Kullum sai an sake wa gawarwaki kaburbura a Khartoum - Jami'ai

Asalin hoton, Ken Mungai / BBC
Jami'ai a babban birnin Sudan da yaki ya daidaita, Khartoum sun ce a kullum sai sun gano sababbin kaburbura yayin da masu aikin sa-kai ke tono gawarwakin domin 'yan uwansu su yi musu jana'izar da ta dace.
Tsawon shekara biyu ana fafata yaki a babban birnin tsakanin rundunar sojojin kasar ta Sudan da kuma tsofaffin abokan aikinsu na kungiyar RSF – inda yakin ya yi sanadiyyar hallaka dubban fararen hula.
A watan Maris ne rundunar sojin ta sake kwato birnin, wanda tun daga sannan ya kasance kusan cikin zaman lafiya.
Wani jami'in ma'aikatar lafiya ya ce kusan a kullum ana gano kaburbura a ko'ina a fadin Khartoum ciki har da a kofar gidaje da makarantu da masallatai. Kuma kaburburan ba su da zurfi – an dan binne gawar ne kawai a rufe ta.
Hakan ko ta kasance ne saboda a lokacin da ake tsananin yaki tsakanin bangarorin biyu na soji da na kungiyar RSF, don kwace iko da babban birnin- dole mutane su binne 'yan uwansu a kusa da inda suke kuma cikin sauri.
Jami'in ya ce , yawan gawarwakin da ake samu a irin wadannan kaburbura a unguwanni sun bambanta – wasu an binne gomman jama'a wasu kuma gawarwakin kadan ne uku ko hudu.
A yanzu kasancewar yakin ya karkata zuwa can yammacin kasar nesa da babban birnin – shi ne mutane suke tono gawarwakin 'yan uwan domin su yi musu jana'izar da ta dace yadda ya kamata.
Gwarawakin ba na fararen hula ba ne kadai har da na mayakan da ke yaki a tsakaninsu na rundunar soji da kuma na ‚yan kungiyar RSF – inda ake tono su ana sake musu jana'iza a kai su makabartu na sosai.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A Darfur kusan mutum miliyan daya ne suka makale a birnin El Fasher cikin yunwa saboda dakarun RSF sun tsare su, a kokarin kwace birnin daga hannun rundunar sojin Sudan din.
Can a Kordofan ma fararen hula na cikin hadari daga hare-hare ta sama na sojoji kuma ana zargin mayakan RSF da kashe dimbin mutane a kauyuka.
Yakin ya hallaka dubban jama'a tare da raba miliyyin 'yan Sudan din da gidajensu – wasu daruruwa ma sun bar kasar zuwa makwabtan kasashe.
Yakin da aka fara tun watan Afirilu na 2023 ya daidaita babban birnin da kuma wasu birane uku —Khartoum, da Omdurman, da kuma Bahri, tare da jefa rayuwar mutane cikin mummunan hali.
Kiyasin mutanen da suka mutu a kasar a sanadiyyar yakin ya bambanta sosai daga 20,000 har zuwa 130,000, kamar yadda kafofi daban-daban suka bayyana.
Wata kafar ta daban a ma'aikatar lafiya ta ce kusan mutum 3,000 ne suka mutu a 'yan watannin nan sakamakon kamuwa da cutuka da sauran matsaloli na rashin lafiya saboda yadda yakin ya kassara tsarin kula da lafiya na kasar.











