Buni ya samu wa'adi na biyu a Yobe

buni

Asalin hoton, Facebook/Mai Mala Buni

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta - INEC ta ayyana Mai Mala Buni na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Yobe.

Da yake sanar da sakamakon zaben a Damaturu babban birnin jihar, babban jami'in da ke kula da zaben, Farfesa Umaru Pate ya ce Mai Mala Buni ya lashe zaben da kuri'u 317,113 a yayin da Sheriff Abdullahi na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 104,259.

A shekarar 2019 ne aka zaɓi inuwa a matsayin gwamnan jihar ta Yobe, inda ya yi wa'adinsa na farko.