Hezbollah da Isra'ila: Ana fargabar sake ɓarkewar wani sabon yaƙi a Gabas ta Tsakiya

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da ake ci gaba da gwabza yaƙin Gaza, akwai fargabar sake ɓarkewar wani yaƙin a yankin Gabas ta Tsakiya, lamarin da ka iya warzaga ragowar zaman lafiyar yankin, da ma wasu wasu yankunan duniya.
Isara'ila da ƙungiyar Hezbollah a Lebanon (wadda ke samun goyon bayan Iran) sun shafe a ƙalla wata tara suna musayar wuta a kan iyakokin ƙasashen biyu.
Idan wannan yaƙi ya ɓarke, hakan zai iya kawar da hankali daga yaƙin da ake yi a Gaza, sannan zai janyo hankalin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a Iraƙi da Yemen - da ke samun goyon bayan Iran - su tayar da rikici a yankin Gabas ta Tsakiya, lamarin da ka iya harzuƙa Amurka. Haka kuma ana ganin cewa Iran da kanta ka iya shiga yaƙin kai-tsaye.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin samun ''mummunan bala'i fiye da yadda ake zato''.
A yanzu yayin da kowane ɓangare ya kawo wuya, hari ɗaya ka iya jefa ilahirin yankin cikin mummunan yaƙi.
Hare-haren abubuwan fashewa na daga cikin abin da tsohon birnin Tyre na Lebanon ke fuskanta a bazarar 2024, yayin da ƙungiyar Hizbullah da Isra'ila ke musayar wuta daga nesa a kan iyakokokinsu mai nisan kilomita 25.
"Kowace rana bam," in ji Roland, mai shekara 49, yayin da yake hutawa a kan lilo. Yana zaune a ƙasashen waje amma a yanzu ya dawo gida hutu.
Abokinsa Mustafa, mai shekara 39, ya ce: “Mun saba da shi tsawon watanni, ko da yake yara suna ɗan jin tsoro.” Ya gyada kai zuwa ga ɗiiyarsa Miral, mai shekara 7, wadda ke wasa da ruwa a tafkin.
"Idan ta ji fashewa, takan yi tambaya, 'Shin za a samu bam yanzu?'" in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images
A farkon wannan watan, an samu fashewar bam a garin Tyre da ke makwabtaka da wurin, Isra'ila ta ce ta kashe wani babban kwamandan Hezbollah, Mohammed Nimah Nasser.
"Mun ji hayaniya," in ji Mustafa, "kuma muka ci gaba da cin abinci."
Amma masu wanka a gaɓar tekun Tyre ka iya fuskantar cikas. Wannan birni zai kasance cikin wuraren da za su fuskanci hare-hare, tare da sauran yankunan kudancin ƙasar Labanon, inda nan ne Hizbullah ta fi ƙarfi.
Rikicin na ci gaba da ta'azzara
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ranar 8 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata – kwana guda bayan mayaƙan Hamas sun kai hari cikin Isra'ila tare da kashe kimanin mutum 1,200 tare da yin garkuwa da wasu 251 – Hezbollah ta shiga yaƙin, inda ta riƙa harba rokoki zuwa Isra'ila.
Ƙungiyar - wadda ke bin tafarkin Shi'a - ta ce tana yin hakan ne domin nuna goyon bayan wa Gaza.
Ba a jima ba Isra'ila ta mayar da martani.
Hezbollah - wadda ita ma jam'iyyar siyasa ce - ita ce mafi karfi a Lebanon.
Kamar ƙungiyar Hamas, ƙasashen duniya da dama ciki har da Amurka da Birtaniya, sun sanya ta cikin ƙungiyoyin ta'addanci, ciki har da Birtaniya da Amurka.
Amma ba kamar Hamas ba, Hezbollah na da ƙarfin makaman da za ta iya yi wa Isra'ila barazana.
An yi imanin cewa tana da makaman rokoki da makamai masu linzami fiye da 150,000 - wasu na musamman - masu iya yin ɓarna a faɗin ƙasar.
A taƙaice Hizbullah - wadda a Hausa za mu iya fassara ta da 'Gungun mutane masu bin tafakin Allah' - tana da makamai fiye da wasu ƙasashe da dama.
Ƙasar Iran da ke goyon bayanta - wadda ke inkarin yancin wanzuwar Isra'ila - tana bai wa mayaƙan ƙungiyar horo da tallafin kuɗi ga maƙiya ƙasar ta Yadudawa.
Rikicin ya ta'azzara, inda aka yi ta kai hare-hare kan iyakokin ƙasar.
Tuni wasu ƙasashen ciki har da Jamus da Netherlands da Canada da Kuma Saudiyya suka faɗa wa ƴan ƙasashensu da ke Lebanon su gaggauta ficewa daga ƙasar.
Haka kuma Birtaniya ta shawarci ƴan ƙasarta su guji yin bulaguro zuwa Lebanon, tare da umartar 'yan ƙasarta da ke can su fice matuƙar za su iya.
Ya zuwa yanzu, duka ɓangarorin biyu sun fi kai hare-hare kan wuraren da sojojin juna suke a kusa da kan iyaka - waɗanda ke cikin shirin ko-ta-kwana.

