Ana fargaba a duniya kan yiwuwar fadowar kumbon da China ta harba sararin samaniya

The rocket lifting off from southern China on July 24, 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar 24 ga watan Yulin 2022 ne China ta harba kumbon nata daga kudancin ƙasar zuwa sararin samaniya

Ana sa ran tarkacen kumbon da China ta harba sararin samaniya zai faɗo duniyarmu ta Earth a ƙarshen makon nan.

Sai dai barazanar yiwuwar faɗawarsa yanki mai cike da jama'a ba ta da yawa.

Amma hakan ya sanya tambayoyi a kan yadda kowace ƙasa za ta kwashi rabonta na tarkacen kumbon.

A baya Nasa ta sha kiraye-kiraye kan hukumar sararin samaniyar China, cewa ta tsara kumbunanta ta hanyar ɓangarorinsa su kasance ƙanana a yayin kutsawa samaniyar, saboda haka tsarin ƙasa da ƙasa yake.

Kumbunan China da a baya-bayan nan ake harba su tasharta da ke sararin samaniya wacce ba a kammala ta ba mai suna Tiangong, ba sa iya kutsawa saman yadda ya kamata.

A ranar Lahadi ne ta sake harba kumbon na bayan nan, mai suna Long March 5, ɗauke da ɗakin gwaje-gwaje zuwa tashar Tiangong.

A ranar Laraba gwamnatin China ta ce harba kumbon ba zai zama barazana ga mutanen da ke doron duniya ba saboda ga dukkan alamu a teku zai faɗa.

Kazalika, akwai yiwuwar tarkacen kumbon za su iya faɗowa ƙasa a yankin da ke cike da jama'a, kamar yadda ya faru a watan Mayun 2020 lokacin da tarkacen ya faɗa kan wasu ƙadarori a ƙasar Ivory Coast har suka lalace.

A yanzu haka dai kumbon wanda babu komai a cikinsa yana ta zagaye a saman duniya inda ake jawo shi don ya faɗo doron duniyar.

Wata hukumar kula da sararin samaniya mai zaman kanta ta Aerospace Corporation, da ke da cibiya a California, ta ce zai faɗo duniyar ne da misalin ƙarfe 12.24 na dare agogon GMT ranar Lahadi,

Ya yi wuri a san inda tarkacen mai yawan ton 25 zai faɗa.

Akwai yiwuwar tarkacen ka iya faɗa wa wasu yankuna a Amurka ko Afirka ko Australiya ko Brazil ko Indiya ko Kudu maso gabashin Asiya, a cewar hasashen hukumar.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X

Wani ƙwararre mazaunin Birtaniya da ke bin diddigin abubuwan da ke yawo a sararin samaniya, kuma daraktan hukumar Tsaron Arewacin Samaniya, Sean Goldsbrough, ya shaida wa BBC cewa, "Ba a san ainihin inda kumbon Long March 5 zai faɗa ba.

"Kuma irin hakan ce ta yi ta faruwa a baya da aka harba shi."

"Rashin sadarwa, da kuma rashin sanin abin da zai faru a gwaje-gwajen baya da aka yi, shi ne abin da ya kawo fargabar.," in ji shi.

Yawanci hukumomin sararin samaniya kan tsara ɓangarorin kumbunonsu ne a ƙanana saboda gudun faɗowar, tun bayan da wani kumbon Amurka ya faɗo Australiya daga sararin samaniya a shekarar 1979.

Ko a bara da irin hakan ta faru, wani babban jami'in Nasa Bill Nelson, ya ce "ga alama China ba ta bin dokokin da suka dace na aika kumbo sararin samaniya."

Ya ce dole ƙasashe su taƙaita barazanar illata mutane da ƙadarori a duniya daga ɓarnar da tarkacen kumbunan da aka harba samaniya za su iya jawowa.

Bayanan bidiyo, Ƴan sama jannatin Rasha da Amurka sun ce lafiya lau suke zaune a sararin samaniya

Sau biyu kenan an harba kumbon Long March 5, ɗaya a watan Mayun 2020 ɗayan kuma watan Mayun 2021, inda suka ɗauki kaya daban-daban zuwa tashar Tiangong.

Sai dai kuma sau biyun duka yana rikitowa ya faɗo duniya, a ƙasar Ivory Coast da kuma Tekun Indiya.

Waɗannan duk sun biyo bayan wani gwaji da aka taɓa yi da ya faɗo Tekun Fasifik ne a shekarar 2018.

Sai dai ba a taɓa samun wanda ya ji rauni ba amma dai lamurran sun jawo suka da Allah-wadai daga hukumomin sararin samaniya da dama.

A ranar Talata, wata jaridar gwamnatin China mai suna Global Times, ta zargi kafafen yaɗa labaran ƙasashen yamma da taya Amurka yayata farfaganda kan kumbon Long March 5.

A watan Afrilun 2021 ne China ta fara tsara tasharta ta sararin samaniya, kuma tana sa ran kammalawa zuwa ƙarshen 2022.