Isra'ila na tunanin Hezbollah mai makamai da jajirtattun mayaƙa za ta gajiya

Hayaki ya turnuke sararin samaniya, lokacin da Isra'ila ta kai hari ta sama a Marjayoun,kusa da iyakar kasar da Lebanon, ranar 23 ga watan Satumba 2024

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Cikin kwanaki biyu Isra'ila ta kaddamar da hare-hare ta sama 1,000 zuwa a kan Lebanon
    • Marubuci, Jeremy Bowen
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Editan ƙasashen duniya, BBC News
    • Aiko rahoto daga, Jerusalem
  • Lokacin karatu: Minti 9

Shugabannin Isra'ila na ta murnar nasarar da suka samu ta kai harin farko kan Hezbollah ta hanyar sanya ababen fashewa cikin na'urar sadarwa ta oba-oba, daga nan suka kaddamar da hare-hare ta sama.

A ranar Litinin, ministan tsaron Isra'ilar Yoav Gallant ya yi ta koda kasarsa kan namijin kokarin da ta yi na kai harin.

“Yau babbar rana ce.... Wannan ne mako mafi muni ga Hezbollah tun kafuwarta, kuma sun ga mummunan sakamako a zahiri.” in ji shi.

Gallant ya ce hare-hare ta saman sun lalata dubban makaman roka da watakil a kashe Isra'ilawa da su.

Hukumomin Lebanon sun ce sama da mutum 550 ne suka mutu a harin, ciki har da yara 50. Wannan rabi ne na adadin wadanda aka kashe cikin wata guda da Isra'ila da Hezbollah suka kwashe suna gwabza fada a shekarar 2006.

Isra'ila ta yi amanna zafafa hare-hare da matsa lamba ne kadai za su tanƙwara Hezbollah yin biyayya ga abin da take bukata, da bakanta ran shugaban kungiyar Hassan Nasrallah da aminansa - musamman Iran da ke mara wa Hezbollah baya.

'Yan siyasa da sojojin Isra'ila na bukatar yin nasara ta kowacce fuska. Duk da shekara guda sojojin Isra'ila suka dauka a yaki da kungiyar Hamas a Gaza, da alama kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.

Har yanzu Hamas na da karfinta kuma mayakanta ba su gaji ba, kullum tudadowa suke yi daga hanyoyin karkashin kasa, suna kuma yi wa Isra'ilar barna, kuma har kawo yanzu suna tsare da Isra'ilawan da suka yi garkuwa da su.

Kungiyar Hamas ta mamayi Isra'ila da shayar da ita mamaki a watan Oktobar bara. Ita dai Isra'ila ba ta kallon Hamas a matsayin wata barazana, amma lamarin ya sauya cikin kankanin lokaci.

Rundunar sojin Isra'ila IDF da hukumar leken asiri ta Mossad sun jima suna shirya yadda za su yaki Hezbollah, tun bayan kawo karshen yakin da ya gabata a shekarar 2006.

Firaminista Benjamin Netanyahu ya amince akwai nasara a fadan da ake gwabzawa a halin yanzu, a ganinsa suna samun cigaba a kokarin da suke yi na gurgunta karfin ikon Hezbollah.

Burin Netanyahu shi ne dagakatar da Hezbollah daga harbawa kasarsa makaman roka. A bangare guda kuma, sojojin Isra'ila na cewa shirin su shi ne su tilastawa Hezbollah janyewa daga iyakar kasar, su kuma lalata wuraren da suke kitsa kai hare-haren da ke barazana ga tsaron Isra'ila.

An samu wani Zirin Gazar?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A makon da ya gabata, al'ummar Lebanon sun ga tashin hankalin da suka jima ba su gani ba, lamarin ya yi kama da wanda aka gani a Gaza, musamman bayan Isra'ila ta umarci farar hula su fice daga kudancin kasar da ta ke shirin kaddamar da hare-hare nan ba da jimawa ba.

Ta dora alhakin hakan kan kungiyar Hezbollah, kamar dai yadda ta dora hakkin halin da fararen hula ke ciki a Gaza kan kungiyar Hamas.

