Hanyoyin da za ku gane ana so a damfare ku ta intanet

Wata mace tana danna wayarta

Asalin hoton, Getty Imges

    • Marubuci, Aisha Babangida
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 6

A zamaninmu na yau, intanet ta zama hanya mafi sauƙi da mutane ke amfani da ita wajen sadarwa da kasuwanci da samun bayanai.

Amma kamar yadda take da amfani, haka kuma ta zama cibiyar aikata laifuka ga mazambata.

Masu damfara ta intanet suna amfani da dabaru iri-iri wajen yaudarar mutane domin sace musu kuɗi ko bayanai masu muhimmanci.

Wannan matsala ta shafi kowa, daga matasa zuwa manya, musamman a ƙasashe masu tasowa kamar Najeriya da sauran ƙasashen Afirka, inda rahotanni suka nuna yadda dubban mutane ke rasa miliyoyin kuɗaɗe saboda damfara ta intanet.

Gano hanyoyin da ƴan damfara ke amfani da su na da wahala saboda tsananin dabararsu da hikima, kamar yadda Abdullahi Salihu Abubakar, mai bincike kan kafofi da hanyoyin sadarwa na zamani ya shaida wa BBC.

Yadda ƴan damfara ke aiki

Damfara

Asalin hoton, Getty Images

Abubakar ya ce ƴan damfara na amfani da hanyoyi da dama wajen jefa mutane cikin tarkonsu, ba ta intanet kaɗai ba.

Wasu daga cikin dabarunsu sun haɗa da:

  • Nazarin yanayin mutane: Kafin su tura saƙo ko su tunkari mutum, sukan yi nazari kan halayensa da abin da ya fi jan hankalinsa. Wannan yana taimaka musu wajen tsara dabaru masu tasiri.
  • La'akari da ɗabi'un mutane: Suna lura da ɗabi'un mutum domin su fahimci yadda za su ja hankalinsa cikin sauri da sauƙi.
  • Lura da abin da ya fi ɗaukar hankali: Suna bincika abubuwan da mutane suke yi a wani lokaci domin su tsara saƙo ko aiki da zai fi jan hankali.
  • Tsara dabaru domin jan hankalin mutane: Suna ƙirƙirar dabaru daban-daban domin mutane su saurare su, su bi sawu, ko su bayar da bayanai na sirri.
  • Aika saƙonni ta wayar salula: Ƴan damfara kan tura saƙonni tas kai-tsaye, ko su kira mutum da wasu lambobi da ba a saba gani ba kuma su yi iƙirarin cewa akwai matsala a bankinsa wadda ake buƙatar ya gaggauta bayar da bayanai domin gyarawa.
  • Amfani da manhajojin sadarwa da shafukan boge: Suna amfani da Facebook, WhatsApp, Instagram, TikTok da imel. Ta hanyar jan hankali da ake kira 'social engineering', suna nuna kamar sun san ka ko sun taɓa haɗuwa da kai domin su samu bayanai kamar lambobin waya, imel, ko bayanan sirri.
  • Bijiro da buƙatu na ƙarya: Suna amfani da labaran ƙarya kamar cewa kuɗin mutum sun maƙale, ko ana ɗaukar ma'aikata domin su ja hankalinsa ya bayar da bayanai ko kuɗi.
Damfara

Asalin hoton, Getty Images

Kutse a na'ura ko manhaja

Damfara

Asalin hoton, Getty Images

Masu aikata zambar kan aika saƙonni masu ɗauke da labarai daban-daban ga mabobin zauren da suka yi wa kutse, yayin da wasu kuma kan aika saƙon bai-ɗaya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Suna iya tura saƙonni masu haɗari domin samun damar shiga cikin na'urarka. A WhatsApp, sukan shiga zauren tattaunawa (group) ta hanyar yi wa ɗaya daga cikin jagororin zauren kutse.

Ta haka ne za su dinga ganin duk tattaunawar da ake yi a zauren, da mambobin cikinsa, sannan su zaɓi wasu daga ciki domin aika musu saƙon yaudara.

  • Buƙatar kuɗi da sunan matsala

Sau da yawa, saƙon nasu yana buƙatar kuɗi saboda "banki na da matsala" ko da sunan rance. Wannan hanyar tana matsa wa mutum ya aika kuɗi cikin hanzari.

  • Saƙonnin samun kuɗi cikin sauƙi

Galibin saƙonnin damfara na ɗauke da yaudara, suna nuna yadda za a samu kuɗi cikin sauƙi ba tare da shan wahala ba.

