihaya ta ce hannu rabbana ta dawo daga Jordan, hatta takardun asibitin danta duk sojin Isra'ila sun kwace.

Kasar Jordan dai ta ce ta bai wa yara irin su Naveen da Muhammad kulawar da ta dace, kuma dukkan iyalan sun tabbatar da hakan.

Sai dai iyalan na cikin damuwa, kan zaman 'ya'yansu a wurin da ya fi ko ina hadari a duniya da ake yaki babu dare ba rana, hakan zai sake tabarbare lafiyar da 'ya'yansu suka fara samu.

"An kai matakin da ina cike da farin ciki sakamakon lafiyar da dana ya fara samu, ina cikin farin ciki idan na gan shi ya na walwala,'' in ji Nihaya, yayin da hawaye ya cika mata ido. ''Amma a yanzu fargaba da tsoro sun cika min zuciya, an dawo da hannun agogo baya. Ina cike da tsoro, ba na son dana ya mutu.''