Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Baccin ƙasa da awa biyar ga ƴan sama da shekara 50 ka iya jawo cututtuka
- Marubuci, Michelle Roberts
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital health editor
- Aiko rahoto daga, BBC News
Wani sabon bincike ya nuna cewa mutanen da shekarunsu suka haura 50 kuma suke baccin ƙasa da sa'a biyar kowane dare na cikin haɗarin kamuwa da matsalolin lafiya.
Binciken da wasu ƙwararru ƴan Birtaniya suka yi, ya yi nazarin mutum dubu takwas da shekarunsu suke daga 50 zuwa 70.
Mutanen da suka ce suna samun baccin sa'a biyar ko kasa da haka sun fi yiwuwar kamuwa da cututtuka kamar daji da ciwon suga da ciwon zuciya sabanin wadanda suke samun baccin sa'a bakwai zuwa sama.
Masu binciken sun ce rashin lafiya ka iya katse bacci - amma rashin isasshen bacci ma na sa haɗarin kamuwa da cututtuka.
Akwai hujjojin da ke tabbatar da cewa barci na taimaka wa wajen samun isasshen hutu da farfaɗo da jiki da ƙara kuzari.
Tambayoyin da aka yi wa kusan mutum 8,000 din su ne:
"Barcin awa nawa kuke samu a ƙalla a duk dare?
Wasu kan sanya wani agogo mai bin diddigin lokutan baccinsu.
An kuma binciki matsanantan halin lafiyarsu kamar ciwon suga da kansa da ciwon zuciya na tsawon shekara 20.
Waɗanda suke barcin awa biyar ko ƙasa da haka a shekaru 50 sun fi fuskantar hadarin kamuwa da cututtuka da dama da kashi 30 cikin 100 fiye da masu yin baccin awa bakwai.
An kuma alaƙanta rashin barci sosai a shekaru 50 a haɗarin fuskantar mutuwa sakamakon munanan cututtuka.
Ƙwararrun masu bincike daga Jami'ar College London da Jami'ar Paris Cité, sun bayar da shawarar a dinga samun barcin awa bakwai ko takwas.
Me ya sa muke barci?
Masana kimiyya ba su san ainihin dalilin ba, amma a bayyane yake cewa barci na taimaka wa ƙaƙwalwa wajen tuno da abubuwa kuma yana inganta yanayin, da mayar da hankali da kyautata tunani.
Sannan barci wata dama ce da ke sa ƙwaƙwalwa ke warwarewa da kawar da duk wasu gurɓatattun abubuwa daga cikinta.
Dabarun samun ingantaccen barci
Ka gajiyar da kanka da rana ta hanyar yin aiki sosai amma idan lokacin barci ya yi kusa sai ka ɗan sassauta
Ku guji barcin rana
Ku samar wa kanku tsari mai kyau na hidimomi da daddare, kamar tabbatar da cewa ɗakin barcinku yana cikin yanayi mai kyau - da labulaye masu kauri, shimfiɗar gado mai kyau, sannan ku guji taɓe-taɓen waya a yayin da kuka kwanta don yin barcin
Ku rage shan gahawa ko barasa a lokacin barci
Idan barcin ya ƙi zuwa, to kar ku tursasa kanku ko shiga damuwa - ku tashi ku ɗan yi wani abu da zai hutar da ku kaɗa, kamar karanta littafi, daga baya idan kuka fara jin barcin sai ku ajiye ku yi
Idan aikinku na dare ne, ku yi ƙoƙarin yin barci da zarar kun tashi daga ikin, sannan kuna iya sake barcin da farkon dare kafin lokacin aikin.
Daraktan Cibiyar Barci ta Surrey, Farfesa Derk-Jan Dijk, ya shaida wa BBC cewa: "Wannan aikin ya tabbatar mana da cewa rashin samun isasshen barci ba abu ne mai kyau a gare mu ba. A taƙaice dai yana da illa ga lafiya - duk da cewa hakan ba illa ba ne ga wasu.
"Babbar tambayar ita ce me ya sa wasu mutanen ba sa samun isasshen barci. Me ke jawo hakan, kuma me za mu iya yi a kai?
Idan aka daɗe ba a samun isasshen barci hakan na iya shafar lafiyarmu sosai.
A yanzu jefi-jefi likitoci kan bayar da maganin barci, amma yana iya jawo wasu matsalolin daban.
Amma a mafi yawan lokuta ana iya magance matsalar rashin barci.