Masu suka da makiya Isra'ila sun ce an yi gargadin cikin gadara da isa sannan babu isasshen lokacin da iyalai za su nemi mafaka a wasu wuraren.

Yawancin hare-haren da Hezbollah ta kai wa Isra'ila sun shafi farar hula, hakan ya take dokokin da suka bai wa farar hula kariya a lokacin yaki. Isra'ila da aminanta ciki har da Amirka da Birtaniya sun jima da ayyana kungiyar Hezbollah a matsayin ta 'yan ta'adda.

Hukumomin Isra'ila dai sun sha nanata sojojinsu na da cikakkiyar tarbiyya da bin dokokin yaki, amma yawancin kasashen duniya sun yi allawadai da abin da ta ke yi a Gaza.

Bayanan bidiyo, Kalli yadda ababen fashewa suka tashi a wata kasuwa a Lebanon

Bari mu duba harin ababen fashewa a na'urar sadarwa.

Isra'ila ta ce abin da ta yi niyya shi ne kai wa mayakan Hezbollah hari, wadanda ke amfani da na'urar sadarwar ta pager, amma Isra'ilar ba ta san takamaimai inda na'urorin za su kasance ba idan an sanya bama-bamai a ciki a lokacin da za su tashi, wannan ne dalilin da ya sa farar hula da kananan yara a cikin gidaje, da kantuna suka mutu, wasu suka jikkata.

Wannan ya sa wasu lauyoyi suka karkare da cewa Isra'ila na amfani da karfi wajen kashe mutane ba tare da la'akkari da abin da zai je ya dawo ba, musamman kan bai wa farar hula kariya, hakan ya sabawa dokokin yaki na duniya.

Tun a shekarun 1980 Isra'ila da Hezbollah suka fara yaki.Amma yaki a iyakar kassashen biyu ya fara ne tun ranar 7 ga watan Oktoba, lokacin da Hassan Nasrallah ya umarci sojojinsa kai hare-hare a kowacce rana a iyakarsu da Isra'ila domin goyon baya ga Hamas. Sun mamayi sojojin Isra'ila tare da tilastawa mutanen garuruwan da ke iyakar kasasshen biyu kusan 60,000 tserewa.

Tunanin hare-haren da aka kai a baya

An jiyo daidaikun kafafen yada labaran Isra'ila na kwatanta tasirin hare-hare ta sama da aka kai wa Hezbollah da irin wanda ta kai kasar Masar a watan Yunin shekarar 1967.

Samame ne da ya yi tambari a duniya da kuma ya daidaita sojin sama na Masar, lokacin da aka jere jiragensu a kasa. Cikin kwanaki shida Isra'ila ta yi nasara kan kasashen Masar da Syria da Jordan.

Wannan nasara ita ce ta dasa damba ga Isra'ila har ta yi nasarar karbe ikon yamma da gabar Kogin Jordan, ciki har da yammacin birnin Kudus, da zirin Gaza da tuddan Golan.

Sai dai a nan akwai bambanci, ma'ana yaki a Lebanon da Hezbollah, saboda Isra'ila ta dan sha kan Hezbollah, amma duk da hakan bai hana ta kai munanan hare-hare Isra'ila ba.

A baya dai, yake-yaken da aka gwabza tsakanin Isra'ila da Hezbullah, an yi gumurzu, da yi wa juna barna sai dai babu wanda ya yi nasarar kirki tsakanin bangarorin biyu.

Watakil wanna karon ma tarihi ya maimaita kan shi, ko da ya ke nasarar da Isra'ila ta yi a makon da ya wuce ta dan karfafawa sojoji da hukumar leken asirin kasar kwarin gwiwa.

Hare-haren da Isra'ila ke kai wa tamkar caca-ce, da fatan nan da dan lokaci Hezbollah za ta raunana ta kuma janye daga iyakar Isra'ila da daina harba makamai. Sai dai yawancin masu sharhi na ganin babu rana bare lokacin da Hezbollah za ta daina hakan, saboda yakar Isra'ila na daga cikin dalilan da ya samar da Hezbollah.

