'Hare-haren Isra'ila sun mayar da Beirut fagen daga'

Hari a Beirut
Lokacin karatu: Minti 3

Wakiliyar BBC a Gabas ta Tsakiya Nafiseh Kohnavard, wadda take babban birnin Lebanon ta ce yanayin hare-haren da Isra'ila ke kaiwa a yanzu sun mayar da birnin tamkar filin daga.

Ta ce a daren da ya gabata na Juma'a birnin ya sha luguden manyan bama-bamai, wani bayan wani, inda ta ce ta ƙirga hare-hare ta sama har 12 a kudancin wajen birnin.

Wakiliyar ta ce dare da rana jiragen sama marassa matuƙa na leken asiri na Isra'ila na ta shawagi a birnin - sai kararsu ake ta ji kawai har ma ta zama jiki.

Sassa daban-daban na birnin na cike da tantuna na 'yan gudun hijira.

Isra’ila ta ƙara yi wa babban birnin Lebanon, Beirut ruwan bama-bamai inda aka rika ganin wuta da hayaki na tashi cikin dare, a yankunan da Hezbollah ta mamaye.

Ita kuma ƙungiyar ta Hezbollah na cewa mayaƙanta na mummunan ɗauki-ba-daɗi da sojin Isra’ilar a yankin iyakar kudancin kasar ta Lebanon.

Ƙungiyar ta ce dakarun na Isra’ila na ƙoƙarin kutsawa zuwa garin Adaysshe ne da ke, kudu.

Ana ganin Isra'ilar na son kama iko da yankin ne tare da kawar da 'yan Hezbollah daga yankin saboda galibi daga nan ƙungiyar ke ruwan makaman roka zuwa arewacin Isra'ila.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kafofin yaɗa labaran Falasdinu sun ruwaito cewa jagoran ɓangaren mayaƙan Hamas Saeed Atallah, ya rasu tare da wasu mutum uku daga cikin iyalansa a hare-haren.

Rundunar sojin Isra'ila tana da ƙwarin gwiwa cewa ta hallaka mutumin da take ganin shi ne zai gaji shugaban Hezbollah da ta kashe Hassan Nasrallah a makon da ya wuce, Hashem Safieddine, wanda abokin wasa ne ga marigayin - na 'yan uwa.

A ranar Juma'a Isra'ila ta hare shi a Beirut a kwatankwacin hare-haren da ta kai ta kashe Nasrallah.

Sojin na Israila sun ce katafariyar garkuwan nan tasu, ta tare yawancin makaman roka kusan 180 da Hezbollah ta harba mata daga kudu zuwa yankin arewacin ƙasarsu.

Harwayau Isra'ilar ta kuma kai hari kan wani gini na jama'a a arewacin tashar ruwan Tripoli babban birnin Libya.

Shi kuwa Shugaba Biden na Amurka cewa ya yi yana ƙoƙarin shawo kan Isra'ila kan kada ta kai hari kan wuraren haƙar mai na Iran a matsayin ramuwar gayya ta harin makamai masu linzami da Iran ɗin ta kai wa Isra'ilar ranar Talata, bayan da hasashen kai harin kan wuraren hakar man ya sa farashin mai ya tashi da kashi biyar cikin ɗari a duniya a ranar Alhamis.

Shugaban wanda ya ƙara jaddada cewa Isra'ila tana da duk wata dama da 'yanci na ramuwar gayya, a jawabin da ya yi ga manema labarai a fadar gwamnatin Amurka, White House, ya ce shi a karan kansa ba zai so a kai hari kan wuraren hakar mai na Iran ba.

Biden ya kuma gargaɗi Isra'ila da kada ta kai harin da zai shafi farar hula.

''Shirin da na haɗa, ya samu goyon bayan kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, da yawancin abokanmu a faɗin duniya, a matsayin wata hanya ta kawo ƙarshen wannan. 'Yan Isra'ila suna da duk wani 'yanci na mayar da martani ga miyagun hare-hare a kansu, ba wai kawai na Iraniyawa ba, a'a daga kowa ma kama daga Hezbollah da 'yan Houthi. To amma abin shi ne dole su yi taka tsan-tsan sosai don kauce wa farar hula da za a samu.''

Kawo yanzu yanayin zaman tamkiya tsakanin ƙasashen biyu- Iran da Isra'ila na ci gaba da kasancewa yayin da Firaministan Isra'ilar Benjamin Netanyahu ke nazarin yadda zai mayar da martani kan harin makamai mazu linzami da Iran ta kai wa ƙasarsa ranar Talata.