Labaran tsadar rayuwa a ƙasashen duniya biyar ciki har da Najeriya

Abinci na ci gaba da tsada, wani lokacin yana ƙaranci ko ina a faɗin duniya.

A ko ina mutane sun koma karɓar sabon yanayin da suka shiga ko da kuwa ya kama sauya cimarsu.

Safiya ce misalin ƙarfe 4, lokacin da Donna Martin ta isa wajen aiki.

Kowace rana na zuwa da irin nata ƙalubalen na ciyar da yaran makarantar da ke gundumar ta.

Ms Martin dai ta kasance daraktar kula da abinci da ke sa ido kan yara 4,200, galibinsu suna tsarin ciyarwa na gwamnati a kyauta.

"Muna da shagunan sayar da kayan abinci biyu a yankin da ke da al'umma 22,000," a cewarta.

Amma a shekara biyar da ta gabata, tana fama wajen samun abin da take buƙata.

Hauhawar farashin kayayyakin abinci a shekara ya kai kashi 10.9 cikin 100 a Yuli, mataki na ƙololuwa da ya taba kaiwa tun 1979.

Yayin da farashin kayayyaki ke ci gaba da hauhawa, wasu daga cikin masu kawo wa Ms Martin kayan abinci sun fara ja baya kan batun ciyar da makarantu.

Ana sa ido kan shirin ciyar da makarantun gwamnati a Amurka. Hakan na nufin dole kayan abinci su zama babu sikari ko gishiri da yawa. A don haka dole Ms Martin ta zaɓi irin kayan abincin da take so.

Ta lura cewa masu kai mata abinci suma suna fuskantar ƙalubale. Ƙarancin ma'aikata na nufin ba za su iya samun direbobi ba, sannan farashin mai ya ƙaru da kashi 60 cikin 100 tun shekarar da ta gabata.

  • A watan Yuli, hauhawar farashin kayayyaki a Amurka ya kai kashi 10.9.
  • Amurkawa na kashe kashi 7.1 na kuɗaɗensu kan abinci (USDA 2021)

A baya-bayan nan da ta rasa inda za ta samu sha-daka, wani abu da yaran ke matuƙar so, sai ta sauya musu da faten wake.

Ta ce "na san yaran ba za su so shi sosai ba amma dole na basu wani abin,"

Lokaci zuwa lokaci ita da ma'aikatanta suna shafe safiya da dare suna duba shuguna irinsu Walmart.

Ƴan Sri Lanka na karkata ga ɗan itaciyar Jackfruit

A wurin da a baya ake noman shinkafa a wajen Kandy da ke Tsakiyar Sri Lanka, Anoma Kumari Paranathala na tsinkar wake da ganyen na'a-na'a daga lambunta.

Ko daga nan kana iya hango irin halin da ake ciki a wani yankin ƙasar ganin yadda gwamnati da tattalin arziki ke ƙara taɓarɓarewa.

Akwai ƙarancin abubuwa - magunguna, mai da abinci. Ko mutanen da suke da rufin asiri na fuskantar ƙalubale wajen sayan kayayyakin yau da kullum.

"A yanzu mutane sun damu game da makomarsu," kamar yadda Ms Paranathala ta ce. "Suna fargabar za a rasa abinci,"

Filin mallakin iyalinta ne, sun soma shuke-shuke a lokacin annobar korona domin ɗebewa kansu kewa , a yanzu ya zama abin buƙata.

  • Hauhawar farashin kayayyaki a Sri Lanka ya kai kashi 75.8 cikin 100 a watan Yuni.
  • Al'ummar Sri Lanka na kashe kashi 29.6 cikin 100 na kuɗaɗensu wajen sayen abinci.

Haka ne ya sa Ms Paranthala ta koyi yadda za ta dasa kayan lambu daga shafin Youtube da litattafai. A yanzu tana da tumatur da alayyahu da dankali a lambun nata.

Ba kowa ke samun irin wannan dama ba ta samun filin shuka amma galibin ƴan Sri Lanka na koma wa ga ɗan itaciyar Jack a matsayin abinci.

Ta fara sarrafa ɗan itaciyar ta fuskoki da dama. Wasu na daka ƙwallon ɗan itaciyar domin yin garin flour ta yin biredi da kek da roti.

Shi ya ɗanɗanon wannan ɗan itaciya? "Ɗanɗano ne da ba zai misaltu ba, a cewarta.

Gidajen gasa biredi sun fara shiga halin tsaka mai wuya

Emmanuel Onuorah ba shi da sha'awar duk wani abu da ya shafi siyasa, babu abin da yake so irin sana'ar burodi.

Amma kwanan nan sana'arsa tana fuskantar barzanar dakatarwa a Najeriya.

A cikin shekara ɗayar da ta gaba, farashin fulawa ya ƙaru da fiye da kashi 200, sikari ya ƙru da kusan kashi 150, shi kuwa ƙwai ya ƙru da kusan kashi 120," ya ce. Asara kawai muke tafkawa babu riba," ya faɗa. Wannan lamari ya sa ya sallami ma'aikata 305 daga cikin 350 da yake da su.

"Da me za su ciyar da iyalansu?"

A matsayinsa na shugaban wata ƙungiyar masu gidajen burodi, shi ke jagorantar fafutukar adawa da wannan hauhawar farashi.

A watan Yuli ma sai da ya nemi abokan sana'arsa masu gidajen burodi kusan rabin miliyan da su rufe na tsawon kwana huɗu.