  • Sayen aikin gwamnati ko matsayi

Wasu masu damfara suna sayar da guraben aikin yi, musamman na gwamnati, inda mutane ke biyan kuɗaɗe masu yawa.

  • Amfani da shafukan boge wato (Phishing)

Wannan na nufin amfani da shafukan boge da suke kama da na asali. Misali, shafukan intanet na banki, ko kuma na sadarwa.

Hikimar yin hakan ita ce; idan mutum ya shigar da bayanan bankinsa da sauran kalmomin sirri masu shafin ne za su kwashe domin amfani da su a wani wuri da zimmar zambatarsa.

Mummunan tasirin Damfara

...

Asalin hoton, Getty Images

Mai binciken ya ce ba ƙaramin tasiri damfara ke yi wa waɗanda suka faɗa tarkon masu damfara ba wanda suka haɗa da:

  • Jefa mutum cikin ƙunci da tashin hankali, wanda zai iya kaiwa ga damuwa, ko hauka, ko ma kisan kai
  • Rage amincewa da saƙonni a tsakanin mutane
  • Rashin iya mu'amala cikin sauƙi
  • Tasiri ga tattalin arziki ta hanyar zuba jari na boge, ko sayen ayyukan gwamnati da ba a samu ba

Hanyoyin kare kai daga damfara ta intanet

...

Asalin hoton, Getty Images

Abubakar ya ce akwai hanyoyin da masu amfani da intanet da shafukan sada zumunta za su bi domin kare kan su daga mazambata.

  • Makullin mataki biyu (two-step verification)

Makulli mai mataki biyu da ake kira two-step verification hanya ce shafukan sada zumunta ke amfani da ita wajen bai wa masu amfani damar ƙara wa asusunsu tsaro.

Idan kuka saka ƙarin makullin, duk lokacin da wani ya yi ƙoƙarin yi muku kutse za a buƙaci ya saka lambobin sirrin da aka tura masa ta saƙon imel ko tes. Hakan zai tilasta masa ya haƙura saboda ku ne kaɗai za a turo wa lambobin, ba shi ba.

Kusan kowane dandali yanzu yana da wannan damar.

  • Ilimin amfani da shafuka

Mutum ya zama yana da ilimi kan yadda ake amfani da wayar salula da tsarin imel, da shafukan sada zumunta. Ilimin nan zai taimaka wajen gano saƙonnin da ba su da tushe da kuma guje wa shiga tarkon damfara.

  • Sanin 'netiquette'

Wannan yana nufin ɗabi'un mu'amala a kafofin sadarwa na zamani. Idan aka aika wa mutum saƙo daga wani wuri da bai sani ba, musamman idan saƙon yana ɗauke da wani adireshi, kada ku ziyarci shafin. Maimakon haka, kawai ku goge saƙon.

  • Tantance kiran waya daga wanda ba ku sani ba

Idan mutum ya kira ku ba tare da kun san shi ba, abu na farko shi ne ku yi ƙoƙarin wane ne shi da kuma inda ya samu lambarku. Wannan zai sa ko dai ya kashe wayar ko kuma ya sauya shawara saboda ba zai iya samun bayananka cikin sauƙi ba.

  • Guji saƙonnin samun kuɗi cikin sauƙi

Duk wani saƙo da ke ɗauke da alkawarin samun kuɗi cikin sauƙi na boge ne.

Ƴan damfara kan yi amfani da wannan hanyar domin jan hankalin mutum ya saka kuɗi da farko, daga nan sai su matsa ka kara zuba kuɗi saboda sun riga sun kama ka.

  • A guji saƙonni da hotuna ko adireshi masu tayar da sha'awa

Wasu saƙonni suna cewa idan kuka tura hotuna ko adireshi ga wasu, za ku samu kuɗi. Duk wannan ƙarya ne. Latsa adireshin ko hoton na iya ba su damar kutse cikin na'urarku, wanda zai ba su damar samun bayanan bankinku da sauran sirri.

  • Kariya daga shafukan bogi 'phishing'

Phishing na nufin amfani da shafukan boge da ke kama da na asali. Duk lokacin da aka turo muku adireshi ku tabbatar ya fito ne daga bankinku ko kuma kamfanoni na gaskiya. Akasari kamfanoni na gaskiya na da sanannen adireshi da suka saba turo saƙo, sannan kuma ba kasafai suke tambayar mutum ya saka lambobin sirrinsa ba.