Me zai faru da shafukan sada zumuntarmu idan mun mutu?

Lokacin da wani makusancinsu ya rasu, mutane kan yi kewar tattaunawa, da shaƙuwa da runguma da kuma ganin da suke wa juna, amma yayin da aka samu bunƙasar shafukan sada zumunta, wannan kewa da ake fuskanta bayan mutuwar makusanci ta faɗaɗa zuwa shafukan sada zumunta.
Shafukan waɗanda suka mutu kan ɓace bayan mutuwarsu, ko kuma su ci gaba da kasancewa a matsayin tunatarwa game da rayuwarsu, to sai dai ɗaukar mataki game da makomar shafukan na hannun makusanta mamatan.
"Ina tunanin dangane da wasiyyar mahaifiyata bayan mutuwarta, mafi yawanmu mun kasance masu son tunawa da rayuwarta, don haka har yanzu kusan shekara huɗu bayan mutuwarta, mun kasa aiwatar da wasiyarta na rufe shafinta bayan ta mutu,'' kamar yadda Katarina Milošević, wata ƙwararriyar kan harkokin yawon buɗe ido daga Belgrade ta shaida wa BBC.
Akwai kuma masu ra'ayin cewa barin shafukan waɗanda suka mutu don tunawa da su ba shi ne mafita ba, don haka suna da ra'ayin a rufe shafukansu bayan mutuwarsu, ɗaya daga cikin masu irin wannan ra'ayi ita ce Jelena Šain, wadda ke amfani da shafin Facebook tun 2008.
"Ba zan yi amfani da shafin wani bayan mutuwarsa ba, haka kuma ni ma ba zan so wani ya yi hakan don tunawa da ni ba."
"Ba daidai ba ne wani ya ga hirarrakin da wani ya yi ba saboda kiyaye sirrinsa, kuma ba za ka ji daɗi ba idan ka fahimci cewa a cikin abokanka na shafukan sada zumunta har da matattu" in ji wani masanin zane-zane daga Pancevo.
Shafin Data Report ya ce kusan mutum biliyan biyar ne a faɗin duniya ke amfani da shafukan sada zumunta a rubu'i na uku na shekarar 2023, kusan kashi 61.4 cikin 100 na al'ummar duniya.
Shafin ya ƙara da cewa kusan dukkanin masu amfani da intanet suna amfani da shafukan sada zumunta.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani bincike da aka danganta da jami'ar Oxford da aka wallafa a mujallar Time, ya nuna cewa a farkon ƙarnin da ke tafe, adadin masu amfani da shafukan waɗanda suka mutu zai zarta masu amfani da shafukan, kuma hakan zai faru ne kawai idan shafin Facebook bai ƙara samun masu amfani da shi ba.
Wasu alƙaluma daga kamfanin 'An extra' mai lura da masu amfani da shafukan sada zumunta ya ce Facebook ne shafin sada zumunta mafi shahara, inda shafin ke da masu amfani da shi biliyan 3.03, sai kuma shafin Youtube ke bi masa wanda ke da masu amfani da shi biliyan 2.49, shafukan Vocap da Instagram kuwa kowannesu na da mutum biliyan biyu da ke amfani da shi, daga nan sai shafin WeChat mai mutum biliyan 1.33, sai Tiktok mai biliyan 1.22
Shafukan Facebook da na Instagram na bayar da dama a mayar da shafin wanda ya mutu zuwa shafin da zai riƙa tunatar da mutane mamaci, don haka zai iya ci gaba da kasancewa ko kuma a rufe shi in ana buƙata.
Shi kuwa shafin X da a baya aka fi sani da Twitter, ba ya bayar da damar ci gaba da ajiye shafin wani a matsayin na tunarwar, don haka za a iya goge shafi idan mai amfani da shi ya mutu ko ba ya buƙatar ci gaba da amfani da shi.
Ana amfani da shafukan waɗanda suka mutu ba ta yadda ya dace ba kamar yadda Saša Živanović, tsohuwar shugabar sashen kula da masu aikata laifukan intanet a ma'aikatar cikin gida ta Sabiya ta bayyana.
"Akan yi amfani da hotuna da bayanai da bidiyoyi domin ƙirƙirar shafukan ƙarya da sunaye daban-daban, domin samun kuɗi daga abokai da masoyan mutumin, waɗanda ba su da labarin mutuwarsa,'' in ji Živanović.