Amma a nan ɓangaren Lebanon, mun ga irin ɓarnar da aka yi wa yankunan fararen hula inda aka samu ƙone-ƙonen gonaki, da gidajen da ba a taba gani ba, da ƙauyuka da dama da mazaunansu suka fice.
Wannan zaman tankiya da ake ciki ta tilasta wa dubban mutane barin gidajensu, inda fiye da mutum 90,000 daga Lebanon da kuma kusan 60,000 daga ɓangaren Isra'ila suka bar gidajensu.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce Hezbollah ta kashe sojojinta 21. Adadin fararen hula da suka mutu ya kai 12, a cewar jami’an gwamnati.
Asarar Lebanon ta fi girma , inda ta kai 466, a cewar Ma'aikatar Lafiyar ƙasar. Hezbollah ta ce akasarin waɗanda suka mutu mayaƙanta ne.
Daya ɗga cikin fararen hular da mutuwarsu ta girgiza iyalinta, ita ce Sally Skaiki.
'Ba za mu yafe musu ba'
“Ban kiranta da sunanta 'Sally,” in ji mahaifinta Hussein Abdul Hassan Skaiki. “A koyaushe nakan kirata da ‘rayuwat’ - Ita ce komai nawa.”
“Ita kaɗai ce mafe a gidanmu, kuma mun rasata, ni da 'yan uwanta uku.”
Sally, mai shekara 25, ma'aikaciyar sa kai ce da ke aiki da wata ƙungiyar lafiya . An kashe a wani hari ta sama da Isra'ila ta kai da magariba ranar 14 ga watan Yuni, a lokacin da take tsaye a kusa da gini.
Mahaifinta, sanye da baƙin tufafin domin nuna jimami, tare da koren shirami na ƙungiyar Amal ta Shi'a, wadda ƙawa ce ga ƙungiyar Hezbollah.

Asalin hoton, BBC / Goktay Koraltan
Mun haɗu da shi a ƙauyensu na Deir Qanoun En-Naher, mai nisan kilomita 30 daga kan iyaka. Babban titin ƙauyen na cike da hotunan mayaƙan ƙungiyar da aka kashe a yakin da suke da Isra'ila - a watannin baya-bayan nan, wasu kuma a shekarar 2006 lokacin da ɓangarorin biyu suka yi yaƙi na ƙarshe.
A wancan rikici, ƙungiyar Hizbullah ta yi yaƙi Isra'ila, amma ta yi babbar hasarar ga ƙasar da a'ummarta. An samu mummunar ɓarna, kuma an kashe fararen hula fiye da 1,000 na Lebanon, tare da wasu mayaƙan Hizbullah da ba a tabbatar da adadinsu ba, kamar yadda alƙaluman hukuma suka nuna.
Gwamnatin Isra'ila ta ce adadin waɗanda suka mutu a ƙasar ya kai 160, yawancinsu sojoji ne.
A gefen da Hussein ke zaune akwai wani katon hoton Sally, cikin gyalenta sanye da kayan aikinta na jinya. Yana maganar 'yarsa cikin alfahari da bacin rai.
"Tana son taimaka wa mutane," in ji shi. “Duk wata matsala da ta faru, takan garzaya wurin. An so ta sosai a ƙauyen. A kodayaushe fuskarta cike da murmushi.”
Yayin da muke zantawa da shi, sai muka ji wata ƙara da ta girgiza tagogin gidansa.
Hussaini ya ce wannan ya zame mana jiki, al'amari ne na yau da kullum.
"Isra'ila ta jima tana kashe mutanenmu a nan," in ji shi.
“Ba za mu yafe musu ba. Ba ma fatan zaman lafiya tsakaninmu.”
A wannan karon, babu mutuwa ko halaka. Maimakon haka, jiragen yaƙin Isra'ila suna haddasa sauti don sanya tsoro da fargaba cikin zukatan jama'a.
Kuma, tun daga watan Oktoba, Isra'ila ta fara yaɗa wani abu a kudancin Lebanon - wani farin hayaƙi ne da ke haddasa shaƙewa.

