Chelsea ta fara Champions League da kafar hagu

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea mai rike da Champions League biyu ta fara wasan kakar bana da kafar hagu, bayan da Dinamo Zagreb ta doke ta 1-0 a wasan farko a cikin rukuni.
Kungiyar da ta lashe kofin gasar Croatia ba ta yin kokari a gasar Zakarun Turai, wadda ta ci wasa biyar daga 43 da ta fafata kafin fuskantar Chelsea ranar Talata.
Dinamo Zagreb ta ci kwallo a minti na 13 da fara tamaula ta hannun Mislav Orsic, wanda ya buga ta wuce mai tsaron raga Kepa Arrizabalaga.
Dinamo ta kusan kara na biyu ta hannun Stefan Ristovski, sai dai Arrizabalaga ya sa kwazo da kwallon bai shiga raga ba.
Sabon dan wasan da Chelsea ta saya a bana Pierre-Emerick Aubameyang ya fara yi mata wasa a Croatia, inda tsohon dan wasan Arsenal ya ci kwallo amma aka soke da cewar an yi satar gida.
Armando Broja ne ya maye gurbin Aubameyang, amma dai dan kasar Albania bai taka rawar da za ta bai wa Thomas Tuchel damar farke kwallon da aka ci ba.
Daf da za a tashi daga wasan Chelsea ta kai wani hari ta hannun mai tsaron baya Reece James, amma kwallon bai shiga raga ba.







