Bayanan hoto, Tun shekarar 1955 Sarauniya take nada firaiministoci
Sarauniya ta soma nada firaiministoci ne a 1955 lokacin da ta nada Anthony Eden, amma Liz Truss firaiminista ta farko da aka gayyata zuwa Scotland.
A wani mataki na saba wa al'ada, sabuwar firaiministar ba ta gana da Sarauniya a fadarta ta Buckingham da ke London ba. Maimakon hakan, basarakiyar ta gana da sabuwar firaiminista a Balmoral.
Sarauniyar ta hau karagar mulki ne a 1952, lokacin da Winston Churchill ya zama firaminista. Ga wasu hotunanta tare da firaiministoci 16 da ta nada a shekara 70 da ta kwashe tana mulki.
Winston Churchill 1951 - 1955
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Sarauniya tare da Yarima Charles da Gimbiya Anne, ta gana da Sir Winston Churchill a1953
Anthony Eden 1955 - 1957
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Sarauniya ta gaisa da Sir Anthony Eden a 1956
Harold Macmillan 1957- 1963
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Harold Macmillan, wanda aka nada a matsayin uban Jami'ar Oxford, ya yi wa Sarauniya maraba da zuwa Jami'ar a 1960
Alec Douglas-Home 1963 - 1964
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Sarauniya tana magana da Sir Alec Douglas-Home da Lady Home lokacin wata liyafa a dakin Couty Hall a 1964
Harold Wilson 1964 - 1970
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Harold Wilson tare da Sarauniya a 1969
Edward Heath 1970 - 1974
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Sarauniya tare da Edward Heath, Richard Nixon da kuma Pat Nixon a Chequers a shekarar 1970
Harold Wilson 1974 - 1976
Asalin hoton, Alamy
Bayanan hoto, Harold Wilson ya yi wa Sarauniya maraba da zuwa fadar 10 Downing Street a 1976
James Callaghan 1976 - 1979
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, James Callaghan ya gana da Sarauniya don cin abincin rana a fadar Windsor Castle a 1977
Margaret Thatcher 1979 - 1990
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Sarauniya tare da Margaret Thatcher da Ronald Reagan a fadar Buckingham Palace a 1984
John Major 1990 - 1997
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Sarauniya tare da John Major, na uku daga hagu, da tsofaffin firaiministoci Margaret Thatcher, Harold Wilson, Edward Heath da kuma James Callaghan a 1992
Tony Blair 1997 - 2007
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Sarauniya yayin da aka dauke ta a hoto tare da Tony Blair a fadar Buckingham a yayin da ta gayyace shi ya kafa gwamnati a 2002
Gordon Brown 2007 - 2010
Asalin hoton, Alamy
Bayanan hoto, Gordon Brown ya gana da Sarauniya a 2007
David Cameron 2010 - 2016
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, David Cameron a Fadar Buckingham Palace a shekarar 2010 a yayin da Sarauniya ta gayyace shi domin ya kafa gwamnati
Theresa May 2016 - 2019
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Theresa May ta ziyarci Fadar Buckingham a yayin da ta zama firaiminista a 2016
Boris Johnson 2019 - 2022
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Boris Johnson ya ziyarci Buckingham Palace a 2019 domin maye gurbin Theresa May
Liz Truss a 2022 zuwa nan gaba
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Liz Truss ta zama firaiminista ta 15 da Sarauniya ta nada a yayin da ta karbi mulki daga wurin Boris Johnson