Asalin hoton, Getty Images
Abin, wani sinadari ne da ke cakuɗa da iskar shƙa ta oxygen. Yana mannewa kan fata da tufafi kuma yana iya shiga cikin jiki ya ƙone kashi, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana.
Moussa al-Moussa - manomi, mai shekara 77 - ya ce ya san hayaƙin sosai.
Ya ce Isra’ila ta shafe wata guda tana hura farin hayaƙi cikin gonarsa da ke kauyen al-Bustan a kowace rana, lamarin da ke shafar numfashinsa da kuma ryuwarsa.
Ya ce mini, “Na sa shiramina, kuma na lulluɓe baki da hancina har sai da aka kawo ni asibiti”.
"Ba mu da abin rufe fuska. Na kasa numfashi. Ba zan iya hango nisan mita guda a gabana ba. Kuma idan ka taɓa wani abu, bayan kmar mako guda sai ka ga ya ƙone''.
Ƙungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch, ta tabbatar da amfani da farin hayaƙin a yankuna masu yawan jama'a a kudancin Lebanon, ciki har da al-Bustan.
Ta ce amfani da farin hayaƙin da Isra'ila ke yi "ba tare da nuna bambanci kan wuraren da jama'a ke ciki ba ya saɓa wa doka".
Dakarun tsaron Isra'ila (IDF) sun musanta hakan, suna masu cewa yin amfani da harsashi na farin hayaƙi "ya halasta a ƙarƙashin dokokin duniya". Ya ce ba a amfani da waɗannan harsasai a wuraren da jama'a ke da yawa "sai dai akwai wuraren ak togance".

Asalin hoton, BBC / Goktay Koraltan
Kamar sauran manoman da ke kusa dakan iyakar, Moussa na fargabar cewa Isra'ila ta sanya guba a ganakinsa na zainun da na ganyen taba.
“Farin hayaƙin na ƙona gonakin, su kuma ƙona mutane da amfanin gona da lalata gidaje,” in ji.
Ko da ya koma gida, yana fargabar girbin amfanin amfanin gonarsa, saboda tsoron yi wa iyalinsa da masu saye barazana.
A lokacin da na tambayi Moussa cewa yaƙi nawa ya gani a rayuwarsa, sai ya yi dariya
“Mun shafe duka rayuwarmu cikin yaƙi,” in ji shi. “Allah kawai ya sani ko yaushe wannan abu zai ƙare.”
'Ba tsoro muke ji ba'
A matsayinsa na ɗaya daga cikin manyan kwamandojin Hizbullah, Mohammed Nimah Nasser, wanda ake nema ruwa a jallo.
Ya shiga yaƙi da Isra'ila a 2006, da kuma kafin, kuma ya yi yaƙi a Siriya da Iraƙi.
A cikin 'yan watannin nan ya "shirya jagorantar kai hare-hare da dama kan Isra'ila", a cewar Hezbollah.da
Isra'ila ta bibiye shi tare da kama shi a Tyre a ranar 3 ga Yuli. Inda aka kashe shi a wani hari ta sama da ya faɗa kan motarsa da rana tsaka.
An kuma yi masa jana'izar ban girma a matsayin shahidi a kudancin Beirut, inda Hezbolla ta fi ƙarfi.











