Ko Chelsea za ta taka rawar gani a kakar bana kuwa?
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.
Rahoto kai-tsaye
Mohammed Abdu
Ra’ayoyi da kuke tafkawa a kan shafin BBC Hausa Facebook
Kan doke Bayern Munich da Man City ta yi a wasan sada zumunta
Fulham ta kusan daukar Mbabu
The Mail ta bayar da rahoton cewar Fulham na kokarin karkare cinikin fam miliyan 6.4 don daukar dan wasan Wolfsburg dan kasar Switzerland, Kevin Mbabu.
Ta kuma ce mai shekara 27 an kammala auna lafiyarsa a Portugal ranar Asabar ana kuma sa ran zai je Landan don kammala cinikin.

Asalin hoton, Reuters
'Yan wasa uku na Brazil za su tsawaita zamansu a Real Madrid
Wasu rahotanni na cewar Real Madrid ta bari ana ta ciniki a Sifaniya, sai dai kungiyar na shirin tsawaita yarjejeniyar 'yan wasa uku a kungiyar.
Cikin matasan 'yan wasan sun hada da Eder Militao da Vinicius Jr da kuma Rodrygo.
Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Davies ya saka hannu kan ci gaba da zama a Tottenham
Mai tsaron bayan Tottenham, Ben Davies ya saka hannu kan kwantiragin kaka daya da zai kare a 2025.
Mai shekara 29 dan kwallon tawagar Wales ya yi wasa 271 a Tottenham, tun bayan da ya bar Swansea a 2014.

Asalin hoton, Getty Images
Ra’ayoyi da kuke tafkawa a kan shafin BBC Hausa Facebook
Dangane da nasarar da Barcelona ta yi kan Real Madrid a wasan sada zumunta a Las Vegas din Amurka.
An tabbatar da Arsenal na son daukar Paqueta
The Times ta wallafa cewar Arsenal ta tabbatar da son sayen dan kwallon Lyon, Lucas Paqueta, amma kawo yanzu ba ta taya dan wasan mai shekara 24 dan kasar Brazil ba.
Kane ya ci kwallo biyu a Tottenham a wasan sada zumunta, Rangers 1-2 Tottenham
Harry Kane ne ya ci kwallo biyu a wasan da Tottenham ke yi don tunkarar kakar bana, wadda ta yi nasara a kan Rangers da ci 2-1 a karshen mako.
Sabon dan kwallon da Tottenham ta dauka Yves Bissouma ya buga wasan tare da Richarlison da Ivan Perisic da Djed Spence da Clement Lenglet da kuma Fraser Forster a fafatawar da aka yi a filin wasa na Ibrox.

Asalin hoton, Reuters
Ra’ayoyi da kuke tafkawa a kan shafin BBC Hausa Facebook
Dangane da nasarar da Barcelona ta yi kan Real Madrid a wasan sada zumunta a Las Vegas din Amurka.
Ko kwalliya za ta biya kudin sabulu a Barcelona a bana?
A watan da ya gabata mataimakin shugaban fannin tattalin arzikin Barcelona Eduard Romeu ya ce yana bukatar Yuro miliyan 500 don "ceto kungiyar".
Yanzu, makwanni shida bayan haka, kungiyar na ta wadaƙa da kuɗi wajen sayan ƴan wasa.
Kimanin fan miliyan 100 ƙungiyar ta kashe wajen sayo dan wasan Leeds Raphinha da na Bayern Munich Robert Lewandowski, haka kuma tana zawarcin dan wasan Sevilla Jules Kounde da na Manchester City Bernardo Silva.

Asalin hoton, EPA
PSG ta amince za ta karbi aron Mukiele daga Leipzig
Jaridar Daily Mail ta wallafa cewar Paris St-Germain ta amince da tayin biyan fam miliyan 13 domin karbar aron dan kwallon RB Leipzig, Nordi Mukiele, mai shekara 24.