Don haka, maimakon Isra'ila ta amsa shan kaye a yakin, ta gwammace ayi ta tafiya a hakan. Idan Hezbollah ta ci gaba da kai hare-hare arewacin Isra'ila da maida shi yanki mai hatsari ga farar hula, ndole zabi biyu ya ragewa Isra'ila, ko dai ta kaddamar da yaki ta kasa watakil ta karbe wasu yankuna da za su shiga karkashin ikonta.

Jirgin yakin Isra'ila samfurin F-15 a sararin Haifa ranar 24 ga watan Satumba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jirgin yakin Isra'ila lokacin da yake keta sararin arewacin kasar, kuma ministan tsaron kasar ya kira hare-hare ta sama da sojojinsu suka kai Lebanon da abin alfahari da nasara

Ba wannan ne karon farko da Isra'ila ke mamayar Lebanon ba.

A shekarar 1982 sun far wa birnn Beirut domin hana Falasdinawa kai samame kasar. An tilasta musu mika wuya a cikin gida da waje, lokacin da Isra'ila ta yi garkuwa da wasu mabiya adinin Kirista, bayan kisan kare-dangin da aka yi wa Falasdinawa farar hula a sansanonin 'yan gudun hijira na Sabra da Shatila a birnin Beirut.

Zuwa shekarar 1990, Isra'ila ta kara mamaye wasu filayen Lebanon da ke iyakar kasashen biyu. A wancan lokacin, janar-janar din sojin Isra'ila na yanzu matasa ne wasu kuma yara kanana, wadanda suka gwabza fada babu kakkautawa da Hezbollah, lokacin da take samun karfi da kuma barazana ga Isra'ila.

Firai ministan Isra'ila na wancan lokacin, Ehud Barak, da tsohon shugban ma'aikatan rundunar sojin kasar IDF, sun fice daga kungiyar tsaro a shekarar 2000. A cewarsu, babu wata rana da ta yi mu su ta fuskar tsaro, sai ma kashe zaratan sojojinta.

A shekarar 2006 Hezbollah ta kaddamar da hari kan sojin Isra'ila a iyakar kasar tare da cafke wasu daga ciki. Bayan karewar yakin, shugaban kungiyar Hezbollah Hassan Nasrallah ya sanar da cewa da ya san abin da Isra'ila ta shirya yi bayan samamen da bai kai shi ba. Amma kafin a dauki mataki, firai minista Ehud Bank ya kaddamar da yaki.

Da farko, fatan Isra'ila shi ne amfani da karfinta wajen hana kai hare-haren makaman roka zuwa kasarsu Amma da ba ta yi nasara ba, sai tankokin yaki da sojoji suka fara dannawa ta kasa zuwa iyakar kasashen biyu. Yakin ya kasance mummuna da tashin hankali ga farar hular Lebanon. Ko a ranar karshe ta yakin, Hezbollah ba ta daina harba makaman roka zuwa Isra'ila ba.

Yaki a yanzu da mai zuwa nan gaba

Kwamandojin sojin Isra'ila sun kwana da sanin matukar suka shiga Lebanon ana barin wuta to za su samu kai a tsaka mai wuya, fiye da yakin da suke yi da Hamas a Gaza.

Ita ma Hezbollah tun bayan yakin da suka gwabza a shekarar 2006 take shirye-shiryen ramuwar gayya da mamaya ta kasa, ta amfani da kudancin Lebanon mai cike da tsaunuka da manyan duwatsu, da za su taimaka wa wanda ya san kan yankn cin abokin gaba da yaki.

Cibiyar kwararru ta mai mazauni a Washington DC, ta yi kiyasin akalla kungiyar Hezbollah na da mayaka 30,000, baya ga masu shirin ko-ta-kwana 20,000, yawanci an ba su horo kan kwarewar fagen daga, wasu kuma suna da kwarewar yaki musamman wadanda suka shiga yakin Syria domin mara baya ga gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad.

