Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Turancin Ingilishi ke samun karɓuwa a Algeria
Cikin jerin wasiƙu daga ƴan jaridar Afirka, Maher Mezahi ya yi rubutu kan matakin Algeria na baya-bayan nan na nesanta kanta daga Faransa, ƙasar da ta yi musu mulkin mallaka a baya.
Manyan tituna uku na Tsakiyar babban birnin Algeria duk suna haskakawa daga Grande Poste, wani tsohon gini na musulunci da aka yi a saman ruwa.
Daga babban gidan waya na ƙasar, hanyoyin sun bi ta tekun Mediterranean daga arewa sannan suka bi ta gabas, yamma da kudu da Algiers.
Tsawon shekara 132 da Faransa ke mulkin mallaka a ƙasar, ana kiran titunan rue d'Isly, Boulevard Michelet da rue Sadi Carnot.
Bayan samun ƴancin kai ne gwamnatin Algeria ta yi ta fafutukar share duk wani ɓurɓushin mulkin Faransa.
Don haka aka sake raɗawa titunan nan uku na Algiers suna - an maye sunan Michelet da Didouche Mourad, rue d'Isly ya koma Larbi Ben M'Hidi sai Sadi Carnot da ya koma Hassiba Ben Bouali.
Yayin da ƴan Algeria suka karɓi sunayen "Didouche" ko "Hassiba", ina yawan mamakin yadda akasarin al'ummar wajen suka ci gaba da kiran "Rue d'Isly - sunan da Faransa ta sa.
Babu wani dalili da zai yi bayanin abin da ya sa wasu suka rungumi sabbin sunayen, wasu kuma suka yi fatali da su - alama ce kawai ta cewa harshe wani abu ne da bai cika tafiya dai-dai da dokokin hukuma ba.
Sama da rabin ƙarni bayan fafutukar neman ƴanci a shekarun 1950 da 1960, siyasar harshe ta kasance mai mahimmanci.
A watan da ya gabata, Shugaban Algeria Abdelmadjid Tebboune ya sanar cewa ƙasarsa za ta janye daga koyar da Faransanci, ta koma koyar da Ingilishi a matsayin harshe na biyu a makarantun Firamare na gwamnatidaga zangon karatu na gaba.
"Hakan na nuna cewa Ingilishi ya zama gama-gari a duniya," in ji shi.
Amma, ga galibin ƴan Algeria, matakin mai ban mamaki ya koma ga gazawar shekarun 1970 lokacin da Shugaban Algeria, Houari Boumediene ya nemi ya bijiro da wani tsari na amfani da Larabci a makarantu da fannin shari'a.
Domin cike giɓin rashin masu yin Larabci karɓaɓɓe ne ya sa Algeria ta ɗauki dubban malamai daga Masar da Iraki waɗanda a wasu lokutan suke takun saƙa da Algeria ta fannin al'ada.
Duk da cewa ƙwararre kan harsuna a Algeria, Abderrazak Dourari yaƙi yanke hukunci kan game da matakin fifita Ingilishi kan Faransanci, ya damu game da rashin ƙwararrun malamai da kuma kayan koyarwa.
"Ba za ka kawo mai aikin tafinta a matsayin malami ba. Ba zai yiwu ba, bai yi ma'ana ba," kamar yadda ya faɗawa kafar yaɗa labarai ta intanet Tout Sur l'Algerie. Amma cikin ƴan siyasa da ma'aikata a Algeria, akwai haɗaka wajen janyewa daga tasirin Faransa - ko dai a siyasa ko tattalin arziki ko ma al'ada.
A baya-bayan nan ne Algeria taƙi sabunta yarjejeniyarta da wasu kamfanonin Faransa da ke ɓangaren sufuri da ruwa, inda ta miƙa ayyukan ga wani amfanin na cikin gida.
Sannan bisa al'ada, a yanzu ƴan Algeria sun fi karkata zuwa ga kallon fina-finan Turkiyya ko ma shafukan da ke nuna fina-finai mallakin Amurka kamar Netflix a maimakon kallon shirye-shiryen da ake haskawa a gidan Talabijin na Faransa.