Arsenal za ta ɗauki Premier League a wannan shekarar - Saka

Bukayo Saka

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan Arsenal Bukayo Saka ya ce ''a wannan shekarar'' Gunners za ta kawo karshen kaka 21 rabon da ta lashe Premier League.

Ƙungiyar da Mikel Arteta ke jan ragama ta kare a mataki na biyu karo na biyu da Manchester City ke lashe kofin babbar gasar tamaula ta Ingila.

Rabon da Arsenal ta ci Premier League tun karkashin Arsene Wenger a 2003/04, lokacin da ta ɗauki kofin ba tare da an doke ta ba.

Kawo yanzu Gunners tana mataki na uku a kan teburi da maki iri ɗaya da na Manchester City ta biyu da tazarar maki ɗaya tsakani da Liverpool ta farko, bayan wasa shida-shida.

''Ba na son in saka mana matsi a kan mu, amma dai ina jin wannan shekarar ta Arsenal ce za ta ci Premier Leagure'' kamar yadda Saka ya sanar da CBS Sports.

''Mun yi na biyu a kaka biyu a jere a gasar, inda kiris ya rage mu lashe kofin, amma dai muna fatan wannan shekarar ta Arsenal ce.''

Bayan da Arsenal ta yi ta biyu a Premier League, Saka yana cikin ƴan wasan da tawagar Ingila ta yi rashin nasara karo biyu a jere a gasar cin kofin nahiyar Turai Euro 2021 da kuma 2024.

Ranar Talata Arsenal ta doke Paris St Germain 2-0 a wasa na biyu a Champions League a bana, inda suka fafata a Emirates.

PSG ta fara da doke Girona 1-0, ita kuwa Gunners ta tashi 0-0 a Atalanta.

Ranar Asabar 5 ga watan Oktoba, Arsenal za ta karɓi bakuncin Southampton a wasan mako na bakwai a Premier League.