Yana fatan gwamnati za ta shiga lamarin ta rage yawan haraji kan kayayyakin da suke shigar da su ƙasar.

Rashin kywaun amfani goda da matsalar da annobar cutar korona ta jawo na daga cikin abubuwan da suka sa alkama da man gyaɗa suka yi tsada a duk faɗin duniya.

Yaƙin Rasha da Ukraine kuma ya ƙara rikita al'amuran.

A Najeriya kusan dukkan kayayyakin da ake buƙata a gidajen burodi shigar da su ƙasar ake yi. • Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya kai kashi 22 cikin 100 a watan Yuli • Ƴan Najeriya na kashe kashi 59.1 cikin 100 na yawan kuɗin da suke samu a wajen sayen abinci.

Sannan kuma ƙasar na fama da yawan ɗauke wutar lantarki, don haka yawanci masu kasuwanci da masana'antu kan yi amfani da janareto ne suna sayen man dizel.

Duk da hauhawar farashin kayayyaki, Mr Onuorah ya ce ƙrin kuɗin buruodin da ya yi bai wuce kashi 10 zuwa 12 cikin 100 ba.

Masu sayen burodin ba za su iya saya ba idan ya ƙara kuɗin fiye da haka.

A Peru matsakaiciyar tukunya ce ke ciyar da mutum 75

A yayin da take tafiya a wata hanya mai kwazazzaɓai a birnin Lima, Justina Flores tana tafe tana tunain ko me za ta dafa a ranar?

Matsala ce da kullum mutane ke fama da tunaninta. Mafi yawan mazauna San Juan de Miraflores aikatau ne sana'arsu - kamr kuku ko rainon yara ko wanke-wanke da shara.

Amma mutane da dama irin su Ms Flores sun rasa aikinsu lokacin annobar cutar korona.

Iyalai sun shiga hali na yunwa.

Sai suka ƙirƙiri wata dabara inda suka dasa takunya a ƙofar gidan Justina,suka gina ƙaramar bukka, wani malamin coci kuma ya bayar da rusho.

Sai Ms Flores ta nemi ƴan kasuwa da su bayar da kyautar kayan abincin da suka fara lalacewa. Sai suke dafa abinci da yawa.

Shekara biyu bayan fara wannan abu sai ga shi suna iya ciyar da mutum 75 sau uku a mako.

Hakan ya sa Ms Flores, wacce a da aikin girki take yi, ta zama wata gwarzuwa a yankinta.

"Har yanzu ina zuwa gida-gida neman tallafi."

• Hauhawar farashi ta ƙaru da kashi 11.59 a Peru a watan Yuli • Al'ummar Peru na kashe kashi 26.6 cikin 100 na abin da suke samu kan sayen abinci

Yawanci takan dafa miyar dage-dage ne da shinkafa. Amma a watannin da suka gabata, an rage samun taimakon kayan abincin.

"Muna cikin yanayi, a dole na rage yawan abincin da muke dafawa," a cewar Ms Flores. Da ƙyar take samun ko da shinkafar ma.

A yanzu dai Ms Flores ta daina yin girki da nama saboda hauhawar farashin da aka ƙara samu a kwanan nan.

Ta koma amfani da hanta da ƙasusuwa da ƙundu saboda sun fi araha.

A ranar da BBC ta tuntube ta don yin hira kuma, taliya da wata miyar albasa ta dafa

An ƙaurace wa cin kaza a Jordan

A ranar 22 ga watan Mayu an wallafa wani saƙo a Tuwita da aka rubuta da Larabci da ke kira ga mutane su wallafa hotunan abinci dangogin kaza tare da maudu’in #Boycott_Greedy_Chicken_Companies, wato a ƙaurace wa kamfanonin sarrafa kaji.

Kwanaki kaɗan bayan nan a Jordan, Salam Nasralla ta kama hanyar tafiya gida daga wani kanti bayan da ta ga kamfe ɗin ya yaɗu kamar wutar daji.

“Mun ji labarin hakan daga ko ina, dukkan abokan arzikinmu da ƴan uwanmu suna magana a kan hakan. Labarin ya yaɗu a shafukan intanet,” in ji Ms Nasralla.

Ko a lissafin sayayyar kayan abincinta ta ga yadda farashi ya yi sama. A matsayinta na uwar yara biyu da take yawan yi wa iyayenta da ƙanne da yayyenta girki, takan sayi kaji da dama. Sai ta ga ya kamata ta shiga wannan fafutukar.

Sai da ta shafe kwana 10 ba ta sayen kaji, amma abin da wahala. Saboda sauran dangogin nama irin su kifi da jan nama sun yi tsada.

Salam da iyalanta sai sun ci nama kusan kullum.

Suan ci gurasa da burudo a maimakon naman.

Kwana 12 bayan fara fafutukar sai farashin kaji ya sauka da kashi uku cikin huɗu, kusan dala ɗaya kenan kan kowane kilo.

Hauhawar farashin kayayyaki a Jordan ya ƙaru da kashi 4.1 cikin 100 a watan Yuni

• Al’ummar Jordan na kashe kashi 26.9% na kuɗin da suke sama a kan sayen sabinci

Rami Barhoush, wanda ke da gonar kiwon kaji ya goyi bayan ƙauracewar amma yana ga ba a tsara abin sosai ba.

Gonarsa na fama da matsalar hauhawar farashin a farkon shekara, musamman ta fannin sayen man janareto da abincin kajin.

Wadanda suka taimaka wajen haɗa wannan rahoto su ne Suneth Perera, Guadalupe Pardo da kuma Riham Al Baqaeen.