Abin da ya sa Facebook ke rufe shafukan mutane

Asalin hoton, Getty Images
A ƴankwanakin nan masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi ta ganin wasu maganganu da ake ta yaɗa a shafukan sada zumunta, cewa shafin Facebook zai rufe duka shafuka masu alaƙa da suna ko saɓani a bayanan NIN.
Maganganun na zuwa ne ƴan kwanaki bayan shafin Instagram wanda mallakin Meta ne kamar Facebook ya goge wasu miliyoyin shafuka.
Haka ma a farkon watan Agusta kamfanin na Meta ya sanar cewa ya rufe shafukan manhajar WhatsApp miliyan 6.8 a faɗin duniya a watannin farko na 2025, waɗanda ake ganin suna da alaƙa da ayyukan zamba.
Da dama daga cikin shafukan da aka sauke na da alaƙa ne da gungun masu aikata ɓarna a Kudu maso gabashin nahiyar Asiya inda mutanen ke amfani da irin wannan shafuka wajen tilasta mutane harkar bauta.
Wata ƙwararriya a Birtaniya ta ce: "Masu amfani da shafukan Facebook, Instagram da WhatsApp na samun saƙonnin zamba babu ƙaƙƙautawa, abin da ya haɗa da tallace-tallacen zuba jari na bogi da na yaudara da kuma guraben ayyukan ƙarya."
A kan haka ne kamfanin Meta ya fara amfani da wata fasahar ƙirƙirarriyar basira (AI) wajen sauke miliyoyin shafukan da yake zargi da ayyukan rashin gaskiya a facebook da Instagram.
Meta ya shaida wa BBC cewa yana amfani da fasahar zamani da kuma mutane wajen ganowa da kuma sauke shafukan da suka saɓa wa ƙa'idojinsa.
Za a iya rufe shafin facebook saboda suna?
E, haka ne.
Facebook ana buƙatar mutane su yi amfani da sunan da suke amfani da shi a zahirin rayuwa.
Idan aka gano cewa mutum yana amfani da sunan karya ko na wani, ana iya dakatar da ko rufe shafinsa.
Wannan yana cikin dokarsu don kare mutane daga zamba, da damfara, da rashin gaskiya.
Yawancin shafukan da akan rufe sanadiyyar amfani da suna na daban na faɗawa ne cikin waɗanda Facebook ke kallo a matsayin shafukan bogi.
Dalilin da ke sa Facebook ya rufe shafin mutum
Facebook na iya rufe shafi saboda dalilai kamar:
- Amfani da sunan karya, wato sunan wani kenan.
- Sanya hotuna ko rubuce-rubuce masu dauke da cin mutunci, ko batsa, ko nuna ƙiyayya.
- Yawan aika friend requests ga mutanen da akwai ƙarancin alaƙa tsakanin ka dasu.
- Hawa shafinka daga wurare daban-daban cikin lokaci ɗaya (misali daga Abuja, sai ga ka sake hawa a birnin Tokyo na Kasar Japan, cikin kasa da minti guda).
- Yawan amfani da kalmomi ko comments iri ɗaya a wurare da yawa. Wannan kan sa ayi zaton kana aika saƙonnin kasuwanci ne ko na bogi (spam), wanda hakan ya saɓa wa ƙa'ida.
Ta yaya mutum zai kare shafinsa?
Ga wasu matakai da za ka iya bi:
- Yi amfani da sunanka na gaskiya.
- Guji yawan aika 'friend request' ba tare da alaƙa tsakaninka da waɗanda kake aika wa ba.
- Kada ka ɗora abun da ke ɗauke da cin mutunci, ko batsa, ko nuna ƙiyayya.
- Ka yawaita amfani da shafin ka ta hanyar ɗora bayanai masu ma'ana da nuna kyakkyawar mu'amala tsakaninka da abokanka.
- Ka yawaita karantawa da kuma bin dokokin Facebook da ake sabuntawa yau da kullum.
Facebook na rufe shafuka bisa kuskure?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kamfanin Meta ya sha suka daga dubban masu amfani da shi kan saukewa ko dakatar da shafukan facebook masu ɗimbin yawa a Facebook da Instagram ba bisa ƙa'ida ba.
Lamarin ya kai ga gabatar da wani ƙorafi da aka yi wa taken "Meta na kuskuren rufe shafuka ta hanyar na'ura ba tare da kulawar wani ɗan'adam ba", inda mutane suka riƙa nuna goyon baya kan ƙorafin a shafin change.org.
Mutane da dama sun bayyana yadda suka rasa shafukansu na kasuwanci ko kuma ƙungiyoyi.
Akwai zarge-zargen cewa Meta ya rufe sauke shafukan wasu mutanen bisa zargin su da karya dokokinsa na lalata da ƙananan yara.
Masu amfani da facebook da dama sun soki yadda Meta ke amfani da ƙirkirarriyar basirar AI wajen yanke hukunci kan irin wadannan shafuka, inda suka ce babu wata hanya da mutum zai iya tuntuɓar wani bil'adama idan aka rufe shafinsa.
BBC dai ba ta tantance gaskiyar waɗannan zarge-zarge ba.
A cikin wata sanarwa, kamfanin Meta ya ce: "Muna ɗaukar matakai ne kan shafukan da suka karya ƙa'idojinmu, amma mutum zai iya yin ƙorafi idan ya ga kamar mun yi kuskure.
Kamfanin ya ce yana amfani da mutane da kuma fasahar zamani wajen ganowa da sauke shafukan da suka saɓa ƙa'idojinsa, kuma ba ya da wata masaniya kan ƙaruwar kuskuren rufe shafuka.
Ba kamfanin Meta kawai ba - wanda shi ne mamallakin shafin facebook da instagram da kuma WhatsApp - kamfanonin sada zumunta da dama na ɗaukar matakan rage yaɗuwar labaran ƙarya da kuma damfara ta intanet.
Sabbin sauye-sauye Facebook
Ga wasu daga cikin sauye-sauyen da suka bayyana cikin ƴan kwanakin nan:
- Duk bidiyon da aka ɗora yanzu ana maida shi Reels.
- Ana iya amfani da fuska, da tambarin yatsa ko PIN don shiga Facebook.
- Facebook Messenger na ba da damar ƙirƙirar stickers da amfani da AI a cikin group chats.
- Facebook na rage yawan nuna bayanan da suka fi kama da hira ko masu ƙarancin kima wajen tallata hajoji ko kasuwanci. A takaice dai, suna bai wa bayanan ƙwararrun da ke samar da bayanan kasuwanci da tallace tallace (Creators) mahimmanci.
- Ana samar da sabbin fasali don sauƙaƙa amfani da manhajojin dake shafukan masu tallace tallace.











