Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
KU BA MU LABARANKU: Shin wannan tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyakin sun shafe ku?
Iyalai a faɗin duniya suna ta fama da tsadar rayuwa kuma mutum miliyan 71 ne a ƙasashe masu tasowa ke faɗa wa cikin tarkon talauci sakamakon hauhawar farashin kayayyaki a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.
Wahalar samun abinci da tsadarsa suna tursasa mutane da dama rashin samun damar cin abinci sau uku a rana kamar yadda ya dace. Wasu da dama sun sauya tsarin cin abincinsu ta yadda daga cin mai daɗi aka koma garau-garau, kuma hakan na shafar lafiyarsu.
Shi wannan tsadar rayuwa tana tasiri a kanku? Ba mu labarin yadda rayuwarku ta sauya – idan har mun ga labarinku mai ma’ana ne, to za mu tuntuɓe ku don yin hira da ku da kuma wallafa shi.