Abubuwa huɗu da suka kamata ku sani kafin fara amfani da Meta AI da ChatGPT

- Marubuci, Rebecca Thorn
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC 100 Women
- Lokacin karatu: Minti 5
Takan taya ku yin lissafi. Za ta iya amsa tambayoyi na jarrabawar neman aiki. Za ta iya zama ma abokiyar neman shawara. Ƙirƙirarriyar Basira ta Artificial intelligence (AI) na ƙoƙarin zama komai da ruwanka.
Fasahar na haɓaka cikin gaggawa, yayin da kamfanoni ke rige-rigen wuce juna ta hanyar fitar da sababbin tsare-tsare masu kaifin basira.
ChatGPT na ɗaya daga cikin mafiya haɓaka a tarihi. Manhajar ta samu masu amfani da ita miliyan ɗaya kwana biyar kacal da ƙaddamar da ita, sun kai miliyan 100 bayan wata biyu, kamar yadda rahoton cibiyar International AI Safety Report ya bayyana wanda ƙasashe 30 mambobin Tarayar Turai, da Majalisar Ɗinkin Duniya, da OECD ta haɗakar tattalin arziki suka fitar.
Kamfanin Microsoft, wanda ya kafa manhajar Co-Pilot a 2023, ya ce yana sa ran samun kuɗi daga kamfanonin kasuwanci da ke amfani da AI da za su zarta dala biliyan 10 nan da tsakiyar 2025, har ya faɗaɗa tashoshin ajiyar bayanansa zuwa 60 a fadin duniya.
Shi kuma AI Overviews na Goggle, wanda ke bayar da taƙaitattun bayanai na abubuwan da aka nemi ƙarin sani a kansu, yana da masu amfani da shi biliyan 1.5 duk wata a ƙasashe sama da 200, kamar yadda shugaban kamfanin Alphabet Sunder Pichai ya bayyana.
Ƙwararru na cewa fasahar ta zo kenan, saboda haka ne muka tambayi ɗaya daga cikinsu ta yaya mutum zai yi kyakkyawan amfani da ita.
Sasha Luccioni 'yar Canada ce ƙwararriya a fannin muhalli da ke aiki da cibiyar Hugging Face, wani kamfani da ke son sauƙaƙa hanyoyin da mutane ke amfani da AI.
"Ina kallon AI a matsayin wata hanyar ɗaukakawa - na abubuwan da suka dace da waɗanda ba su dace ba - amma dai akwai buƙatar mu saka ido," kamar yadda ta shaida wa Shirin BBC na Mata 100.
Ga wasu tambayoyi huɗu da ta bayar da shawarar mutum ya tambayi kansa kafin fara amfani da Ƙirƙirarriyar Basira ta AI.
1. Shin wannan ce fasahar AI da ka fi buƙata?

