Wane mataki Hezbollah, Iran, da Isra'ila za su ɗauka nan gaba?

Magoya bayan Hezbollah suna riƙe da hotunan Hassan Nasrallah

Asalin hoton, Reuters

    • Marubuci, Frank Gardner
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Security Correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 3

Kashe shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah da Isra'ila ta yi babbar tsokana ce a yaƙin da take yi ƙungiyar ta ƙasar Lebanon na tsawon shekaru.

Lamarin ya ƙara sanya fargaba da ingiza yankin, da tuntuni ake ganin mummunanan yaki ka iya barkewa da kasashen Amirka da Iran za su shiga tsundum.

Saboda haka, har zuwa ina ake sa ran rikicin zai kai?

Wannan amsar na kunshe cikin madogara guda uku.

Ko me Hezbollah za ta yi?

Kungiyar Hezbollah na cikin jimami da alhini, kan munanan raunukan da akai ma ta na rashin zakakuri kuma jajirtaccen shugaba kamar Hassan Nasrallah.

An fille kan shugabancinta bayan kashe kusan jagorori 12. An lalata hanyoyin sadarwarta ta hanyar cika na'urorin pager da na oba-oba da ababen fashewa, sannan kuma an lalata makamanta masu yawa.

Mai sharhi kan al'amuran Gabas ta Tsakiya mazaunin AmurkaMohammed Al-Basha ya ce: "Rashin Nasrallah zai shafi ƙungiyar sosai da gaske, zai shafi harkokin siyasarta da na soji na ɗan lokaci."

Amma duk wani tunani da ke cewa Hezbollah za ta mƙa wuya ba mai yiwuwa ba ne.

Ƙungiyar ta ci alwashin za ta ci gaba da fafatawa. Har yanzu tana da dubban mayaƙa, da yawansu waɗanda suka taya gwamnatin Syria, kuma zukatansu cike suke da ɗaukar fansa.

Har yanzu tana da makamai masu linzami, waɗanda da yawnansu masu cin dogon zango ne kuma masu linzami da ka iya kaiwa har birninn Tel Aviv. Tabbas wasu mambobinta za su matsa kan a yi amfani da su kafin Isra'ila ta lalata su.

Amma idan suka yi hakan ta yadda na'urorin kakkaɓo makaman ba za su iya tare su ba kuma suka kashe fararen hula, martanin da Isra'ila za ta mayar zai muni sosai - lalata gine-ginen Lebanon ko ma ta haɗo har da Iran.

Me Iran za ta yi?

Kazalika, kisan nasa lakuce wa Iran hanci ne, wadda ta bayyana kwana biyar na makoki.

Ta kuma ɗauki matakin ta-kwana na ɓoye shugaban addininta Ayatollah Ali Khamanei saboda kada shi ma a kashe shi.

Har yanzu Ira ba ta ɗauki fansar kisan shugaban Hamas Ismail Haniyeh ba, wanda aka yi a ƙasarta kuma take zargin Isra'ila da aikatawa.

Iran na da gungun ƙawaye masu ɗauke da makamai a duka faɗin Gabas ta Tsakiya waɗanda ake kira ƙawancen gwagwarmaya wato "Axis of Resistance" a Turance.

Baya ga Hezbollah, akwai Houthi a Yemen, da wasu masu yawa a Syria da Iraƙi. Iran za ta iya neman su tsananta hare-hare a kan Isra'ila da sansanonin Amurka a yankin.

Amma duk martanin da za ta mayar, akwai yiwuwar za ta yi hakan ta yadda ba zai jawo mummunan yaƙi ba.

Wane mataki Isra'ila za ta dauka?

Wani mutum ne yake leƙen ramin da hari ta sama ya haƙa bayan kashe Hassan Nasrallah a Beirut

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani mutum ne yake leƙen ramin da hari ta sama ya haƙa bayan kashe Hassan Nasrallah a Beirut
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Idan ma akwai masu shakku game da irin wannan hari, to yanzu babu.

A bayyane take Isra'ila ba ta da niyyar dakatawa da hare-haren duk da tayin tsagaita wuta na kwana 21 da ƙawayenta suka gabatar, cikinsu har da Amurka.

Rundunar sojin ƙasar na ganin ta samo kan Hezbollah yanzu saboda za su so su ɗora kan har sai sun ga bayan makamanta.

Abu ne mai wuya a iya gane ta yadda Isra'ila za ta kawar da barazanr Hezbollah ba tare da tura dakaru ta ƙasa ba.

Rundunar ta fitar da wani bidiyo da ke nuna dakarunta na atasaye a kusa da iyakar Leabonon.

Amma Hezbollah ma ta shafe shekara 18 da suka wuce, tun daga yaƙinsu na ƙarshe, tana shirin fafata yaƙi na gaba. A jawabinsa na ƙarshe kafin ya rasu, Nasrallah ya faɗa wa mabiya cewa idan Isra'ila ta kai samame kudancin Lebanon "wata dama ce mai cike da tarihi".

Kutsawa ta ƙasa kudancin Lebanon abu ne mai sauƙi a wajen Isra'ila. Amma kuma fitowa - kamar yadda muke gani a Gaza - za ta ɗauki mai tsawo.