Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hotunan firaiministocin Birtaniya 16 da Sarauniya Elizabeth ta nada a tarihi
Sarauniya ta soma nada firaiministoci ne a 1955 lokacin da ta nada Anthony Eden, amma Liz Truss firaiminista ta farko da aka gayyata zuwa Scotland.
A wani mataki na saba wa al'ada, sabuwar firaiministar ba ta gana da Sarauniya a fadarta ta Buckingham da ke London ba. Maimakon hakan, basarakiyar ta gana da sabuwar firaiminista a Balmoral.
Sarauniyar ta hau karagar mulki ne a 1952, lokacin da Winston Churchill ya zama firaminista. Ga wasu hotunanta tare da firaiministoci 16 da ta nada a shekara 70 da ta kwashe tana mulki.