Uƙubar yunwa da mazauna El-Fasher ke ciki a Sudan

Hoton da aka yanke don ɓoye fuskokin wasu matan Darfur sanye da tufafi masu launi daban-daban, ɗaya daga cikinsu riƙe da kwanon cin abinci da babu komai a cikinsa . An ɗauki hoton a watan Afrilun 2025

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Bayanan hoto, Yaƙin basasar Sudan - wanda ke cikin shekara ta uku - ya kasance ɗaya da cikin mafiya munin matsalar jin ƙai a duniya
    • Marubuci, Barbara Plett Usher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa correspondent, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 4

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa iyalan da ke maƙale a birnin El-Fasher na Sudan da aka yi wa ƙawanya na fuskantar tsananin yunwa.

WFP ya ce fiye da shekara guda kenan bai samu shigar da abinci zuwa birnin da e yammacin yankin Darfur ba.

Mayaƙan RSF sun shafe kusan wata 16 da yi wa birnin ƙawanya, da nuin ƙwace shi daga sojojin gwamnati.

Gargaɗin na WFP na zuwa ne yayin da ƴan gwagwarwamayar ƙasar suka fara bayar da rahotonnin mace-mace sakamakon tsananin yunwa a birnin, wanda yanzu haka ke da mutum kusan 300,000 a cikinsa.

Sudan ta faɗa yaƙin basasa ne a cikin watan Afrilun 2023 bayan da rikicin jagoranci ya ɓanrke tsakanin rundunar sojin ƙasar da tsohuwar ƙawarta rundunar RSF, yaƙin n da ya haifa da ɗaya daga cikin mafiya munin halin jinƙai a duniya.

Asusun Kula da Ƙananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, (Unicef) ya fitar da wata sanarwa da a ciki yake cewa matsalar rashin abinci a shafar ƙananan yara a faɗin ƙasar, inda ƙananan yara da dama ke ramewa suna komawa daga ''fata sai ƙashi''.

Gargaɗin na WFP ya ƙara ƙarfafa kiran da gwamnan Arewacin Darfur, Al-Hafiz Bakhit, ya yi na buƙatar taimakon gaggawa, yana mai cewa halin da ake ciki a birnin El-fasher ya munana.

Bakhit na tare da gwamnatin sojin Sudan, da ke ƙoƙarin ci gaba da riƙe ikon birnin, wanda shi kaɗai ne ya rage da ke hannunta a yankin Darfur.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dakarun RSF na ƙoƙari ne domin ƙwace birnin daga hannun sojojin Sudan, lamarin da ya sa suka zafafa hare-hare, bayan da aka kore su daga Khartoum, babban birnin ƙasar.

Alƙaluman Majalisar Dinkin Duniya a farkon watan Yuli sun nuna cewa kashi 38 cikin 100 na ƙananan yara ƴan ƙasa da shekara biyar da ke zaune a sansanonin ƴangudun hijira a el-fashe ko kusa da birnin na fama da matsalar tamowa.

WFP ya ce tsananin ƙarancin abinci da ake fama da shi a birnin ya janyo mummunan tashin farashin kayayyaki a birnin, tare da kafa hujja da rahotonnin da ke cewa mutane na cin ciyayi da abincin da suka lalace domin su rayu.

Shirin Smar da Abincin na Majalisar Dinkin duniya dai bai ambaci ɓangaren da ke da alhakin haifar da yunwa, amma RSF ta datse hanyoyin kasuwanci tare da hana shigar da kaya zuwa birnin.

"Duk wanda ke el-Fasher na fama da yunwa a kowace rana," a cewar Eric Perdison, Daraktan WFP a gabashi da kudancin Afirka.

"Mutane sun gaji da wahalar da yaƙin da sanya su ciki fiye da shekara biyu. Matsawar ba a ɗauki matakan gaggawa ba aka samu damar shigar da abinci, rayuka da dama za su salwanta," in ji shi.

WFP ya ambato wata yarinya mai shekara takwas, Sondos - wadda ta fice daga birnin tare da ƴangidansu biyar - tana bayyana irin uƙubar yunwar da ake sha a birnin.

''El-Fasher na fama da ruwan harsasai da yunwa. Yunwa kawai ake yi da ruwan boma-bomai," in ji yarinyar, tana mai cewa a gidansu kullum gero kawai suke ci.

Hukumar Majalisar Dinkin Duniyar ta ce tana da manyan motoci maƙare da abinci da a shirye suke su kai abinci birnin bayan samun sahalewar gwamnatin Sudan.

Amma har yanzu tana jiran martanin RSF kan buƙatar da ta gabatar mata na ba su damar shigar da agajin, ta hanyar dakatar da faɗa domin bai wa motocin dmar shia birnin.

Tun farkon watan Yuni ne Majalisar Dinkin Duniya ke neman cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako guda, bayan da aka farmaki motocinta da ke kan hanyar shiga El-Fasher - inda sojoji da RSF ke zargin juna da kai harin.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya bayar da rahoton cewa shugaban rundunar sojin ƙasar, Janar Abdel Fattah al-Burhan - wanda kuma shi ne shugaban mulkin sojjin ƙasar - ya amince da tsagaita wuta na wucin gadi.

To amma rundunar RSF ba ta mayar da martani a hukumance ba.

To sai dai rahotonni sun ambato mashawartan RSF na cewa ƙungiyar ta yi fatali da shirin saboda ta yi imanin cewa za a yi amfani da yarjejeniyar wajen shigar da abinci da harsasai zuwa da ''dakarun Burhan'' da ke cikin birnin.

Sun kuma yi iƙirarin cewa RSF da ƙawayenta na kafa hanyoyi ''masu inganci'' domin fararen hular da ke son ficewa daga birnin.

Taswirar Sudan da ke nuna wuraren da sojoji da mayaƙan RSF da sauran ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ke iko da su
Bayanan hoto, Taswirar Sudan da ke nuna wuraren da sojoji da mayaƙan RSF da sauran ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ke iko da su

A watan da ya gabata ne hukumar kula da ƴancirani da duniya (IOM) ta ce fiye da mutum miliyan guda ne suka fice daga el-Fasher tun bayan ɓarkewar rikicin, ciki har da waɗanda suka fice daga sansanin Zamzam mai maƙwabtaka da RSF ta ƙwace a watan Afrilu.

BBC ta samu zantawa da wasu daga cikinsu domin jin halin da suka shiga na zaƙuwar ficewa daga birnin mai fuskantar ruwan boma-bomai da hare-haren RSF da ƙawayenta.

WFP ya ce ya cimma nasarori wajen shirya tsaftataccem tsarin shigar da kayan abinci zuwa wasu yankunan Darfur, amma ya ce sauran yankuna irin el-Fasher na da hatsari kwarai wajen shigarsu, musamman a wannan lokaci na damina da tituna suka lalace.

Wakilin Unicef a Sudan, Sheldon Yett ya ce an ɗan amu sassaucin yanayi a wasu yankunan tsakiyar ƙasar, da a baya-bayan nan aka riƙa samun shigar da agaji bayan da sojoji suka kori mayaƙan RSF a yankunan.

Sai dai ya ce suna fuskantar matsalar ƙarancin abinci saboda dakatar da tallafin Amurka da Donalt Trump ya yi ga ƙasashen duniya.

"Muna kan hanyar samun mummunar illa ga ƙananan yara masu tasowa, ba wai don ba mu da ilimi ko abubuwan kula da su ba ne, sai don rashin ɗaukar matakan da suka dace kan lokaci.''