Me ake nufi da shafin tunawa da mamaci?
A lokacin da Milosevic ta yi ƙoarin mayar da shafin mahaifiyarta zuwa shafin tunawa da ita ta fuskanci matsala.
"Facebook ya buƙaci da ta aika masa da takardar shaidar mutuwa, amma ba ni da ita a lokacin, a duk lokacin da na fara yin sa, ba na iya wuce wurin saboda dole sai na cike wajen kafin ci gaba,'' in ji matashiyar mai shekara 31.
"Yanzu an kusa shekara huɗu tun da ta rasu, kuma har yanzu shafin na nan,'' in ji ta.
Shafin Facebook ya ce a duk lokacin da aka tabbatar masa da mutuwar wani mai amfani da shafin, to nan take zai mayar da shi shafin tunawa da mamaci, har sai idan daga baya an nuna rashin buƙatar hakan.
Abubuwan da aka wallafa a shafin za su ci gaba da kasancewa a shafin kuma za a iya ganinsu, to sai dai shafin ba zai riƙa bayyana bangaren tayin sabbin abokai ba, (People You May Know), kuma ba za a riƙa sanar da abokansa game da zagayowar ranar haihuwarsa ba.
A kusa da sunan mai shafin rubutun ‘memory’, wato ‘tunawa’ zai bayyana, kuma babu wanda zai iya shiga shafin domin mayar da shi shafin tunawa da mamaci, sai idan ainhinin mai shafin ya taɓa bayyana sunan wanda zai gaji shafin nasa, (legacy contact).
'Legacy contact', wani mai amfani da shafin ne, wanda yawanci ɗan’uwa ko aboki ne ga mamaci, wanda zai iya sauya hoton bayan shafin wato 'cover photos', sannan kuma zai iya wallafa saƙon karshe a shafin, ko ya buƙaci a dakatar da shafin.
Haka kuma za a ba shi damar samun bayanai, ko ya goge ko kuma ya ƙara abokai.
Shin matasa za su iya ɗauke kansu daga shafukan sada zumunta?
Makomar shafukan sada zumunta sun bambanta dangane da fasahohin da muke amfani da su.
Hanyoyin samun bayanan mamaci sun bambanta, kuma kamfanonin fasahar suna bai wa sirrin mamaci muhimmaci - ba za aika cikakkun bayananai, ko wasu bayanansa ba, kamar hotuna da bidiyo, za a iya samunsu ne kawai ta hanyar aika buƙata ta musamman, a wasu lokuta ba ta hanyar umarnin kotu.
Sai dai shafukan sada zumunta na baya-bayan nan kamar TikTok da Snapchart, ba su da wasu dokoki kan shafukan waɗanda suka mutu.
Shafukan za su ci gaba da kasancewa har sai wani ɗan'uwansa na sanar da kamfanin game da rasuwar mai shafin, sannan ya buƙaci a dakatar da shafin.
Amma shafukan Facebook da Instagram na mayar da shafukan na tuna wa da mamatan wato "memorialization".
Za ku iya goge shafukan waɗanda suka mutu, da bayanansu a shafukan, idan kuka tabbatar da cewa ku makusantansu ne.
Kamfanin Google, mai shafin YouTube da G-mail, zai aiwatar da irin wannan hanya, sai dai idan mai amfani da shafin ya canza saitin da ake kira "inactive account"
Waɗannan saitunan suna za su ba ku damar ɗaukar mataki kan abin da zai faru da shafinku na Google da bayananku muddin ba ku yi amfani da shafin ba na tsawon wani lokaci.
Hakanan za ka iya zaɓar wanda zai kula da waɗannan shafuka kuma ka bar musu wasiyar da za su karanta idan ka mutu.
Jelena Šain tana amfani da shafukan Facebook da Instagram don wallafa hotuna, d aike wa da waƙoƙi da bayanai ga abokanta, kuma ta aike da dubban hotuna da waƙoƙi da bayanai ga abokanta tun lokacin da ta fara amfani da waɗannan shafuka.
Duk da cewa ba lallai ne ta yanke shawara kan abin da zai faru da shafukan sada zumunta na makusantanta ba, tana tunanin abin da za ta yi a wannan yanayin.
Kamar yadda ta ce, ta ji cewa akwai damar ƙirƙirar asusun tunawa da mamaci, amma wannan ba shi ne zaɓinta ba.
