Dalilan da suka sa Chelsea ta kori Thomas Tuchel

Asalin hoton, Reuters
Masu sharhin kwallon kafa da dama sun yi hasashen cewa daga kalaman Thomas Tuchel a hira da manema labarai bayan Dynamo Zagreb da doke shi a gasar Zakarun Turai, sun nuna cewa ya ci taliyar karshe a Chelsea, don a cewarsa 'ba bu abinda ke tafiya daidai a kungiyar.'

Asalin hoton, Getty Images
1. Tarihi ne ya maimaita kansa
Kuma ga duk wanda ke bibiyar yadda ake tafiyar da kungiyar tun lokacin Roman Abramovich ba zai yi mamaki ba.
Chelsea ta kashe fam miliyan 255 a kaka daya, abunda wata kungiya a Ingila bata taba yi ba a tarihi, to amma sai gashi ta kori kocin da ya ci mata kofin Zakarun Turai bayan ya gaji Frank Lampard.
Hakan na nufin kungiyar ta Stamford Bridge ta yi abinda ta saba, wato rashin bai wa koci uzuri ko da ya yi abun azo a gani a baya.
Idan aka duba tarihi, Chelsea ta kori Mourinho bayan ya ci kofin Firimiya, haka kocin Tottenham na yanzu Antonio Conte, uwa uba ma Di Matteo wanda har kofin zakarun turai ya ci da kofin kalubale a matsayin kocin riko.
To amma inda suka sha bamban da Tuchel shi ne an bashi wuka da nama a kan duka sauran masu horarwar.
Ba bu kungiyar da za ta baka damar kashe fam miliyan 255 ka sayi yan wasa ka kuma karbo wadanda ke zaman aro a lokaci guda ba tare da ka sayar da wasu ba kuma kasa kasa cin wasa sannan a kwashe lafiya.
Misali a bara ya siyo Ben Chilwell fam miliyan 50, amma kuma bana ya ajiye shi a benci duk da rawar da ya taka bara, ya siyo Cucurella. Ya siyo Wesley Fofana fam miliyan 70 alhali yana da Chaloba, matashin dan wasa da ya haska sosai bara.
Haka ma ya karbo masu zaman aro kamar Gallager da Broja, matasa ne da ake rububi, to amma sun dawo sun sami cewa ya siyo Sterling ga Havertz ga Pulisic ga Aubameyang ya siyo.
Wato a takaice ya tara yan wasa da dama a kungiyar da bai san yadda zai amfani da su ba, kuma hakan na nufin fitar da sha dayan farko ya zame masa abu mai wahala, kamar yadda muka gani a wasannin da ya sha kashi baya bayannan.
To amma kuma duk da haka gaskiya Todd Boehly ya yi gajan hakuri wurin korar Tuchel, duka wasa nawa aka yi? Shi kan shi yaushe ya sayi kungiyar?
'Yan wasan da Chelsea ta dauka a bana:

Asalin hoton, Getty Images
- Raheem Sterling (£50m, Manchester City)
- Kalidou Koulibaly (£34.2m, Napoli)
- Omari Hutchinson (Kwantiragi ya kare, Arsenal)
- Gabriel Slonina (£12.3m, Chicago Fire)
- Carney Chukwuemeka (£20m, Aston Villa)
- Marc Cucurella (£55m, Brighton & Hove Albion)
- Wesley Fofana (£72.4m, Leicester City)
- Pierre-Emerick Aubameyang (£10.8m, Barcelona)
- Denis Zakaria (aro, Juventus)
Kudin da ta sayo ‘yan wasa: £251.1m
Wadanda suka bar kungiyar a bana:

Asalin hoton, EPA
- Timo Werner (£18m, RB Leipzig)
- Billy Gilmour (£9.4m, Brighton & Hove Albion)
- Michy Batshuayi (£3.2m, Fenerbahce)
- Marcos Alonso (Kwantiragi ya kare, Barcelona)
- Antonio Rudiger (Kwantiragi ya kare, Real Madrid)
- Charly Musonda (ta barshi ya bar kungiyar)
- Danny Drinkwater (ta barshi ya bar kungiyar)
- Jake Clarke-Salter (Kwantiragi ya kare, Queens Park Rangers)
- Andreas Christensen (Kwantiragi ya kare, Barcelona)
- Matt Miazga (Kwantiragi ya kare, FC Cincinnati)
- Ross Barkley (Kwantiragi ya kare transfer)
- Emerson Palmieri (West Ham United)
- Kenedy (Real Valladolid)
‘Yan wasan da ta bayar aro:
- Lucas Bergstrom (Peterborough United)
- Sam McClelland (Barrow)
- Romelu Lukaku (Inter Milan)
- Nathan Baxter (Hull City)
- Jamie Cumming (MK Dons)
- Ian Maatsen (Burnley)
- Tino Anjorin (Huddersfield Town)
- Henry Lawrence (MK Dons)
- Levi Colwill (Brighton & Hove Albion)
- Malang Sarr (Monaco)
- Callum Hudson-Odoi (Bayer Leverkusen)
- Abdul-Rahman Baba (Reading)
- Xavier Simons (Hull City)
- Dujon Sterling (Stoke City)
- Ethan Ampadu (Spezia)
- Harvey Vale (Hull City)
- Bryan Fiabema (Forest Green Rovers)
- Jayden Wareham (Leyton Orient)
Abin da ya haddasa dagulewar lamurra a Chelsea

Asalin hoton, Getty Images
Tafiyar daraktar wasanni Marina Granovskaia da tsohon golan kungiyar Petr Cech ya kara lalata lamurra a Chelsea lura da rawar da suka taka a ci gaban kungiyar a lokacin Abramovich.
Kazalika an samu rashin jituwa tsakanin shi da abokan aikinsa na horarwa Coching Staff kenan da ma su kansu yan wasan, saboda kamar yadda na fadamaka kowa na duban ya cancanci a fara da shi.
Bugu da kari ga shi ya kasa cin kananan wasanni tun ba a je ko‘ina ba a kakar nan.
Leeds ta doke Chelsea haka Southampton wasannin ma da ya iya ci da kyar da gumin goshi ne kamar na West Ham da kunnen dokin da ya yi a wasan hamayya da Tottenham.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bai kamata Chelsea ta bar wasu 'yan wasan su bar kungiyar ba
Tun kan fara kakar bana bai kamata Chelsea ta bari kwantiragin Antonio Rudiger ta kare ba tare da an tsawaita masa ita ba, domin nawa za a bashi kan abinda ya bukata.
Mai zai yi a Real Madrid tun da ya lashe Champions League a kungiyar Stamford Bridge, maimakon wwasu 'yan wasa da aka dauka a bana da an tsawaita zamansa a kungiyar.
Haka kuma Andreas Christensen da Marcos Alonso duk bai kamata a ce sun bar Chelssea ba, domin sun saba a kungiyar an kuma san rawar da suka taka.
Chelsea ba ta damu da daukar matasan da take rena ba
Chelsea tana kan gaba wajen tarin matasa da take da su, amma ba ta morarsu, inda da dama sai da bayar da aronsu daga baya ta sayar da su sai kaji sun zama wasu a fannin tamaula a duniya.
Misali shi nee Mohamed Salah, wwanda dan kwallonta ne ta kasa mora ta sayar da shi a Roma daga baya Liverpool ta dauka sauran sai tarihi.
Saboda haka ya kamata Chelsea take amfani da matasan 'yan wasan da take da su maimakon kashe dan karen kudi wajen sayo ssabbbin 'yan kwallo.

Asalin hoton, Getty Images
Wa zai maye gurbin Tuchel?
To tuni jaridu sun fara bayyana cewa Chelsea ta fid da kociyoyi uku da zu iya maye gurbin Tuchel.
Daga ciki akwai tsohon kocin Tottenham da PSG Mauricio Pochettino.
Akwai kuma tsohon kocin Jamus Joachim Low, wanda ya ci mata kofin duniya a 2014 kuma dama Chelsea ta dade tana sha’awarsa.
Sai kuma Graham Potter da yanzu haka ke horar da Brighton, Shi kuma matashin koci ne da ya bada mamaki irin yadda ya farfado da karamar kungiya da yan kasafin kudin da bai taka kara ya karya ba. Kuma a gani na zai fi dacewa da Chelsea a yanzu.