Asalin hoton, Reuters
Hulda ba ta kare ba tsakanin Barcelona da Messi
ESPN ta wallafa cewar shugaban Barcelona, Joan Laporta bai yanke tsammanin cewar Lionel Messi zai iya sake komawa Camp Nou da taka leda.
Shugaban ya sanar cewar har yanzu Messi yana da rawar da zai taka a Camp Nou.
Kyaftin din tawagar Argentina ya bar Barcelona, bayan kaka 21, wanda ya koma Paris St-Germain.

Asalin hoton, Reuters
ESPN ta ce Barcelona na shirin kara zama da Manchester United kan batun cinikin Frenkie de Jong.
United na fatan daukar dan kwallon tawagar Netherlands, domin kara karfin kungiyar don fuskantar kakar bana.
Arsenal ce kan gaba a Ingila a kashe kudin sayen 'yan wasa a bana
Arsenal ce kan gaba a yawan kashe kudi wajen sayo 'yan wasa a Premier League.
Kawo yanzu Gunners ta kashe fam miliyan 121.5, wajen sayo 'yan kwallo biyar a bana da suka hada da Gabriel Jesus da Oleksandr Zinchenko da Fabio Vieira da Marquinhos da kuma Matt Turner.
Kwalliya ta fara biyan kudin sabulu, bayan da Arsenal ta yi nasara a karawa ukun da ta yi a Amurka don tunkarar kakar bana da cin kwallo tara aka zura mata daya a raga.
Gunners wadda ta yi ta biyar a kakar da ta wuce za ta buga Europa League a bana.

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta caskara Chelsea a wasan sada zumunta, Arsenal 4-0 Chelsea
A karshen mako Arsenal ta caskara Chelsea da ci 4-0 a wasan sada zumunta da suka fafata a Orlando.
Wadanda suka ci wa Gunners kwallayen sun hada da Gabriel Jesus da Martin Odegaard da Bukayo Saka da Albert Sambi Lokonga.
Hakan na nufin Arsenal ta yi nasara a dukkan wasa ukun da ta buga a Amurka da cin kwallo tara aka zura mata daya a raga a wasannin sada zumunta don tunkarar kakar da za a fara cikin watan Agusta.

Asalin hoton, Reuters
A rana irin ta yau a 2018 Alphonso Davies ya koma Bayern Munich.
Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Mykolenko da Patterson sun taka rawar gani a wasan Everton, Blackpool 2-4 Everton
Sabbin 'yan wasan da Everton ta dauka a bana, Nathan Patterson da kuma Vitalii Mykolenko sun taka rawar a karawar da suka doke Blackpool, suna daga cikin wadanda suka zura kwallo a raga a karawar.
Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Alli ya ci kwallo a wasan farko da Everton ta ci a shirin tunkarar kakar bana, Blackpool 2-4 Everton
Everton ta yi nasarar Blackpool ranar Lahadi karawar farko da ta yi nasara a wasannin sada zumunta don shirin tunkarar kakar bana.
Eveton ta yi rashin nasara a hannun Arsenal da ci 2-0 a Amurka, sannan Minnesota United ta casa ta 4-0.

Asalin hoton, Reuters
Damben gasar matasa don lashe mota
Ranar Lahadi a gidan wwasa da ke Ado Bayero Square a Kano, Najeriya aka buga wasan karshe don lashe mota a damben matasa tsakanin Ramadan da Manu Shagon Garkuwa.
Ramadan daga Jamus da Manu Shagon Garkuwa Guramada sun yi turmi shida amma ba a samu gwani ba.
Karo na biyu kenan da suka dambata har yanzu ba a samu gwani ba, bayan da suka yi turmi takwas.
Tun farko Dogon Sisco daga Kudu ya doke Abba Shagon Roget daga Kudu.

Za a buga karawar daf da karshe a kwallon mata a gasar kofin nahiyar Turai
Za a buga karawar daf da karshe a gasar cin kofin nahiyar Turai a gasar mata
- Ingila da Sweden (Talata)
- Jamus da Faransa (Laraba)