Wasu kuma na kiyasin Hezbollah na da makaman roka da masu linzami 120,000 zuwa 200,000. Masu cin dogo da gajeren zango, da wadanda ka iya fadawa biranen Isra'ila.

Wani jami'in tsaron Isra'ila ya wufe ta gefen wani gini da makamin roka ya daidaita a garin Kiryat Shmona da ke arewacin Isra'ila, ranar 24 ga watan Satumba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tun a watan Oktobar bara Hezbollah da Isra'ila ke gwaba fada, lamarin da ya tilasta wa dubban mutane barin muhallansu musamman a garin Kiryat Shmona da ke arewacin Isra'ila

Isra'ila na tunanin Hezbollah ba za ta yi amfani da dukkan mayakanta ba, kan tsoron sojin sama na Isra'ila kar su yi wa na su sojin abin da suka yi a Gaza da suka mayar da daukacin garuruwa tamkar kufai, da kashe dubban farar hula.

A nata bangaren, Iran ba za ta so Hezbollah ta yi amfani da manyan makamai ba, ta na son ajiye su ne idan Isra'ila ta yi kuskuren kai hari wuraren ajiyar makaman nukiliyarta. Wannan ma wata cacar ce da babu riba. Hezbullah za ta iya amfani da makaman da take da su kafin Isra'ila ta lalata su.

Yayin da ake ci gaba da yaki a Gaza, fargaba na karuwa a yamma da gabar kogin Jordan da Yahudawa 'yan kama wuri zauna suka mamaye, dole Isra'ila ta san yadda za ta yi shirin mamayar Lebanon. Su na karfafa gwiwar sojojinsu, an ba su horo da kayan aiki, sai dai wasu kebantattun zaratan sojojin Isra'ila sun fara sarewa da gajiya, a daidai lokacin da aka kusa cika shekara guda da fara yaki tsakanin Hamas da Isra'ila.

Makurar karshe a huldar diflomasiyya

Kasashe aminan Isra'ila da Amurka ke jagoranta ba sa son Isra'ilar ta tsawaita yaki da Hezbollah ba kuma sa son ta mamaye Lebanon. Sun kafe sasancin diflomsiyya ne kadai zai kawo zaman lafiya a iyakokin kasashen biyu, sannan farar hula da suka tserewa garuruwansu, su koma gida.

Wata tawagar wakilan Amirka na kokarin ganin an cimma wata yarjejeniya, karkashin kudurin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na 1701 da akai amfani da shi wajen kawo karshen yaki tsakanin Hezbollah da Isra'ila a shekarar 2006.

Sai dai jami'an diflomasiyya na tsaka mai wuya, matukar ba a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza. Shugaban kungiyar Hezbollah Hasan Nasrallah ya ce ba za su daina kai wa Isra'ila hari ba har sai ta dakatar da hare-haren da ta kaiwa a Gaza.

A halin yanzu daga kungiyar Hamas, har sojin Isra'ila na kokarin ganin an hau teburin sulhu da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da a Gaza, da musayar fursunonin bangaren Isra'ila da Falasdinu.

Isra'ila na ci gaba da luguden makamai masu linzami a Lebanon. kuma tuni iyalan da ke fama da talauci da matsin tattalin arziki suka fara fuskantar kalubale, da firgicin rashin sanin madafa. Isra'ila dai ta san Hezbollah za ta iya yi ma ta illa fiye da wadda ta faru a baya.

Ta kuma yi amanna lokaci ya yi da za a yi amfani da matsi da karfin iko a kawo karshen ayyukan Hezbollah a iyakar kasar. Sai dai lamarin ba mai sauki ba ne sakamakon Isra'ilar na gwabza yaki da mayaka masu ingantattun makamai, kuma suke cike da fushi.

Wannan ne lokaci mai matukar hadari, a kusan shekara guda da Hamas ta kaddamar da yaki kan Isra'ila, kuma har yanzu babu alamun sassauci daga dukkan bangarorin biyu.

A gefe guda kuma farar hular Falasdinawa na ci gaba da shan bakar wahala.