Asalin hoton, Getty Images
Manhajojin AI na iya yin abubuwa daban-daban, a cewar Lucconi.
"Wani zubin mukan nemi amfani da mafi shahara a cikin manhajojin AI saboda su muka sani kuma suna iya yin abubuwa da yawa. Amma kuma akwai waɗanda aka tsara domin su yi wani aiki na musamman - kamar amsa tambayoyin kimiyya."
Akwai manhajoji da dama da ake ƙaddamarwa, waɗanda suke iya yin wasu abubuwa na musamman - manya da ƙanana.
Wata manhaja daga cikinsu kan bai wa mutane damar ɗaukar hoton darasinsu na lissafi, ita kuma ta amsa tambayoyin. Wata kuma takan harhaɗo wa mutum jerin addu'o'in da zai yi daga litattafai da yawa.
A cewar wani rahoto kan AI a 2025 daga Jami'ar Stanford, jami'ar ta ƙirƙiri fasahohin AI 40 a sekarar da ta gabata, idan aka kwatanta da na China 15, da kuma na Turai uku.
Ku san manhajojin da ake da su tukunna kafin ku zaɓi wadda za ku yi amfani da ita.
2. Za ku iya aminta da amsoshin AI?
AI za ta iya ba ku amsa, amma ba lallai ta zama daidai ba ko kuma ma gaskiya, in ji Luccioni.
"Fasahohin AI za su iya ƙirƙirar abubuwan da babu su kawai saboda sun yi kama da gaskiya. Hakan zai iya haifar da matsala idan ya yi amfani da shi a wajen aiki ko kuma makaranta," kamar yadda ta bayyana.
Domin guje wa hakan, ta bayar da shawarar kodayaushe a dinga tsettsefe amsoshin da manhajojin suka bayar.
"Ku sake karantawa a tsanake kuma ku yi nazari kan abin da suke faɗa. AI na da ƙwarin gwiwa a maganganunta, amma duk da haka ya zama kuskure."
3. Me nake faɗa wa AI ɗin?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Luccioni ta ce ya kamata masu amfai da AI su dinga tunani game da bayanan da suke bai wa manhajojin kamar yadda suke yi kan bayan da suke samu daga gare su.
Tsarin AI na aiki ne ta hanyar kwaso bayanai masu yawa kuma ta yi amfani da shi domin horar da kan ta. Hakan na nufin, bayanan da kuka zuba mata, kamar hoto ko rubutu, za ta iya riƙe su, ta nazarce su domin yin amfani da su a amsar da za ta ba ku nan gaba.
Kowace manhaja na da tsarin ajiye bayananta, saboda ku duba ƙa'idojin kafin ku yi amfani da ita.
"Idan bayanan na ƙashin-kai ne ko kuma na jin kunya, kada ku saka shi a manhajar saboda zai iya ɓulla a internet," a cewar Luccioni.
Ta bayar da misali da manhajar Meta AI, inda mutane ba su sani ba cewa tambayoyin da suke yi wa manhajar ana wallafa su a wani wuri da kowa ke iya gani da ake kira 'Discover'.
BBC ta gano misalai na mutanen da ke wallafa hotunan tambayoyin jarrabawarsu na makaranta, da masu neman a ba su hotunan tsiraici, da masu neman shawara kan jinsinsu.
A 2023 Italiya ta zama ƙasar Turai ta farko da ta hana amfani da ChatGPT saboda fargabar tsare bayanan sirri.
Koriya ta Kudu, da Australia, da Amurka ma sun nuna damuwa kan yadda DeepSeek, wanda mallakar China ne, ke ajiyewa da kuma amfani da bayanan sirrin mutane.
4. Da gaske ina buƙatar amfani da AI?

Asalin hoton, Getty Images
Ku yi amfani da AI a matsayin abin aiki, ba wai a madadin ƙwaƙwalwarku, a cewa Luccioni.
Ku duba tukunna kan ko za ku iya yin aikin da kanku, ko kuma ta hanyar amfani da wasu kayan aikin daban, kamar kwakuleta wajen warware wata matsalar lissafi.
Ta kuma bayar da shawarar yin amfani da basirar wasu mutanen da muke zaune tare da su domin taimaka mana da wasu amsoshin.
"AI ba za ta iya ɗaukar wani mataki ba game da abin da ya dace a rayuwar ɗan'adam da wanda bai dace ba a wani yanayi na musamman, kuma da ma bai kamata mu ƙyale ta ta dinga faɗa mana abin da ya dace mu yi ba a rayuwarmu," kamar yadda ta ce.
Haka nan, manhajojin AI na amfani da makamashi mai yawa fiye da sauran na'urorin matambayi ba ya ɓata da aka saba.
Tashoshin ajiyar bayanai na AI da ake da su a fadin duniya na buƙatar ruwa mai yawa sosai domin sanyaya nau'rorin, abin da ka iya jawo ƙarancin ruwan ko hanyoyin rarraba su.
"Manhajojin AI ba su zo don su koma ba - musamman ma saboda yadda muke ƙara dogara da intanet da kuma shafukan sada zumunta," in ji Luccioni.
"Amma hakan ba shi nufin mu dinga yin amfani da AI a kan komai na rayuwarmu, wanda zai iya jawo mana rasa wani muhimmin ɓangare na mutuntakarmu - basira, da zamantakewa, da maƙwabtaka.