"Ni ba mai sha'awar irin waɗannan bayanan ba ne, kuma ina son aboki ko dangina, idan sun tabbatar na mutu, su rufe shafina nan take," in ji Shain.
Hakan zai kawar da “cin zarafi ko amfani da shafi ta hanyar da ba ta dace ba”, saboda babu daɗi ka ga an wallafa wani saƙo daga shafin wani mutum da ka san cewa ya mutu, in ji ta.

Ta yaya doka ke lura da gadon shafukan sada zumunta?
Wani bincike da jami'ar Oxford ta gudanar a shekarar 2019, ya yi hasashen cewa zuwa shekarar 2100 masu amfani da shafin Facebook da suka mutu zai kai biliyan 4.9.
Duk da cewa wannan adadin ka iya ƙaruwa, saboda ba doka ce ta tanadi a sanar da shafukan mutuwar masu amfani da shafin ba.
"An ɗaukar shafukan sada zumunta a matsayin wani abu na gado da ba a iya gani, don haka ba kowa ne iya yi ba.''
Dokokin Sabiya ba su amince da irin wannan gado na shafukan sada zumunta ba, saboda sannu a hankali ake shigar da abubuwan gargajiya cikin dokokin ƙasar, in ji Duško Majkić, wani lauya a BBC Sabiya.
"Ba a ɗaukar shafin sada zumunta a matsayin wani abu da ke da haƙƙin mallaka ko aikin wani marubuci , amma yana iya zama wani abu da za a iya aikawa, irin su wani ra'ayi ko rubutu ko kuma hoto," in ji wani lauya a ofishin lauyoyi na Živko Mijatović da Abokan Hulɗa.
To amma ya ce, bai ga wata matsala da hakan ba, baya ga kadarorin da za a iya motsawa da waɗanda ba a iya motsa su, magada kan iya gadar shafukan Facebook ko Instagram ta hanyar wasiyya.
Majkić ya ce "Lokacin rubuta wasiyya, ana amfani da wata ƙa'ida wadda ke nufin cewa za ku iya yin duk abin da kuke so da haƙƙoƙinku da dukiyoyinku, matukar al'adarku ba ta hana ku yin hakan ba''.
Ta hanyar amfani da shafukan wasu, kamar shafukan waɗanda suka mutu, ba za a ɗora alhakin ainihin masu shafukan kan aikata wani baban laifi ba kamar yadda dokoki suka nuna, in ji wani lauya da ya ƙware kan batutuwan haƙƙin mallaka.
"To sai dai haka, zai iya haifar da cin zarafi da aikata miyagun laifuka: wallafa saƙonni daga waɗannan shafuka zai iya zama zamba, da haifar da haɗari ko firgita," in ji Majkic.
Amfani da shafin mamaci ta hanyar da ba ta dace ba
Saboda bayanan masu amfani da shafukan waɗanda suka mutu, akan samu matsalar amfani da bayanai kamar hotuna da sauran abubuwan mai asalin shafin ta hanyar da ba ta dace ba.
Ana iya yin hakan ta hanyar sauke bayanai, hotuna da bidiyo saboda babu wanda ke kula da shafin, in ji Saša Živanović.
“Yawanci suna neman wasu makusantan marigayin, wadanda watakila ba su san mutuwarsa ba, inda suke tambayar su kuɗi bisa hujjar cewa wata hasara ta sme su, ko kuma sun tsinci kansu a cikin tsaka mai wuya. " in ji tsohon shugaban sashen manyan laifukan da suka shafi fasaha a ma'aikatar cikin gida ta Sabiya .
Irin wannan nau'i na zamba ya zama ruwan dare a shafukan sada zumunta a Sabiya.
Duk da cewa, yawancin nau'o'in cin zarafi ba su da yawa kuma suna da wahala a aiwatar da umarnin marigayan, saboda rukunin abokansa sun san cewa wannan mutumin ba ya raye kuma ba za su faɗa hannun mazambata cikin sauki ba, in ji Živanović.
Katarina Milošević ba ta fargabar cin zarafi, amma ba ta so ta bar shafin mahaifiyarta ya ci gaba da aiki.
"Na yi imanin nan ba da jimawa ba zan rufe shi gaba ɗaya, ko na mayar da shi shafin tunawa d mamaci''.
“Akwai kyawawan abubuwa da yawa a shafin da zan so in tuna kuma za su saka ni farin ciki da jin daɗi,” in ji matashiyar.











